IPOB: 'Yan Najeriya sun fusata kan 'kisan mace mai ciki da ƴaƴa huɗu' a Anambra

Asalin hoton, AFP
Jama'a da dama a shafukan sada zumunta musamman ƴan arewacin Najeriya sun fusata sakamakon wani bidiyo da ake ta yadawa da ke nuna yadda aka kashe wata mata da yara a Jihar Anambra da ke kudancin Najeriya.
Wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne suka kashe matar mai suna Harira Jibril, mai shekara 32, da ƴaƴanta Fatima, mai shekara tara, da Khadijah, mai shekara bakwai, da Hadiza, mai shekara biyar, da Zaituna, 'yar shekara biyu da wasu aƙalla mutum shida a jihar.
Ƴan sandan Najeriya sun tabbatar da kisan inda suka ce suna neman waɗanda suka aiwatar da wannan aika-aika.
BBC ta tattauna da mijin matar mai suna Jibril Ahmed wanda a cewarsa matar tasa wadda ke ɗauke da cikin wata tara na hanyar dawowa daga ziyarar da ta kai tare da yaransu Orumba North wanda a hanyar ne aka tare su aka kashe su.
Alhaji Usman Abdullahi wanda shi ne Sarkin Hausawan Ihiala a Anambra shi ma ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce matar asalin ƴar Jihar Adamawa ce daga arewacin Najeriya.
Sarkin Hausawan wanda yanzu haka yake gudun hijira ya ce al'ummar Hausawa na cikin wani hali a Jihar Anambra.
A cewarsa, a Ƙaramar Hukumar Ihiala wanda a nan yake, babu wani Bahaushe da ya rage sakamakon duk sun yi gudun hijira saboda barazanar ƴan Ƙungiyar ta IPOB.
Ko a kwanakin baya sai da wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne suka kashe wasu sojoji biyu da suke shirin yin aure a Jihar Imo.
- Sojojin-baka na Ipob da ke kira a kashe mutane a Facebook a Najeriya
- Deborah Samuel: Labaran karya da ake yadawa kan batancin da ake zargin an yi kan Annabi
- Sokoto: Zanga-zanga ta ɓarke kan kamen da 'yan sanda suka yi bayan kashe Deborah Samuel
- Sojojin Najeriya sun zargi 'yan Ipob da fille kan wasu jami'ansu da ke shirin aure
Me ƴan Najeriya ke cewa kan wannan kisa
Ƴan Najeriya da dama sun fusata kan wannan lamari inda da dama ke kokawa kan yadda jaridun ƙasar da dama suka ƙi ɗaukar wannan labari da muhimmanci ko kuma bibiyarsa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Muhammad MK a shafin Twitter kira ya yi da a daina kashe mutanen arewa inda ya rubuta mau'du'in a yi wa waɗanda aka kashe a Anambra adalci.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Adam Aliyu a shafin Twitter tambaya ya yi kan cewa ina masu magana kan kare hakkin bil adama inda yake cewa waɗannan da aka kashe suna da ƴancin su yi rayuwa ko don suna daga arewacin Najeriya ne.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Ilyas Tahir cewa ya yi shugabannin arewa tamkar babu su inda ya ce ba su damu da abubuwan da ke faruwa ba kuma suna iƙirarin suna wakiltar jama'a.