Babangida Aliyu: 'Yan Najeriya na kewar shekaru 16 na mulkin PDP

Mu'azu Babangida Aliyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Babangida Aliyu ya shafe shekara takwas yana mulkin jihar Neja daga shekarar 2007 zuwa ta 2015

Tsohon gwamnan Jihar Neja da ke arewacin Najeriya ya ce 'yan kasar suna kewar mulkin jam'iyyar PDP na tsawon shekara 16 shi ya sa suke son sake zabenta a 2023.

Ya bayyaha haka ne a lokacin da jam'iyyar PDP ta mika wa Alhaji Atiku Abubakar shaidar zama dan takarar ta a zabe mai zuwa.

Atiku Abubakar ya ce ya daura damarar fara yakin neman zabe domin tabbatar da karbe ragamar Najeriya a 2023.

A tattaunawarsa da BBC, Mu'azu Babangida Aliyu, wanda shi ne shugaban tsofaffin gwamnonin jam'iyyar ta PDP, ya bayyana shirinsu na tunkarar zaben badi.

Ya ce: "Na daya mu a jam'iyyarmu, mun tsayar cewa shugaban jam'iyyar zai fito ne daga kudu. Sai wani wanda ke ganin yana da wayo ya sa muka dawo da mukamin arewa, inda matakin ya sa muka bar kowane dan Najeriya ya nemi takara, muka kuma yi shi a rubuce. To kaga tsarin karba-karba an yi shi ne domin a sa harsashin gina dimokradiyya. Amma bayan wani lokaci, sai a bari duk wani mai kwazo ya fito."

BBC: Amma ba ku da farga cewa APC na iya muku bi-ta-da-kulli a lokacin zabe mai zuwa?

Babangida Aliyu: "A'a, wannan kuma na Allah ne. Kuma duk abin da za su yi ba zai hana mu samin kuri'u daga can ba."

BBC: Kaman kuna sane da shirin da jam'iyya mai mulki ke yi na ci gaba da rike mukamin shugaban Najeriya?

Babangida Aliyu: "Wallahi ba komai. Ba Allah ne ya kawo su ba? Ai da Alah ya tashi kawo su, da mu yayi amfani, ya sa wasunmu suka koma jam'iyyarsu. Kar ka manta cewa gwamnoni biyar suka fita daga PDP suka koma jam'iyyarsu. Da wadannan gwamnonin biyar ba su fita ba, da babu inda za su kai."

BBC: Shin wadanne abubuwa kuke son sa wa a gaba idan kuka sami damar komawa bisa karagar mulki?

Babangida Aliyu: "Dan takararmu ya ce akwai abu biyar da ya ce zai mayar da hankali akai. Cikinsu, na daya shi ne hadin kai, na biyu tabbatar da tsaro domin da ma babban aikin gwmanati ke nan, cewa ta tsare rayuka da dukiyoyin al'umarta."

Ya kuma kara da cewa, "Allah ya taimake mu. 'Yan shekaru 16 nan da muka yi kan mulki sun shiga zukatan 'yan Najeriya har ta kai ga suna kewar mu saboda tabarbarewar da abubuwa suka yi a yanzu."