Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wani daliget ya raba wa 'yan garinsu kuɗin da ya samo a zaɓen fitar da gwani na PDP
Wani daliget na jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, wanda ya samu kuɗi lokacin zaɓen fitar da gwani, ya raba kudin ga jama'ar karamar hukumarsa ta Sanga da ke Jihar Kaduna.
Mutumin mai suna Tanko Rossi Sabo ya wallafa a shafinsa na Facebook yadda ya raba wa mabuƙata miliyoyin kuɗi bayan ya koma gida.
An yi zargin cewa wasu masu neman takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar PDP sun raba maƙudan kuɗaɗe da suka hada da dalar Amurka ga daliget domin su zaɓe su.
Sai dai jam'iyyar ta PDP ta musanta zargin.
Lamarin ya sa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta aike da jami'anta filin zaben fitar da gwanin inda aka gan su suna sanya ido kan abubuwan da ke wakana a dandalin.
Akwai rahotanni daban-daban kan adadin kuɗaɗen da ya samu, inda wasu ke cewa sun kai naira miliyan 12, sai dai hotunan da ya wallafa sun nuna ya raba kusan naira miliyan bakwai.
Me ya ja hankalinsa ya raba kuɗin?
Tanko Rossi Sabo ya shaida wa BBC cewa babbar takardar karatu da ya mallaka ita ce ta kammala makarantar sakandare.
Ya ce "shi ya sa na ga idan har wannan takardar tawa ta sakandare tana iya taimakona a rayuwa, to ni kuwa zan yi ƙoƙari na ga cewa na tallafawa yara ƴan makaranta da kuɗin jarabawar WAEC ko da mutum ɗaya saboda damar da na samu.
Ko gaba ɗaya ya raba wa al'umma kuɗaɗen?
"E, na farko na yi wa yara 150 rijistar NECO da WAEC, kuma kowane yaro ɗaya rijistarsa naira 46,000 ne, idan ka yi lissafin 46,000 sau 150 zai ba ka miliyan 6,900,000.
To ko nawa Mista Sabo ya samu a hidimar daliget ɗin da har ya yi waɗannan ayyuka?
"Kudin daliget din ba wani na a zo a gani ba ne, don daga kudin otel sai na abinci sai kuma ɗan kaɗan da ba a rasa ba. Amma mutane sun bayar da gudunmowa don jin wannan niyya ta alheri da na yi.
"Abin da na kashe a hidimar ya fi kuɗaɗen da daliget ya samu, wannan dai sun samu ne dalilin mutanen da suka ba da gudunmowa."
Sai dai Mista Sabo ya ce shi bai yi ciniki da kowa a harkar zaben fitar da gwani ba, kuma bai karbi makudan kudaden kowa don zabarsa ba, yana mai cewa "ba zan sayar da darajar ƴan ƙasa, dole na zaɓi wanda ya fi cancanta kuma zai kawo sauyi a ƙasar nan."
Abin da aka yi da kuɗin da honorabul Tanko ya bayar
Ɗan jarida kuma tsohon mai ba wa tsohon Gwamnan Kaduna Ibrahim Yakowa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Rueben Buhari, ya faɗa BBC Hausa cewa da ma tun kafin ya zama daliget Tanko ya yi wa jama'ar mazaɓarsa alƙawari.
"Da ma tun lokacin da yake takara ya faɗa wa 'yan mazaɓarsa cewa idan suka zaɓe shi a matsayin daliget na ƙasa zai kawo duk abin da ya samu a raba," in ji Rueben.
Abubuwan da aka yi da kuɗin sun haɗa da sayen rigunan ƙwallon ƙafa da biyan kuɗin makaranta da asibiti ga mutane. Ya kuma raba sauran kuɗaɗen ga magoya bayansa.
Mista Tanko ya ce ko wacce irin muhawara ko suka da za a tafka bai dame shi ba, tunda dai duk abin da ya samo ya dawo gida ya sanya farin ciki a fuskokin al'ummarsa.
Tanko Rossi na cikin delegates din Kaduna da suka halarci taron PDP na kasa inda aka gudanar da zabe da tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takara a PDP.