Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben 2023: Ana nuna fargaba kan yadda masu zabe ke sayar da 'yancinsu a Najeriya
Masu sharhi kan harkoki siyasa a Najeriya sun fara nuna fargabar cewa akwai yiwuwar wasu masu hannu-da-shuni da ke neman wani mukamin a zaben da za a yi a shekarar 2023 - ko da ba su cancanta ba - za su sayi kuri'un mutane domin cimma burinsu.
An soma fargabar ne bayan wani bidiyo da aka dauka a zaben gwamnan jihar Ekiti da aka kammala a baya-bayan nan wanda ya nuna wasu 'yan siyasa na raba wa masu kada kuri'a kudi.
Kazalika a zabukan fitar da gwani ma da aka kammala a kasar an ga tasirin hakan in da aka ga wani daliget na raba wa 'yan mazabarsa kudin da ya ce wani dan takarar shugaban kasa ne ya ba shi.
Dakta Kole Shettima, shugaban Cibiyar tabbatar da cigaba da kuma dimokradiyya a Abuja, kuma mai sharhi kan harkokin siyasa ya shaida wa BBC cewa, wannan abu da 'yan siyasa ke yi na da matukar illa.
Ya ce "Idan ana haka to idan ba a yi sa'a ba a zabuka masu zuwa da za a yi sai mai kudi ne zai samu nasara ko da bai cancanta ba."
Dr Kole Shettima, ya ce bisa la'akari da halin da ake ciki a Najeriya na talauci na tsadar kayayyaki, masu neman mukaman siyasa za su iya amfani da yanayin da mutane ke ciki su basu kudi don su zabesu.
Ya ce "Shawarata ga masu kada kuri'a shi ne duk wanda ya basu kudi don su zabe shi to su karbi kudin dama kudinsu ne, to amma idan kuka zo yin zabe sai ku zabi wanda ku kuke gani yafi cancanta."
Akasari mata su ne suka fi fitowa a lokutan zabe, kuma ana zargin 'yan siyasa na ba su sabulu da atamfofi ko kudi don su zabe su wanda haka na da illa sosai ga makomar matan a siyasance.
Barista Aisha Ali Tijjani, mamba ce a gamayyar kungiyoyin fararen hula a jihar Kano, ta shaida wa BBC cewa ba karamar illa ba ce yadda ake yaudarar mata a ba su kudi ko kaya lokacin zabe.
Ta ce "Na farko dai mata ba su san damar da suke da ita da kuma 'yancinsu na zabe ba, sun saryar da 'yancinsu da damarsu na zabar wanda ya cancanta."
Barista Aisha ta ce ya kamata mata su sani duk wani abu da za a ba su a lokacin zabe, to zai musu amfani ne na kankanin lokaci, kuma sun cutar da kansu wajen rashin zabar shugaban da ya dace ba.
A cewarta "Shawarata ga mata ita ce ya kamata mata su waye sannan su bude ido su san cewa ba bukatar yanzu-yanzu ake nema a yaye ba, ma'anar zabe ita ce kadai makamin da talaka ke da shi na canja alkiblar mulki domin ya zabi wanda yake ganin zai ceto shi daga halin da yake ciki."
Baristar ta ce idan har talakawa ba su yi amfani da wannan dama ta zabe wajen canja akalar zaben sun zabo wanda ya cancanta da su ba, to a gaskiya ba mata ne suka shiga uku ba kadai har ma da maza.
Sayar da kuri'a dai tamkar sayar da 'yancin dan kasa ne na tsawon shekaru hudu, kuma tsalle daya ake a fada rijiya, amma sai a yi dubu ba a fito ba.
Sannan bisa la'akari da halin da ake ciki a Najeriya, ya ishi 'yan kasar su yi karatun ta natsu tare da sauya tunani a kan yadda suke mika wuya ga 'yan siyasar da ke siyan kuri'a a lokacin zabe don gudun fadawa hannun gurbatattun shugabanni.