APC: Kashim Shettima ya nemi afuwar Osinbajo da Ahmad Lawan kan muzanta su

Osinbajo da Kashim Shettima da Sanata Ahmad Lawan

Asalin hoton, State House/@KashimSM/@DrAhmadLawan

Bayanan hoto, Kashim Shettima (tsakiya) ya yi kalaman ne yayin wata hira a Channels TV ranar Asabar

Tsohon gwamnan Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya nemi afuwar Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo bisa kalaman muzantawa da ya yi a kansa.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi, Sanata Shettima ya kuma nemi afuwar Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Ahmed Lawan, shi ma bisa kalaman da ba su dace ba da ya yi a kansa.

A ranar Alhamis da ta wuce ne tsohon gwamnan na Jihar Borno ya bayyana cewa Farfesa Osinbajo mutum ne mai kirki, "amma mutanen kirki ba su dace da shugabanci ba sai sayar da gurguru da askirim (ice cream).

Kazalika, ya bayyana cewa duk da yake shugaban majalisar dattawan dan yankinsu ne amma babu wanda ya san shi a Najeriya, yana mai cewa hasali ma idan aka ambaci sunan Ahmad Lawan a yankin kabilar Igbo, mutummin da zai zo musu a rai shi ne "mai sayar da tumatur".

Ya yi wadannan kalamai ne yayin da yake jaddada muhimmancin ganin jam'iyyar APC ta tsayar da tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu a matsayin wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa a zaben 2023.

Sanata Shettima na ganin shi ne kadai yake da "karbuwa sannan aka san shi a fadin Najeriya" a cikin masu son yi wa jam'iyyar takara.

'Ba a fahimci kalamaina ba'

Sai dai a sakon da ya wallafa a Tuwita, Sanata Shettima ya ce yayin tattaunawarsa da gidan talbijin na Channels bai yi niyyar "muzanta kowanne dan takara ba, ballatana abokaina da abokan shawarata."

"Duk cikinsu babu dan hamayya don haka bukatarsu ta tsayawa takara ba barazana ba ce a gare mu," in ji tsohon gwamnan na Jihar Borno.

Sanata Shettima ya kara da cewa an zuzuta kalaman da ya yi a kan Osinbajo da Ahmad Lawan kuma ba a fahimce su ba.

"Ban yi kalamaina domin na nuna su a matsayin wadanda ba su dace su yi takara ba, sai don kawai na nuna cewa su ba barazana ba ne a gare mu," in ji Kashim Shettima.

Ya kara da cewa "duk da haka ina neman afuwa ga mataimakin shugaban kasa da shugaban majalisar dattawa bisa radadin da wadannan kalamai nawa - da na yi ba da niyya ba - suka haddasa a gare su da iyalansu da kuma magoya bayansu."

Buhari ya buƙaci 'ƴan takarar shugaban ƙasa a APC su je su sasanta kansu

APC

Asalin hoton, State House

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya shawarci masu neman takarar shugabancin ƙasar a jam'iyyar APC su sasanta a tsakaninsu don amincewa da mutum ɗaya ya wakilci jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasar na 2023.

Shugaban ya ba su shawarar ce yayin wata ganawa da ya yi da su a daren ranar Asabar a fadarsa da ke Abuja.

Dukkan masu neman takarar sun halarci wannan ganawa, ciki har da jagoran jam'iyyar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, wanda a baya-bayan nan ya furta wasu kalamai kan shugaban da suka tayar da ƙura.

Gwamnonin Arewa na APC na son a ba wa 'yan Kudu takara

Kafin ganawar da Buhari ya yi da masu neman takara a APC ranar Asabar, wata sanarwar hadin gwiwa da wasu gwamnonin APC 11 na arewa suka fitar ta bukaci dukkan masu neman takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar su janye don miƙa wa kudu mulki.

Gwamnonin sun bayyana cewa tattaunawar da suka yi a tsakaninsu ce ta ba su damar yin kiran ga APC da ta miƙa wa 'yan takara daga kudanci tikitin takarar, sannan ta nei 'yan takarar Arewa su janye.

"Bayan tattaunawa cikin natsuwa, muna so mu bayyana matsayarmu cewa bayan mulkin shekara takwas na Shugaba Muhammadu Buhari, ya kamata ɗan takarar APC na zaɓen 2023 ya fito daga 'yan jam'iyyarmu na kudancin Najeriya," a cewar gwamnonin.

"Magana ce ta kimar APC da kuma hukuncin da ba shi da wata alaƙa da matakin da wata jam'iyyar siyasa [PDP] ta ɗauka.

"Muna da tabbas cewa ɗaukar wannan mataki hanya ce ta nuna kishi da kuma gina dunƙulalliyar ƙasa mai ci gaba."