Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 8 ga Mayu zuwa Asabar 14 ga watan.

Tarzoma a Sokoto kan zargin ɓatanci

Zanga-zanga a Sokoto

Asalin hoton, Murtala ST

Gwamnatin Jihar Sokoto ta saka dokar hana fita ta tsawon awa 24 a jihar sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke a ranar Asabar.

Masu zanga-zangar sun nemi jami'an tsaro su saki mutanen da suka kama da ake zargi da kisan matashiyar da ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, wadda suka zarga da zagin Annabi Muhammadu (SAW).

A ranar Alhamis ne wasu ɗalibai da mazauna yankin suka yi wata ɗalibar Kwalejin duka sannan suka ƙona gawarta saboda zargin ta zagin Manzon Allah a kafar na WhatsApp.

Matakin ya kai ga rufe makarantar yayin da ƴan sandan jihar Sokoto suka ce sun kama wasu matasa biyu da ake zarginsu da hannu a kisan da aka yi wa ɗalibar.

Gwamnati Sokoto ta ce ta ɗauki matakin saka dokar hana fita ne "saboda dawo da doka da oda a birnin Sokoto da jihar baki ɗaya."

Wasu ministocin Buhari sun yi murabus

Buhari

Asalin hoton, STATE HOUSE

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ban-kwana da wasu ministocinsa da suka ajiye aiki don yin takara a babban zaɓe mai zuwa na 2023.

Yayin jawabinsa a ranar Juma'a, Buhari ya ce ya yi imani da yawa daga cikin ministocin na da ƙwarewar da za su iya gadarsa.

A ranar Laraba ne Shugaban ya umarci dukkan ministoci da shugabannin hukumomi da ma'aikatu masu son tsayawa takara a muƙamai daban-daban da su ajiye ayyukansu kafin ranar Litinin.

Daga cikin ministocin da suka ajiye muƙamansu, sun haɗa da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da Ministan Neja Delta Godswill Akpabio da Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu da Ƙaramin Ministan Neja Delta Tayo Alasoadura da Karamin Ministan Ilimi.

Sai dai kuma wasu daga cikin ministocin rahotanni sun ce sun janye aniyar takararsu domin ci gaba da riƙe muƙaminsu na minista.

Wahalar man fetur ta dawo a Najeriya

Fetur

Ƴan Najeriya sun sake tsunduma cikin wahalar man fetur a jihohi da dama na ƙasar, lamarin da ya haddasa wahalhalu ga masu ababen hawa.

Tun da farko ƙungiyar manyan dillalan man fetur ta kasa a Najeriya ta yi barazanar dakatar da sayar da man fetur a faɗin ƙasar, har sai hukumar da ke daidaita farashin man fetur ta kasa ta biya ta kuɗaɗenta da mambobinta suke bin gwamnati.

Kungiyar ta IPMAN ta ce kimanin wata tara ke nan da hukumar ta yi burus da su, ba ta biyansu kuɗaɗensu da suka kai aƙalla naira biliyan dari 500 ba.

Shugaban Kungiyar dillalan man reshen arewacin Najeriya, Bashir Ahmed Dan Malam, ya shaida wa BBC cewa wannan ne ya sa mambobinsu suka janye daga dakon man fetur abin da ya haifar da dogayen layukan mai da aka soma gani a birnin tarayya Abuja da kuma wasu jihohin ƙasar.

Ya kuma yi gargadin cewa matsalar za ta yi kamari idan hukumar ba ta dauki matakin biyansu ba.

ASUU ta tsawaita wa'adin yajin aikinta

ASUU

Asalin hoton, Other

Ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya ASUU ta tsawaita yajin aikinta da mako 12 daga ranar Litinin 9 ga watan Mayun 2022.

Shugaban ƙungiyar Emmanuel Asodeke ne ya sanar da tsawaita yajin aikin a wata sanarwa da ASUU ɗin ta fitar, wanda ya ce an ɗauki matakin ne bayan da Kwamitin Zartarwa ya yi wani taron gaggawa a sakatariyar ƙungiyar da ke Jami'ar Abuja.

Mista Asodeke ya ce bayan tattaunawa sosai da gwamnati kan kawo ƙarshen yajin aikin zuwa yanzu ta gano cewa gwamnati ta ƙi ɗaukar haƙƙoƙin da suka ratayu a wuyanta kan batutuwan da ƙungiyar ta bujiro da su a shekarar 2020.

"Hakan ne ya sa muka sake tsawaita yajin aikin da mako 12 domin bai wa gwamnati lokaci don warware matsalolin da suke a ƙasa," in ji shi.

Majalisar wakilan Najeriya ta roki taimakon China don kubutar da fasinjojin jirgin kasa da aka sace

Jirgin kasa

Kwamitin kula da harkokin sufuri a majalisar wakilan Najeriya, ya roki gwamnatin China da ta taimaka wajen ganin an kubutar da fasinjojin jirgin kasan nan 62 da aka sace a ranar 28 ga watan Maris a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja.

Shugaban kwamitin Sanata Abdulfatai Buhari, wanda ya yi magana a madadin 'yan kwamitin a yayin wata ziyarar gani da ido da kwamitin ya kai tashar jirgin kasa ta Obafemi Awolowo da ke Ibadan ya bayyana rashin jin dadinsa a kan rashin kubutar da mutanen har kawo yanzu.

Sanatan ya ce harin da aka kai kan jirgin kasan ya sanya fargaba a zukatan 'yan Najeriya wadanda suka koma tafiye-tafiye ta jirgin.

Ya ce, ba laifi ba ne idan gwamnatin China ta zo ta taimaka wa Najeriya wajen ceto fasinjojin.

Kamfanin kasar China ne dai ya gina layin dogon da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna wanda ke da nisan kilomita 159.

Sanatan ya ce, gwamnatin China ta samu kudi daga irin ayyukan da kamfaninta na CCECC ya yi a Najeriya, don haka ba gazawa ba ce idan an nemi su zo su taimaka.