Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda rogo zai taimaka wajen shawo kan matsalar hauhawar farashin kayan masarufi
A cikin jerin wasikunmu daga 'yan jaridun kasashen Afirka, 'yar kasar Ghana Elizabeth Ohene ta yi nazari kan kiran da shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya yi ga mutane da su ci rogo yayin da farashin alkama ke kara hauhawa a duniya.
Rogo da doya su ne manyan kayan abinci guda biyu a Yammacin Afirka .
Rogo yana samuwa duk shekara, yana da araha kuma za a iya cewa an san shi a matsayin abincin marasa galihu.
Dayan kuma ita ce doya, wadda marubucin nan dan Najeriya Chinua Achebe ya bayyana a matsayin "sarauniyar amfanin gona".
Mutane da dama a Afrika kan yi ta zaman jiran lokacin da za a girbe doya. Hakika, ana yin bukukuwa na musamman kafin a ci sabuwar doya, kuma muna sanya tufafinmu masu kyau don bikin fitar sabuwar doyar.
Rogo kuwa ya kasance abincin yau da kullum na talaka.
Na lura cewa Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya yi kira ga al'ummarsa da su koma cin abinci irin su rogo a matsayin maganin tashin farashin alkama a lokacin da ake fama da matsalar tsadar rayuwa a duniya.
"Idan babu burodi, ku ci muwogo watau [rogo]," in ji shi.
Sai dai kalaman Mr Museveni sun janyo ce-ce-ku-ce, inda masu suka suka ce ba shi da wani kwakkwaran shiri kan yadda za a shawo kan matsalar tsadar rayuwa.
A nan kasar Ghana, mun taba samun wani Ministan Kudi a shekarun 1960 da ya yi kokarin kare matakin harajin da aka kara a kan cewa shirin ba zai shafi talaka ba saboda abincinsu shi ne garin kwaki .
A wannan lokacin an fi sanin gari a matsayin abinci ga talakawa kuma ministan ya bayyana cewa idan ka zuba ruwa a cikin rabin kofi na garin zai kumbura don a samar da isasshen abinci ga mutum uku. Yana da araha kuma yana kosarwa.
Ministan ya kuma yi wannan magana, ba tare da fada wa mutane cewa talakawa ba sa cin biredi ko shinkafa, ko wasu irin kayan marmari da ake shigo da su daga waje ba. Wannan gaskiya ne sosai a wancan lokacin.
Bayan shekaru da yawa, mun samu wani karamin minista wanda ya yi magana game da hauhawar farashin kayan abinci da cewa a ko da yaushe mutane za su iya cin kokonte, wanda ya ba da misali da shi a matsayin madadin shinkafa da sauran kayan abinci da ake shigo da su saboda araharsa.
Ana yin kokonte ne daga garin rogo kuma kamar sauran abubuwa da ake yi da rogo, shi ma an san shi a matsayin abincin da talakawa ke ci.
Shugaba Museveni ya yi maganar cewa shi ma yana cin rogo. Wato, kada kowa ya ji kunyar ci, ko a gan shi yana cin rogo tunda yanzu abincin shugaban kasa ne.
A 'yan kwanakin nan, an bayyana alfanun amfanin gona mai jure fari ga lafiyar bil'adama - tushen rogo ba shi da sinadarin gluten, mai yawan bitamin C da kuma sinadarin copper.
Ban sani ba ko har yanzu ana yi wa rogo kallon abincin matalauta a Uganda, amma a Ghana al'amarin ya sauya.
Misali garin kwaki a yanzu matsayinsa ya tashi daga abincin talaka ya koma abincin daliban makarantar kwana.
Suna zuwa makaranta da jakar gari a cikin "akwatunansu". Abinci iri-iri da suke yi da gari a dakunan kwanan dalibai su ake kira soaks.
Yana da sauri da sauƙi, ba ya buƙatar dafawa ko a saka shi cikin makiroweb don dumama - za ka iya saka gari a cikin kofi, ƙara ruwa, sukari da madara, gauraye shi ke nan. Ka samu abin ciye-ciye mafi daɗi kuma mai kosarwa.
Wata hanya da ake amfani da garin kwaki ita ce amfani da kofi guda na busasshen gari, a yayyafa masa ruwa kadan don ya yi laushi, a zuba cokali guda na shahararren barkono namu, shito, a zuba gwangwanin kifi na sardine, a hade gaba daya - da hey presto, ka hada abinci mai dandano gaske ko da yake wannan abinci ne da ya fi dadin ci tare da 'yan uwa da abokan arziki.
Amma garin ya kara samun karbuwa a lokacin da fitacciyar mai girke-girken abinci ta Ghana, Barbara Baeta, ta ƙirƙiro wasu girke-girke da ake kira "gari foto" - gari da aka gauraye da nama da halittun teku, wanda aka ci a wata liyafa ta jiha a 1970 wadda Firaminista Kofi Abrefa Busia ya shirya.
Nan da nan gari ya zama abincin da ake hidima a wurin taron masu hannu-da-shuni.
A wasu hanyoyi, abinci iri-iri da aka yi da rogo sun zama abincin da mutane ke alfahari da shi.
Ba kamar yadda aka samu a shekarun 1960 lokacin da Amukawa bakar-fata suka rungumi abin da suka ci a matsayin bayi suka mayar da shi abinci na zamani da ake kira " Soul Food".
Ina tsammanin akwai damar da wasu masu girke -girken abinci a Ghana za su samu idan suka je Uganda su kafa gidajen abinci waɗanda za su dafa abincin rogo kawai.
Kuma ina fata cewa a lokacin da aka kawo karshen yakin Ukraine, rogo zai zama abincin zabi a fadin Afirka kuma za mu bar alkama ga masu noma.
Duk da cewa yanzu Chinua Achebe ba ya nan balatana ya yi wa rogo waka, kuma wataƙila ba za mu yi bikin rogo ba amma babu wanda zai sake kiransa a matsayin abincin matalauta, kuma Shugaba Museveni ba zai yi jawabi don ƙarfafa mutanensa gwiwa su ci rogo.
Wasu wasikun daga Afirka: