Sarki Abdallah na Jordan ya yi wa kaninsa daurin talala

Sarki Abdallah

Asalin hoton, Getty Images

Sarki Abdallah na biyu na Jordan ya ce ƙaninsa Yarima Hamzah, wanda aka zargin shi da yunƙurin juyin mulki a shekarar da ta wuce, yana cikin wani yanayi na ruɗani, wanda hakan ya sa za a ci gaba da riƙe shi ƙarƙashin ɗaurin talala a gida.

Ana ɗaukar sabuwar wasiƙa da ke ƙunshe da wannan bayani, wadda Sarkin ya wallafa a matsayin wani abu na kasada, saboda ya bayyana wa duniya saɓanin da ke tsakanin iyalan gidan sarautar.

Lokacin da hukumomin Jordan suka bayar da sanarwar cewa sun bankaɗo wani yunƙurin juyin mulki, shekara daya da ta wuce.

Lamarin ya tayar da zaune tsaye a ƙasar da ake ɗauka a matsayin, ginshikin zaman lafiya a wannan yanki na Gabas ta Tsakiya.

Sai kuma ga wannan wasika mai ɗauke da kalamai masu tsauri da ta fito daga Sarki Abdallah, wadda a cikinta yake cewa, ƙanin nasa wanda suke uba ɗaya, uwa kowa da tasa Yarima Hamza, ya riga ya saryar da duk wata dama da dawowa kan turba madaidaiciya.

Sarkin ya bayar da misalan abin da ya kira ɗabi'u da burukan da ba su dace ba.

Duk da cewa an daure wasu tsoffin jami'an masarautar biyu bisa kama su da laifin haɗa baki don hambarar da Sarkin na Jordan, shi kuwa Yariman ba a gurfanar na shi gaban shari'a ba ma.

A farkon wannan shekara Yariman ya bayar da haƙuri tare da neman gafara a hukumance daga dan uwan nasa, wato Sarkin.

To amma kuma, (an gudu ba a tsira) ya harzuƙa masarautar saboda ya sanya wani sako a shafin Twitter cewa zai ajiye matsayinsa na sarauta saboda ƙin yarda ko amincewa da wasu manufofi na kasar, wanda hakan a fakaice yana suka ne ga Sarkin