Deborah Samuel: Labaran karya da ake yadawa kan batancin da ake zargin an yi kan Annabi

Zanga-zanga a Sokoto

Asalin hoton, Murtala ST

Bayan kisan Deborah Samuel, ɗalibar shekara ta biyu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu saboda zargin ɓatanci ga Manzon Allah (SAWA), labaran ƙarya sun karaɗe shafukan sada zumunta.

Yaƙin cacar-baka ya ɓarke musamman a dandalin Twitter da Facebook tsakanin Musulmai da Kirista a Najeriya, inda ɓangarorin ke zargin juna da tsattauran ra'ayi da kuma rashin jumuri.

Kwana biyu da faruwar lamarin, zanga-zanga ta ɓarke a garin Sokoto, ana neman jami'an tsar su saki mutanen da suka kama bisa zargin kashe Deborah.

BBC ta fahimci cewa da farko zanga-zangar ta lumana ce, kafin daga bisani ta rikide zuwa rikici, inda mutane suka dinga jefa duwatsu kan gidan Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Tuni aka dinga yaɗa hotuna da bidiyo na boge a shafukan zumunta da zimmar tayar da tarzoma da kuma ƙara kunna wutar rikici. Da yawan saƙonnin na ƙunshe da bayani kan dalilin da ya sa masu yaɗa su ke cewa sai an raba Najeriya tsakanin Musulmai masu rinjaye a arewaci da kuma Kiristoci da suka fi rinjaye a kudanci.

Iƙirarin kashe Kiristoci a Sokoto

Emeka Fans Page

Asalin hoton, Facebook

Wani shafin Facebook mai suna Emeka Fans Page ya wallafa wani bidiyo bayan gudanar da zanga-zanagar Sokoto. Daga cikin iƙirarin da ya yi har da cewa "mutanen Sokoto sun kashe dukkan Kiristoci a jiharsu".

An kalli bidiyon nasa sau fiye da 670,000 kuma aka yaɗa ta sama da sau 5,000. Ya kuma mabiyansa da su ci gaba da yaɗa bidiyon.

Wata sanarwar 'yan sanda ta ce an harbi mutum biyu da suka yi yunƙurin afka wa fadar sarkin Musulmi.

Akwai bidiyo na haƙiƙa da suka nuna masu zanga-zanga na ƙona tayoyi a kan tituna kuma ɗauke da makamai tare da yin kabarbari. Kazalika, wani bidiyon ya nuna mutane na sace kayayyaki a wani shago.

Sai dai babu wata hujja da ke tabbatar da kisa ko yanka Kiristoci kamar yadda Emeka Fans Page ya yi iƙirari.

Bidiyon wata mace da ake duka da sanda

Bidiyo a Twitter

Asalin hoton, Twitter

Mutane da dama sun yaɗa wani bidiyon da ke nuna wata mace sanye da yagaggun kaya da maza ke dukanta da sanduna da igiya, wanda suke ta iƙirarin cewa Kirista ce da Musulmai a Sokoto ke ƙoƙarin kashewa.

Ana iya ganin wasu matan sanye da hijabi a gefe suna kallo yayin da ake cin mutuncin matar. Matar ta yi yunƙurin guduwa wani gida da ke kusa amma sai wasu maza suka koro ta. Ana kuma jin ta tana magana da Hausa tana cewa "ba zan sake ba, ku yafe min".

Sai dai binciken da Sashen Labaran Ƙarya na BBC ya gudanar ya gano cewa an fara yaɗa bidiyon tun shekara biyu da suka gabata.

Da farko ba a iya gane abin da ke faruwa a bidiyon, amma daga za a fahimci cewa an ɗauki bidiyon a Kaduna, kuma an kama matar ne da zargin sata da kuma sayar da yara.

Amma har yanzu mutane na yaɗa shi a shafukan zumunta da iƙirarin cewa na rikicin Sokoto ne. Wani ya ce "suna ta kashe Kiristoci yanzun nan, idan kuna da 'yan uwa a Sokoto..."

Hoton ɗan jaridar da aka ce na likita ne mai kashe 'yan Arewa

Dan jarida

Asalin hoton, Twitter

Wani hoton fuskar waya da ake yaɗawa a Facebook na iƙirarin nuna bayanan likita Christopher Uche-Ayodeji (Dr Chris) da ya "amsa laifin" barin Musulmai suna mutuwa da gangan lokacin da yake aiki a arewacin Najeriya.

Hoton na iƙirarin cewa Dr Chris na aiki ne da asibitin University Hospitals Birmingham. An ce ya yi iƙirarin cewa "ya ji daɗin dukkan" abubuwan da ya aikata saboda da ma ramuwar gayya ce ta kai shi yankin saboda kashe wata maƙociyarsa da aka yi yayin zaɓen 2015.

Wani shahararren mai amfani da dandalin Twitter, Gimba Kakanda, ya tura wa University Hospitals Birmingham saƙo ta dandalin game da Dr Chris. Asibitin ya mayar da martani da cewa bai san mutumin ba.

Amma har yanzu mutane na ci gaba da yaɗa shi, har ma cikin kuskure suka dinga haɗa hoton wani mutum cewa shi ne Christopher Uche-Ayodeji.

Sai dai kuma hoton na wani marubuci ne kuma ɗan jarida a Najeriya mai suna Ayodeji Rotinwa, wanda ya roƙi mutane su daina yi masa ƙage.

A Facebook, babu wani shafi na Christopher Uche-Ayodeji (Dr Chris) ko kuma saƙon da ake turawa.

Zargin ƙona gidan Matthew Hassan Kukah

Matthew Hassan Kukah

Asalin hoton, @KukahCentre

Wani labarin ƙarya da aka dinga yaɗawa shi ne na ƙona gidan baban malamin Kirista a arewacin Najeriya, Bishop Mathew Hassan Kukah na Cocin Sokoto Diocese yayin zanga-zangar Sokoto.

Sai dai wata sanarwa da cocin nasa ya fitar ranar Asabar ya ce yana nan lafiya ƙalau, yana mai musanta cewa an ƙona gidansa.

"Muna musanta cewa an kai wani hari kan gidan Bishop Matthew Hassan Kukah," a cewar sanarwar ta Catholic Diocese of Sokoto.

Sai dai ta ce wasu masu zanga-zangar sun kai wa ginin cocin Holy Family Catholic Cathedral hari tare da farfasa gilasai da kuma ƙona wata mota da ke ajiye.