Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 29 ga Mayu zuwa Asabar 04 ga watan Yuni 2022.

Tantance ƴan takarar shugaban ƙasa na APC

Yan takarar APC

Asalin hoton, Other

Jam'iyyar APC ta tantance mutanen da ke neman takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwarta domin gadar shugaba Buhari

Shugaban jam'iyyar Abdullahi Adamu a ranar Asabar ya ce dukkanin ƴan takarar 23 suna nan ba a cire ko ɗaya ba.

A ranar Juma'a kwamitin tantance ƴan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC ya ce ya zubar da mutum 10 daga takarar zaɓen fitar da gwanin da jam'iyyar za ta yi a ranar Litinin zuwa Laraba.

Shugaban kwamitin tantance ƴan takarar John Oyegun ne ya faɗi haka yana mai cewa mutum 13 kawai jam'iyyar ta tantance.

A cewar Oyegun, APC ta tantance mutum 13 ne daga cikin 23 da suka sayi fom suka tsaya takarar.

Ya ƙara da cewa ƴan takarar masu ƙarancin shekaru ne kawai ne suka yi nasara a tantancewar.

Sai dai shugaban kwamitin bai faɗi sunayen ƴan takarar guda 10 ba da aka cire sunayensu.

Tinubu ya tayar da ƙura

Bola Tinubu

Asalin hoton, FACEBOOK/ BOLA AHMED TINUBU

Tsohon gwamnan Jihar Legas Bola Ahmed Tinubu ya tayar da ƙura bayan bugun ƙirjin da ya yi cewa ba don taimakonsa ba da Muhammadu Buhari bai zama shugaban ƙasa ba

Kalaman na Tinubu sun haddasa muhawara tsakanin ƴan Najeriya, musamman kasancewar matsayinsa a jam'iyyar na jagora da kuma hayaniyar shirin tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC.

"Tun da ya zama shugaban ƙasa ban taɓa samun wasu kwangiloli ba, ban taɓa samun kujerar minista ba, ban taɓa roƙar sa komai ba, amma fa ina faɗa cewa lokacin Yarabawa ne...ni ma ina so na zama shugaban ƙasa," in ji Tinubu yayin kamfen din da ya je yi a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun ranar Alhamis.

Yayin jawabinsa, Tinubu ya roƙi wakilai masu jefa ƙuri'a wato daliget da su mara masa baya, kada su mayar da zaɓen a matsayin "ƙabilanci" yayin da ya rage kwana uku kacal jam'iyyarsu ta APC mai mulkin kasar ta gudanar da zaɓen fitar da gwani.

Bayan kalaman sun tayar da ƙura, daga baya Tinubu ya ce fito ya ce ba a fahimci kalamansa ba ne, yana mai cewa yana matukar mutunta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kuma ba zai taba raina shi ba.

'Yan takara fiye da 20 ne ke neman a ba su takarar, ciki har a Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo - wanda Tinubu ya ce shi ne ya ba da sunansa a matsayin mataimakin Buhari - ɗan ƙabilar Yarabawa kuma daga yankin kudu maso yamma kamar Tinubu.

Rikici tsakanin mayakan Bello Turji da abokan gabarsa ya jawo mutuwar 'yan bindiga da dama a Zamfara

Yan bindiga

Asalin hoton, Other

Yan bindiga da dama ne rahotanni suka ce sun mutu sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin gungun ƙasurgumin ɗan fashin daji Bello Turji da wasu 'yan fashi abokan gabarsa a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

Bayanai sun ce 'yan bindigar da ke kashewa tare da garkuwa da mutane sun fara fafatawa a tsakaninsu tun daga ranar Litinin zuwa Talata lokacin da Bello Turji ya jagoranci wani samame kan tawagar fitaccen ɗan fashi mai suna Dullu.

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa harin ya yi sanadiyyar kashe Dullu tare da gwamman mayaƙansa kusan 30.

Mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Maniya da ke Jihar Zamfara, wanda ya yi sanadiyyar kashe gwamman 'yan bindiga daga ɓangarorin biyu.

Bayan Dullu da aka kashe, an kashe wani babban ɗan fashi mai suna Ɗan Maigari.

Bayanai sun bayyana cewa harin da Turji ya kai na ramuwar gayya ne sakamakon kashe wasu 'yan uwansa da gungun Dullu suka yi a kwanakin baya.

Karancin dalar Amurka na kokarin durkusar da masana'antu a Najeriya

kamfani

Asalin hoton, Other

Kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya sun koka kan yadda ba sa iya samun dalar Amurka daga babban bankin kasar don shigo da hajoji a daidai lokacin da farashinta ya tashi a kasuwar bayan-fage.

Kungiyar masu masana'antun ta ce sun dade suna kokawa ga gwamnati kan yadda tashin dalar da karancinta yake shafar kasuwancinsu, amma ba a yi komai kan hakan ba.

Masu masana'antu na wannan furuci ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar farashin kayan masarufi tare da tashin farashin dala a kasuwannin bayan-fage da ke kasar.

Alhaji Aliyu Sufyanu Madugu, mataimakin shugaban kungiyar masana'antu masu zaman kansu a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa rashin samun dalar Amurka yana gab da durkusar da masana'antunsu, sakamakon yadda ba sa iya samar da kayayyakin da suka dace.

Ya ce: ''Ba wai tashin farashin dala kadai ake magana anan ba, a'a babu dalar ce ma baki daya, duk wanda ya ke da masana'anta a Najeriya ya ke sarrafa wani abu, ya kuma ke kawo kayan aiki daga waje, ko na gyara ya na cikin matsanancin hali.

An haramta cin naman daji a Najeriya saboda kyandar biri

Naman daji

Gwamnatin Najeriya ta harantar sayar da naman daji a matsayin matakin kariya domin daƙile yaɗuwar cutar ƙyandar biri.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan cibiyar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta ce mutum shida sun kamu da ƙyandar biri a Najeriya a watan Mayu, kuma mutum ɗaya ya mutu sakamakon cutar.

Kyandar biri, cutar da ƙwayoyinta ba su da ƙarfi, na yaɗuwa a Najeriya a yankunan ƙauye, musamman inda suke da matsanancin zafi.

An taɓa samun ɓullar cutar a 2017.

Dabbobin da kan iya yaɗa cutar su ne nau'ukan su ɓera da zomo.