IPOB: Sojojin-baka masu son kafa Biafra da ke kira a kashe mutane a Facebook a Najeriya

protest in Rome

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai fafutikar kafa ƙasar Biafra, Efe Uwanogho (tsakiya) yayin wani maci na ƙungiyar Ipob a Italiya
    • Marubuci, Daga Disinformation Team
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Wani gungun 'yan Najeriya a wajen ƙasar da ke son kafa ƙasar Biafra na amfani da shafukan zumunta don haddasa tashin hankali da kuma tunzura magoya bayansu don far wa masu adawa da su, kamar yadda wani binciken BBC ya gano.

Gargaɗi: Wannan maƙalar na ƙunshe da bayanan tashin hanakali

Yayin wani shiri kai-tsaye a Facebook da take yaɗa wa mabiyanta fiye da 40,000, Efe Uwanogho wadda kuma aka sani da Omote Biafra, na ta yin kalaman ƙiyayya ta bidiyo.

"Ku far wa waɗannan manyan maƙiyan...Su ne mutanen da ya kamata a fille wa kawuna. Su ne waɗanda ya kamata a ƙona ƙurmus," a cewarta.

Gaban rigar da take sanye da ita na ɗauke da tutar Biafra - wadda ke ƙunshe da launin ja da baƙi da wani ɗan kore, sai kuma ƙwalln rana da ke fitowa.

Tana kira ne da a kai wa masu adawa da yunƙurin kafa Biafra hari, da ke son kafa sabuwar ƙasa a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Gwagwarmayar kafa Biafra na ƙunshe da tarihin zubar da jini.

A shekarar 1967 ne 'yan aware da akasarinsu 'yan ƙabilar Igbo ne suka ayyana 'yancin kai na Jamhuriyar Biafra.

Sun fafata yaƙin basasar da ba su yi nasara ba tare da gwamnatin Najeriya, inda aka kashe mutum fiye da miliyan ɗaya mafi yawansu daga ɓangaren 'yan tawayen.

Biafran soldiers seen here inspecting a bomb during the Biafran conflict, 11th June 1968.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gama yaƙin a 1970 amma aƙidar Biafra ba ta ƙare ba

Kusna rabin ƙarni bayan haka, shafukan sada zumunta sun zama filin dagar waɗanda suke son kafa Biafra har yanzu.

Ms Uwanogho na cikinsu. Ana yi mata laƙabi da "gwarzuwar kafar yaɗa labarai" ta ƙungiyar 'yan tawayen da ake kira Indigenous People of Biafra (Ipob).

Tana yaɗa abubuwa daga Italiya, inda mahukuntan Najeriya ba za su iya cim mata ba. Ƙungiyar Ipob haramtaciyya ce a Najeriya kuma ta 'yan ta'adda, kodayake ƙungiyar ta dage cewa gwagwarmayarta ta zaman lafiya ce.

Binciken BBC ya gano wasu manyan magoya bayan ƙungiyar da ke mata aiki a wajen Najeriya, suna yaɗa kalaman ƙarya ƙarara da kuma tunzura tashin hankali a shafukan zumunta a faɗin nahiyar Turai da Asiya da kuma wasu yankunan Afirka.

Ɗan jaridar Najeriya mai biciken ƙwaƙwaf, Nicholas Ibekwe, ya siffanta ayyukan ƙungiyar a intanet da "gonar girbe tsangwama".

"Shafukan zumunta ne babbar hanyar da Ipob ta fi yin nasara wajen yaɗa dukkan abubuwan da ta sa a gaba," a cewarsa.

Composite image of Nneka Igwenagu (left) and Efe Uwanogho (right)
Bayanan hoto, Nneka Igwenagu (hagu) da Efe Uwanogho (dama) na yaɗa abubuwansu daga wajen Najeriya

Wasu daga cikin magoya bayan ƙungiyar na da mabiya kusan 100,0000 a shafukan zumunta.

Ba mu sani ba ko wani daga cikin mabiyan Ms Uwanogho ya taɓa bin umarninta wajen kai wa mahukunta hari a kudu maso gabashin Najeriya.

Ms Uwanogho ba ta amsa ba lokacin da muka nemi martaninta a lokacin haɗa wannan rahoto.

Amma tashin hankalin na ci gaba da faruwa ƙarara, yayin da tuni aka kashe gwamman jami'an gwamnati a wannan shekarar a hare-haren da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana da "mai ta da hankali sosai".

Nneka Igwenagu wata "gwarzuwar kafar yaɗa labarai" ce da ke fafutikar kafa Biafra, amma tana zaune a Birtaniya.

Yayin wani shiri da take yaɗawa kai-tsaye daga birnin Landan a 2021, tana neman jan hankalin matasa daga kudu maso gabashin Najeriya da suka dinga ƙin bin umarnin Ipob na durƙusar da harkokin kasuwanci da makarantu don nuna goyon baya ga jagoran ƙungiyar Nnamdi Kanu da ke tsare.

Nnamdi Kanu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Jagoran Ipob Nnamdi Kanu ya sha yabon ayyukan "gwarazan kafofin yaɗa labaran"

Yanzu haka hukumomi a Najeriya na tsare da Nnamdi Kanu da ke fuskantar tuhumar ayyukan ta'addanci, waɗanda ya musanta.

Da take magana cikin harshen Igbo, harshen da aka fi yi a kudu maso gabas, Ms Igwenagu na kiran su da "kaji" tana mai cewa:

"Bai kamata ku rayu ba dukkanku...Kazar da ke cinye ƙwanta, ba kwa ganin bai kamata ta rayu ba?"

'Yan makonni bayan shirin da ta yaɗa aka kashe shugaban ƙungiyar da take magana a kan sa. Babu wanda aka kama balle tuhuma da kisna nasa.

Flyer showing news of the death of Ogidi youth leader, with picture of him wearing a blue t shirt and text saying "exit of a hero"
Bayanan hoto, An yi ta alhinin rasuwar shugaban ƙungiyar matasan Ogidi bayan kashe shi

Mun nemi martanin Ms Igwenagu game da wannan binciken, amma ba mu samu komai ba.

Ɗaya daga cikin hanyoyin da 'yan gwagwarmayar ke amfani da su don guje wa mahukunta ita ce yin amfani da harsunansu na al'ada waɗanda ba kasafai ake iya tantance abubuwan da suke faɗa ba.

Dabarar ta girmama cikin wani bidiyo da Okenna Okechukwu, wanda aka sani kuma da Biafran Child (Ɗan Biafra), yake magana da harshen Igbo inda yake neman a fille kan wani mai sukarsu, kafin daga baya ya koma magana da Ingilishi yana cewa:

"Dalilin da ya sa nake amfani da harshena shi ne ba na so su dakatar da ni. Ba na son su dakatar da ni daga wannan dandalin."

David Ajikobi, editan Najeriya na shafin bin diddigi mai suna Africa Check, ya ce ƙarancin lura da abubuwan da ake faɗa da harsunan cikin gida babbar matsala ce, kuma ba wai a Najeriya kaɗai matsalar ta tsaya ba.

"Mun lura da hakan a Indiya, da Ethiophia, inda ake fama da rikice-rikice. Mutane na amfani da harsunansu na uwa ne saboda sun san idan suka yi amfani da Ingilishi za a gane su kuma a toshe shafukansu daga dandalin."

Duk da abubwuan tashin hankali da muka gano, dandalin zumunta ba su fiya sa ido kan maganganun ba.

Bisa ƙa'idojin da Facebook ya shimfiɗa wa kan sa, mun ba da rahton cewa shirye-shiryen da Efe Uwanogho da Nneka Igwenagu ke yaɗawa na ƙunshe da tashin hankali. Da farko sai aka ba mu amsar cewa Facebook ba zai goge bidiyoyin ba.

Sai daga baya da BBC ta yi magana da Facebook kai-tsaye sannan aka cire su. Amma har zuwa lokaci haɗa wannan rahoton akwai bidiyo masu tunzura tashin hankali a shafukan jibge.

Ingiza rikici

Kamfanin Meta da ya mallaki Facebook ya faɗa mana cikin wata snaarwa cewa kiran tayar da fitina haramun ne a dandalin. Ya ce akwai mutum 15,000 da ke bincika saƙonni a harsuna fiye da 70 - ciki har da Igbo.

Binciken namu kuma ya gano yadda mambobin Ipob ke yaɗa labaran ƙarya don ingiza fitina tsakanin ƙabilu a Najeriya.

'Yan gwagwarmayar na ingiza 'yan ƙabilar Igbo, waɗanda akasarinsu Kiristoci ne kuma mazauna kudanci, a ƙabilar Fulani, waɗanda akasarinsu Musulmai ne kuma mazauna arewaci.

A wani bidiyon na Facebook, Ms Igwenagu ta gargaɗi Igbo cewa 'yan Arewa da Fulanin da suka shiga "ƙasar Biafra" na da wata manufa..."ta shafewa da kashewa da share mu baki ɗaya".

Biyan kuɗi saboda wallafa saƙo

Binciken namu ya gano cewa ana ba wa ire-iren waɗan nan 'yan gwagwarmayar lada sakamakon abubuwan da suke wallafawa a shafukan zumunta.

Mun ga wasu bidiyo da su kansu 'yan gwagwarmayar ke amsa cewa na biya su, ko dai daga Ipob ko kuma magoya bayansu, saboda ayyukan da suke gudanarwa, kuma mun ga bidiyon da ake yaɗa bayanan asusun ƙungiyar da ke neman a taimaka mata da kuɗi.

"Da alama Facebook barci yake kawai. Ba sa tunanin cewa waɗan nan kalaman da suke yi, waɗannan saƙonnin da ke kan Facebook na da tasiri," in ji ɗan jarida Nicholas Ibekwe.

Audu M Linus (retired) and Private (Pte)Gloria Matthew
Bayanan hoto, An kai wa Audu Linus da Gloria Matthew hari lokacin da suke kan hanyar zuwa ɗaurin aurensu

A ranar 30 ga watan Afrilu, an kai wa sojojin Najeriya Audu Linus da Gloria Matthew hari kan hanyarsu ta zuwa bikin gargajiya na ɗurin aurensu a Jihar Imo. An sace su, aka azabtar da su sannan aka kashe su.

Daga baya wani bidiy ya ɓulla na yadda aka kashe ma'auratan, wanda Shugaba Buhari ya zargi Ipob da aikatawa.

Sai kuma wasu maganganu suka fara ɓulla a intanet da magoya bayan Ipob ke cewa bidiyon ba na gaskiya ba ne kuma shirya kisan sojojin aka yi.

Sai dai BBC ta tabbatar da kisan sojojin biyu daga danginsu.

Ipob ta musanta hannu a kisan.

Mun tuntuɓi shugabannin Ipob game da abin da muka gano. Sun amsa amma ba su ba da wani bayani ba.

Mun tuntuɓi dukkan "gwarazan kafofin yaɗa labaran" da muka ambata a wannan labarin don su yi martani, amma ba su ce komai ba.