'Alama ta nuna gwamnonin arewa ba al'ummarsu ce a gabansu ba'

Wata kungiya ta matasan arewacin Najeriya, Arewa Youth Consultative Forum AYCF ta yi kakkausar suka a kan shawarar da wasu gwamnonin jam'iyyar APC daga arewacin kasar suka cimma ta cewa kamata ya yi wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari ya fito daga kudu.

Ƙungiyar matasan ta ce shawarar gwamnonin ta sha bamban da matsayin akasarin mutanen yankin, inda ta bukaci masu kada kuri'a a zaben fid da gwani na APC su yi abin da ya dace.

A tattaunawarsa da BBC Shugaban kungiyar Alhaji Yerima Shettima, ya ce abin kusan bai ba su mamaki ba ganin yadda wasu daga cikin shugabannin Arewa suna kaiwa suna komowa sun kasa kama matsaya guda daya.

Ya ce, '' A halin da muke ciki a arewa musamman ma wannan gwamnoni ba mu ji mamaki ba, don saboda duk alama ta nuna cewa wadannan mutane ba al'ummarsu ne a gabansu ba, ba su damu da abin da ya shafi talakan arewa ba.''

Shugaban ya ta'allaka zargin nasa da cewa, ba zargi ba ne saboda abin da ya ce, gwamnonin sun yi ba tare da shawara da arewa ba, inda wasu rahotanni ke cewa gwamnonin sun ce mulki ya koma hannun 'yan kudu, inda za a tsayar da dan takara na zaben 2023, na jam'iyyarsu ta APC daga kudu.

Ya ce babu wani dalili da zai sa arewa ta mika wa kudun mulki, ''Ko Burkina Faso da suka kama mulki, minority suka kama mulki sai da ta yi shekara 35, har yanzu suna rike da mulki minority ne.''

Alhaji Yerima, ya ce, ''Babu hujja a ce don arewa ta yi sheakara takwas da iya al'ummar da muke da shi muka karya kuri'a muka ci zabe a ace haka kawai an dauki mulki an mika wa dumukuradiyya ba a yinta a duniya.''

''Kuma za ka sake duba Kamaru yau shekara 40 Paul Biya yana mulki, minority ne, kuma sun rike mulkin ba abin da ya faru kuma ana tafiya. Don menene, meye dalilin namu gwamnonin na arewa za su dauka lokaci daya kawai su juya baya ba wai kada kuri'a aka yi ba aka kada arewa ba a'a da gangan su dauki mulki su mika wannan cin amana ne ga arewa ga baki daya.'' in ji shi.

Shugaban kungiyar ta AYCF, ya ce babu inda a tsarin dumukuradiyya aka ce idan ka karbi mulki ka dauka ka bayar haka kawai ba tare da an yi kuri'a ba, haka kuma kundin tsarin mulkin Najeriya, da ma na jam'iyyar ta APC ba su zo da haka ba.

Ya ce saboda haka abin da suka yi ba doka ba ne, ba dumukuradiyya ba ne, son kansu ne, kuma mutanen arewa ba za su yarda da shi ba.

Shugaban kungiyar ya ce a halin da ake ciki irin cin kashin da ake yi wa 'yan arewa a kudu, ko alama bai kamata a ce wani ya fito ya goyi bayan arewa ta bar mulki ya koma can ba, in dai b ta hanyar kuri'a ba ne.