Zaben 2023: Mayar da mulki kudancin Najeriya shi ne adalci - Kabiru Gaya

Kabiru Gaya

Asalin hoton, Kabiru Gaya / Facebook

Wani dan majalisar dattawan Najeriya daga jam'iyya mai mulki ta APC ya ce ya kamata jam'iyyarsu ta tsayar da dan takarar shugaban kasar daga yankin kudancin kasar, kamar yadda aka yi alkawari a baya.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce bai wa yankin kudanci takarar shi ne babban alheri da adalci ga APC, kuma a cewarsa zai sa ta ci zabe a shekarar 2023.

Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa ana zaman dar-dar a jam'iyyar ta APC gabanin zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya tara gwamnonin jam'iyyarsu, tare da shaida musu cewa ya zabi wanda zai gaje shi kuma yana son su goya masa baya.

Sai dai rahotanni sun ce wadannan kalamai ba su yi wa wasu gwamnonin dadi ba.

A tattaunawa da BBC Hausa, Sanata Gaya ya ce: "Ita siyasa, ko ma duk rayuwar duniya, alkawari ce. Idan ka yi wa dan Adam alkawari, to ka cika alkawarin da ka yi da shi. An yi alkawari da kudu cewa su amince Buhari ya yi mulkin shekara takwas, ya kamata kuma a mika musu, domin su ma su yi shekara takwas."

Da aka tambaye shi cewa babu wanda ya ga wannan yarjejeniyar karba-karba kuma ba ta cikin tsarin mulki, sai ya ce: "Ai na san ba rubutawa aka yi ba, amma idan ka yi alkawari da mutum, ko da baki ne ba sai ya rantse maka ba."

Ya kuma tabbatar cewa a ganinsa takara kudu za ta tafi a jam'iyyarsu ta APC mai mulkin Najeriya.

"In sha Allah kudu (takarar) za ta domin shi ne alheri ga APC, kuma shi ne alheri ga Najeriya. Su ma 'yan kudun 'yan Najeriya ne, bai dace a ce kullum sai arewa ce za ta yi mulkin Najeriya ba."

Ya ce ba yana nuna kiyayya ga arewacin kasar ba ne, amma ya ce adalci shi ne ginshiki inda ya kara da cewa idan aka sami adalin shugaba, ko daga ina ya fito sai a mara masa baya."

A halin da ake ciki, jam'iyyar ta APC ta kammala tantance masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a inuwarta a ranar Talata.

Abin da ya rage mata, shi ne zaben fitar da gwani, kafin ta tunkari babban zaben da ke tafe a shekara mai zuwa.

Abin jira a gani shi ne ko gwamnonin APC za su yi wa Shugaba Muhammadu Buhari biyayya ta hanyar yi wa dan takarar da ya zaba mubaya'a kamar yadda a kullum suke fadin suna yi masa biyayya ko akasin haka.