Abin da ya sa Afirka ta kasa shawo kan kwararar hamada

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Navin Singh Khadka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Environment correspondent, BBC World Service
Afrika ta sha fama da fari har sau goma sha huɗu a cikin shekara biyu kacal - hakan ya wuce adadin na kowace nahiya - haka kuma Majalisar Ɗinkin Duniya na gargaɗin cewa akwai mutum miliyan 20 da ke cikin hatsari a Gabashin Afrika bayan ba a samu ruwan sama ba kuma.
Hakan ya yi daidai bayan da Ivory Coast ta karɓi taron da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya kan irin illolin da fari da kwararowar hamada suka jawo.
Sai dai ba a cimma wani abin kirki ba a yayin taron da aka yi na tsawon mako biyu a Abidjan domin shawo kan waɗannan matsalolin.
Ƙasashen Afrika da dama na ganin cewa akwai buƙatar a cimma matsaya a duniya baki ɗaya kan yadda za a shawo kan fari - kamar shirin Kyoto protocol da aka ƙaddamar a 1997 domin rage fitar da hayaƙi mai gurɓata muhall.
Uganda da Angola na daga cikin ƙasashen da za su samar da abubuwan da ƙasashen Afrika ke buƙata.
Amma suna ta mayar da hankali wajen ganin cewa wannan lamari ba na Afrika bane kaɗai - suna so batun fari a ɗauke shi da muhimmanci a duniya baki ɗaya da kuma mayar da hankali wajen ganin cewa idanun duniya sun karkata a gareshi.
Sun bayyana cewa sauyin yanayi ne ke jawo fari wanda sai ƙasashen duniya sun haɗa hannu ne kaɗai za a iya magance matsalar, duk da cewa a Afrika batun fari da kwararowar hamada abu ne da ya yi ƙamari.
"Wannan babban lamari ne, ba wai a Afrika kaɗai ba, in ji Kabango Freddie wanda mai shiga tsakani ne.
'Muna ganin idan duka waɗanda ke cikin wannan aikin na Majalisar Dinkin Duniya suka haɗa kansu domin magance wannan matsala, za mu iya taimakon alu'ommin da fari ya yi wa illa ko kuma yake shirin yi wa illa."
Sai dai wannan buƙatar ba ta samu karɓuwa ba daga sauran sassan duniya. Sun bayyana cewa akwai wasu tsare-tsare da ke da akwai a ƙasa waɗanda za a yi amfani da su domin magance wannan matsalar.
Argentina da Jamhuriyyar Dominican waɗanda ke wakiltar Latin Afrika da Caribbean sun bayyana cewa ana mayar da hankali sosai wajen bayar da gudunmawar kuɗi da ƙarfi domin taimaka wa ƙasashen da ke buƙatar taimako.
A ƙarshe, an cimma matsaya - an ɗage batun wata matsaya da aka cimma na matakin da aka ɗauka na shekara biyu domin samar da wata ƙungiya ta tsakanin gwamnati da gwamnati da za ta yi aiki wajen ɗaukar matakan kiyaye fari.
Rasa gonaki suna jawo rikici
Wani rahoto da aka fitar a lokacin tattaunawar, adadin farin da aka samu ya nuna cewa cikin ƙasashe 23 da suka samu tsananin fari a cikin shekara biyu da suka wuce, guda 14 a nahiyar Afrika suke.
"Afrika ta sha baƙar wuya sakamakon yawan farin da ake samu fiye da kowace nahiya inda aka samu fari har sau 134 tsakanin 2000 zuwa 2019 inda har guda 70 aka yi a Gabashin Afrika," in ji rahoton

Asalin hoton, Getty Images
Kashi biyu cikin uku na nahiyar Afrika sahara ce da kuma busashiyar ƙasa, hakan na nufin babu isahiyar ƙasa da za a fara da ita. Domin ƙara ƙazanta lamura, kashi 65 cikin 100 na gonakin da ke da akwai a Afrika igancinsu ya ragu.
Ƙasashen noman da ake da su akasarinsu sun lalace sakamakon rashin tafiyar da su da kyau a harkar noma da kuma ƙaruwa a samar da abinci.
Bayanai sun nuna cewa Afrika na yin asarar kadada miliyan huɗu a duk shekara haka kuma samar da gawayi ya zama babbar barazana da ga dazuka a ƙasashe da dama
Sannan hukumar UNCCD ta ce kwararowar hamada na shafar kashi 45 cikin 100 na Afirka.
Kokarin farfado da shuke-shuke
Tun shekarar 1999 mafi yawan ƙasashen Afirka suka fitar da tsare-tsare don shawo kan kwararar hamada.
Amma wani bincike da Hukumar Abinci Ta Majalisar Dinkin Duniya da wata hukuma ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka suka wallafa a bara ya gano cewa babu wata nasarar a zo a gani da aka cimma,
Wani rahoton da ak sake fitarwa kafin taron ya ce kashi 4% da 2% ne kawai aka cimma a 2020 daga ainihin abin da aka so a cimm ɗin a shirin na Great Green Wall.
A shekarar 2007 ne aka ƙaddamar da shirin da zummar dasa miliyoyin bishiyoyi don farfaɗo da eka miliyan 100 na fili a fadin ƙasashe 11, tun daga Senegal daga gefen Afirka ta Yamma har zuwa Djibouti daga gabas zuwa 2030.

Asalin hoton, Getty Images












