Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnoni arewa sun fi na kudu hujja kan takarar shugaban kasa na 2023 - Masana
Masana kimiyyar siyasa a Najeriya na ci gaba da fashin baki kan matakin da kungiyar gwamnonin arewacin kasar ta dauka na yin watsi da matsayar takwarorinsu da ke kudanci na cewa dole ne shugaban kasa ya fito daga yankin na kudu a zaben 2023.
A ranar Litinin ne gwamnonin arewar suka yi wani zama inda suka tattauna batutuwa da suka hada da martanin, inda suka ce babu wanda zai tilasta wa 'yan Najeriya zaben dan takara daga wani bangare na kasar.
Wani masanin harkokin siyasa a kasar Dakta Abubakar Kari na Jami'ar Abuja ya ce hukuncin da gwamnonin suka yanke na yin hannun riga da matakin takwarorinsu na kudu ya yi dai dai.
"Ni ina ga hanzarin da gwamnonin Arewa suka bayar yana da karfi kwarai da gaske saboda sun yi maganar tsarin mulki ne.
"Kuma tsarin mulkin Najeriya ya fito karara ya nuna cewa hanyoyi biyu ne kawai mutum zai iya zama shugaban kasa, kuma babu maganar bangaranci ko sashe ko kabilanci a ciki."
A cewar masanin hujjar da gwamnoni kudancin suka dogara da ita ba kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya zo da ita ba, saboda haka ba dai dai ba ne su yi kokarin tursasa ra'ayinsu na siyasa a kan masu zabe.
Sai dai ya ce ba shi da haufi idan tafiya ta yi tafiya bangarorin biyu za su warware wannan matsala su goge layin da suka ja.
"Warware wadannan rigingimu da tirka-tirka shi ne siyasar. Kuma su 'yan siyasa sun san yadda suke warware kayansu."
"Kuma yawanci irin wadannan maganganu na fatar baki ne kawai. Su kansu wadanda ke maganar ba su yi imani da abin da suke fada ba," in ji Dakta Abubakar Kari.
Masanin siyasar ya kafa hujja da cewa wasu da ke ikirarin cewa a mika takarar shugabancin kasa a kudu a yanzu gwamnonin jam'iyyar PDP ne da ake maganar ta aminta da mika takara ga dan arewa.
"Mafi yawan gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP yan kudu ne, kuma da su aka yi matsayar cewa dole ne sai mulki ya koma kudu.
"To amma ka ga tun ba a je ko ina ba wasunsu suna nan suna ta kulle-kullen cewa su za su dauki dan takara daga arewa. Saboda haka ita wannan tirka-tirka da rigima warware ta ba wani abu ba ne," a cewar Dakta Kari.
Kumfar bakin da 'yan siyasa a Najeriya ke yi kan batun takarar shugabancin kasa na zuwa a daidai lokacin da manyan jam'iyyun kasar kamar APC mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP suka kasa warware rigingimun shugabancin cikin gida, da ya haifar da rabuwar kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyyun.