Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amfanin sauraro da kunnen basira a alaƙa tsakanin al'umma
- Marubuci, Daga Emily Kasriel
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editor, BBC Crossing Divides
"In matashiyar Musulma wadda ke sanya hijabi ta yanke shawarar ta daina sanya hijabi, zan ɗauke ta mutuniyar banza da ba zan iya abota da ita ba. In kuma muka haɗu sai na tsokane ta," in ji Hawraa Ibrahim Ghandor, wata Musulma 'yar kasar Lebanon.
Ta ce wannan matsayar tata ta samo asali ne daga gidan da ta tashi da suke da rikon addini. Mahaifinta ya nuna mata cewa ta rika abota da wadanda ke da tarbiyya irin tata, kuma ta ce ta rike wadannan shawarwarin har zuwa girmanta da take koyarwa a matsayin malamar Ingilishi a makaranta.
Tana daga cikin mutum 150 'yan Lebanon da suka shiga cikin shirin sauraro na tsanaki da majalisar Burtaniya ta shirya da hadin gwiwar BBC.
Manufar Shirin ita ce su ko yi dabarun tausayawa da shiru tsit da kuma jinkiri wajen yanke hukunci.
"Na koyi yadda zan saurari abubuwa a nutse, ba kuma na yanke hukunci haka kurum sa na fahimci komai, kuma ina bai wa mutane dama su bayyana abin da ke ransu ko suke son fada. In kuma yi musu bayani domin su gane na fahimci abin da suke son na sani.
Abin da a baya take gani a matsayin tsattsauran r'ayi ko rashin hakuri da juna yanzu ba sa tare da ita baki Daya.Shekara guda baya, Hawraa ta fara dabbaka wannan horo da ta samu.
"Da bana son 'yan gudun hijirar Syria da ke Lebanon," in ji ta. „Ina musu kallon ba su damu da tsaftar kansu ba, kuma ba sa rayuwa kamar yadda yan kasarmu ke yi."
Hawraa tace alakarta yanzu da mutane cike take da juriya da hakuri da mutane. "a baya, ba na tattaunawa da mutanen yadda ya kamata, ko kuma sauraren kafafen yada labaari da ke angiza wariya da kyama da wasu ne ya janyo hakan. In zamu saurari juna zamu ga ashe muna da wasu ra'ayoyi iri daya a matsayin mu na mutane."
Haka kuma, kawancen Hawraa da Mayada bai hana Hawraa dardar din da take da shi ba game da wasu al'adun Mayada.
Dan gidan Mayada na daf da auren wata yarinya mai shekara 16, wadda ba gama gari ba ce a cikin 'yan gudun hijirar Syria.
"Na amince da hakan a matsayin zabinsu," Hawraa ta bayyana. " da wannan shirin na sauraro a tsanake za ka fahimci wannan mutumin ba makiyinka ba ne, ko da yana da wasu halaye da ba irin naka ba."
Albarkacin murnar cikar BBC shekara 100 da kafuwa, a watan Mayu mai zuwa BBC World Service da kuma cibiyar British Council za su ba da horo kan sauraro da kunnen basira ga matasa 1,000 a ƙasashe 100.
Idan kuna so ku ƙware a sauraro da kunnen basira a faɗin duniya tare da mutane, kuna iya samun ƙarin bayani a nan. - cikin harshen Ingilishi.
Mohammad, ma'aikacin agaji daga Lebanon, yana sane cewa ba shi da ƙwarewa wajen sauraro, kuma hakan na daƙile shi wajen tattaunawa wajen aikinsa. "Ina yawan datse mutumin da kusan kodayaushe ya san abin da zan faɗa masa," a cewarsa. "A lokacin ne kuma zan fara zato sannan na fara ƙoƙarin yi masa bayanin dalili."
Jim kaɗan bayan samun horon, Mohammad ya samu aiki a Mosul na Iraƙi, inda yake aiki da wata ƙungiyar da ba ta gwamnati ba don yin aiki wajen kula da 'yan gudun hijira. Don ya samu nasara a sabon aikinsa, dole ne sai da Mohammad ya sasanta wasu ɓangarori da ke rigima da juna.
"Za mu mayar da 'yan gudun hijira gida ne? Ko za mu yi ƙoƙarin zaunar da su a biranen da suke? Za su iya zama a unguwanni tare da mutanen da ba 'yan ƙabilarsu ba?" a cewarsa.
Mohammad bai manta bayanan da aka yi masa ba kafin ya fara aikin. Yayin da abokiyar aikinksa ke bayanin abin da aikin ya ƙunsa, ya fara jin cewa akwai abubuwan da ya kamata ya sani amma ba a faɗe su ba.
"Ina tabbatar muku, a harkokin agaji akwai buƙatar ka fahimci ɗabi'ar kowa da kowa kafin ka iya aiwatar da ayyuka yadda suka kamata. Wa ke da sauƙin kai, wa ke da taurin kai kuma wa ke da kunnen ƙashi."
Yanzu Mohammad ya tuna horon da ya samu da kuma amfanin bai wa mutum dama bayan ya kammala magana, a matsayin girmamawa da kuma ba su damar bayyana komai. Bayan abokiyar aikinsa ta gama magana, ya jira daƙiƙa 20.
"A cikin wannna daƙiƙa 20 ɗin na samu damar a amince da ni da kuma fahimtar ta," in ji shi. "Bayan wannan lokacin, alaƙarmu da ita ta haɓaka, har ma ta ƙara min bayani game da duk mutanen da zan yi aiki tare da su."
Yadda sauraro da kunnen basira ke aiki
- Ka tambayi wanda kake magana da shi ya yi bayanin fahimtarsa da kuma dalilin da ya sa suke jin hakan. Saurari ba tare da saka baki ba, ajiye tunaninka da shawararka a gefe
- A taƙaice, tattara abin da abin da ka ji sannan ka duba ko ka fahimta da kyau, ciki har da yadda aka ba ka labarin. Hakan ba ya nufin dole sai ka yarda da abin da ka ji
- Tambaye su ko sun yarda da taƙaitaccen abin da ka fahimta. Idan ba su gamsu ba, tambaye su su sake yin bayani.
- Ci gaba da yin hakan har sai ka ji sun ce "e" da kyau. Daga wannan lokacin, ana sa ran za su fara sauraron labarinka
Akwai wasu lokuta kuma da Mohammad ya ƙi yin amfani da ƙwarewar da ya samu kan sauraro da kunnen basira.
"A harkokin agaji, idan ka ƙware kuma kana tattaunawa da wani, za ka iya shiga wani yanayi da ba ka shirya shiga ba," in ji shi.
Mohammad ya faɗa min wani labari da ya samu a hirarsa da wani direban tasi, wanda aka yi wa bulala 18 saboda ya tuƙa wata mata wadda ba ta tare da ɗan uwanta namiji - abin da aka haramta a lokacin da birnin yake hannun ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta Islamic State.
"Sauraro da kunnen basira na da matsala. Na san cewa abu ne mai haɗari a wurina na ji irin waɗannan labaran. Akwai buƙatar na yi nesa da labaran wasu saboda ban shirya shiga irin wannan yanayin ba."
A gefe guda kuma ga Hawraa, ta yaya ta daidaita tunaninta game da tasowarta da kuma ɗabi'un mahaifinta? Mahaifin nata ya rasu 'yan shekaru da suka wuce, amma takan ziyarci ƙabarinsa duk Alhamis. "Ina jin cewa zai iya ganina daga sama kuma na yi imanin cewa yana farin ciki da alfahari.
"Yawan yadda muka san mutum irin yadda za mu rage tsoronsa kenan. Haka ma idan muka rage zato a kansa. Ba mamaki ya gano cewa duka mutane na da hali iri ɗaya."