Zaɓen shugaban Najeriya na 2023: Gwamnonin Arewa sun janye wa ƴan kudu takarar shugaban ƙasa

Buhari da 'yan takara

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, A baya Buhari ya nemi gwamnoni su goyi bayan ɗan takarar da yake so

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya shawarci masu neman takarar shugabancin ƙasar a jam'iyyar APC su sasanta a tsakaninsu don amincewa da mutum ɗaya ya wakilci jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasar na 2023.

Shugaban ya ba su shawarar ce yayin wata ganawa da ya yi da su a daren ranar Asabar a fadarsa da ke Abuja.

Dukkan masu neman takarar sun halarci wannan ganawa, ciki har da jagoran jam'iyyar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, wanda a baya-bayan nan ya furta wasu kalamai kan shugaban da suka tayar da ƙura.

Sai dai yayin wata hira da BBC Hausa, mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya musanta rahotannin da wasu kafafen yaɗa labaran Najeriyar ke yaɗawa cewa shugaban ya goyi bayan kai mulki Kudu.

bUHARI

Asalin hoton, BUHARI

''Wannan magana ba ta taso ba, abin da kawai ya ce shi ne su tattauna su fitar da mutum guda a cikinsu, kuma ya nuna cewa a matsayinsa na shugaba a shirye ya ke ya ba da jagoranci don ganin cewa hakan ta tabbata'' in ji shi.

Gabanin ganawar, an yi ta tunanin cewa a lokacin ne Shugaba Buhari zai fadi wanda yake goyawa baya gabanin zaɓen fitar da gwani na APC da ake sa ran gudanarwa cikin makon da za a shiga.

Amma Garba Shehu bai kore yiwuwar hakan ba, inda ya ce idan shugaban ya yi shawara da waɗanda suka kamata to akwai yiwuwar a yi irin abin da aka yi lokacin zaben shugaban APC da aka yi baya bayan nan, inda Buharin ya goyi bayan Abdullahi Adamu a ƙurarren lokaci.

Gwamnonin Arewa na APC na son a ba wa 'yan Kudu takara

Buhari da 'yan takara

Asalin hoton, Buhari da 'yan takara

Bayanan hoto, Gwamnonin Arewa 11 ne suka neman Buhari ya zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa daga Kudu

Kafin ganawar da Buhari ya yi da 'ƴan takarar, wata sanarwar hadin gwiwa da wasu gwamnonin APC 11 na arewa suka fitar ta bukaci dukkan masu neman takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar su janye don miƙa wa kudu mulki.

Gwamnonin sun bayyana cewa tattaunawar da suka yi a tsakaninsu ce ta ba su damar yin kiran ga APC da ta miƙa wa 'yan takara daga kudanci tikitin takarar, sannan ta nei 'yan takarar Arewa su janye.

"Bayan tattaunawa cikin natsuwa, muna so mu bayyana matsayarmu cewa bayan mulkin shekara takwas na Shugaba Muhammadu Buhari, ya kamata ɗan takarar APC na zaɓen 2023 ya fito daga 'yan jam'iyyarmu na kudancin Najeriya," a cewar gwamnonin.

"Magana ce ta kimar APC da kuma hukuncin da ba shi da wata alaƙa da matakin da wata jam'iyyar siyasa [PDP] ta ɗauka.

"Muna da tabbas cewa ɗaukar wannan mataki hanya ce ta nuna kishi da kuma gina dunƙulalliyar ƙasa mai ci gaba."

Idan Buhari bai amince da shawararmu ba dole mu janye - Gwamnan Jigawa Badaru

Badaru da Buhari

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar ya ce yana jira Buhari ya ba shi umarni game da janye takararsa

Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar ya ce idan Sugaba Muhammadu Buhari bai amince da shawararsu ta ba wa 'yan takarar kudancin Najeriya tikitin takarar shugaban ƙasa na APC ba dole su janye.

Badaru ya faɗa wa BBC Hausa cewa ya yi mamakin ganin takardar da ta karaɗe shafukan zumunta cewa an amince da matasayin gwamnonin Arewa na miƙa wa ɓangaren Kudu takarar, yana mai cewa shawara ce kawai.

"Haƙiƙanin gaskiya shawara ce za a kai wa baba [Buhari], idan ya amince a ɗauki wannan mataki, idan bai amince ba kuma a ci gaba da shawarar da ya bayar tun da dukkanmu gwamnonin Arewa masu biyayya ne gare shi," a cewar gwamnan wanda shi ma mai neman takarar ne.

"Dukkanmu da muka gana babu wanda Buhari zai faɗi abu ya ce ba daidai ba ne...idan bai amince ba dole mu ajiye wannan magana tamu."

Kazalika ya ce gwamnonin Kebbi da na Filato da na Nasarawa suka naɗa don su kai wa Buhari shawarar.

Game da janyewar tasa takarar, Gwamna Badaru ya ce ba zai iya janyewa ba sai abin da Buhari ya ce.