NFHS-5: Har yanzu Indiyawa sun fi son haihuwar ɗa namiji kan mace - Bincike

Sabon binciken da gwamnatin Indiya ta gudanar ya nuna an samu ci gaba kan jinsin da ake son haifa tsakanin mace da namiji, sai dai yawancin wadanda aka zanta da su sun nuna sha'awar haifar ɗa namiji kan mace, kamar yadda wakiliyar BBC a Delhi Shadab Nazmi ta rubuta.

Kusan kashi 80 da suka shiga shirin jin ra'ayin jama'a na gwamnati sun ce suna son haifar ɗa namiji ko sau daya cikin 'ya'yansu, kuma kididdigar NFHS-5 ta nuna, wannan shi ne bincike na hakika da gwamnatin kasar ta yi.

Wannan mataki na nuna fifiko kan son haihuwar ɗa namiji fiye da 'ya mace shi ake kira ''nuna amfanin da namiji''.

An samu hakan ne tun zamanin iyaye da kakanni, inda sukai amanna shi ne magajin gida da zai kula da iyayensa idan sun tsufa, yayin da 'ya'ya mata ake aurar da su ga kuma sanya biyan sadakin aure mai nauyi.

Masu fafutuka sun ce wannan dalili ne ya sanya ake nuna fifikon haihuwa tsakanin 'ya'ya mata da maza, kuma gagarumar matsala ce mai cike da abin kunya.

Sama da shekara 100 da suka wuce, kidayar da aka yi ta nuna maza sun fi mata yawa a kasar.

Kidiyar shekarar 2011, ta nuna ana samun mata 940 su kuma maza 1,000, sannan adadin haifar 'ya'ya maza da akai nazari daga haihuwa zuwa shekara shida, shi ma ana samun 'yan mata 918, maza 1,000.

Wannan ya janyo ana sukai Indiya da kiran ta ''kasar da matan ta suka bata.''

Binciken NFHS-5 da aka gudanar tsakanin 2019 zuwa 2021, sun nuna a a karon farko cikin shekaru da dama an samu ci gaba ta fannin son haihuwar 'ya'ya mata, hakan ya sanya suka rinjayi maza a Indiyawa.

Sai dai kididdigar ta nuna har yanzu kaunar 'ya'ya maza na nan dankare a zukatan wasu.

Sama da kashi 15-16 na maza da mata kashi 14 sun shaidawa binciken sun fi son 'ya'ya mata fiye da maza.

An samu dai ci gaba idan akwa kwatanta da shekarun baya, iyaye mata na ci gaba da haihuwa har sai sun samu karin 'ya'ya maza.

Indrani Devi, mai shekara 32, tana da 'ya'ya mata uku, kuma aikatau ta ke yi a wani gida da ke Delhi, ta shaidawa BBC cewa ta ce ta so haifar 'ya'ya maza biyu da mace guda.

"Amma Allah ya na da kyakkyawan tsari kan bayinsa, sai ya bani 'ya'ya mata uku," in ji ta.

A yanzu ta karbi kaddararta, ta yanke shawarar ba za ta kara haihuwa ba. "Miji na direban bus ne, ba za mu iya kara haihuwa ba," in ji Indrani.

Kamar dai Indrani Devi, kusan kashi 65 na matan da ke tsakanin shekaru 15-49 wadanda suka haifi akalla 'ya'ya mata biyu ba namiji ko daya, sun shaidawa NFHS-5 ba sa son kara haihuwa.

Adadin ya karu idan aka kwatanta da shekaru shida .

Babu tababa sha'awar haifar 'ya'ya maza ta karu da kashi 5.17, daga kashi 4.96 tsakanin shekarar 2005-2016 in ji NFHS-4.

Sauyin duk da ba mai yawa ba ne, an samu ma'aurata wasu na son kara haifar 'ya'ya mata wasu kuma maza.

Kwararru sun yi amanna wannan na da alaka da rashin haihuwa da Indiya ba ta fuskanta, da kuma adadin 'ya'yan da za su haifa.

Karuwar 'ya'ya matan da ke zuwa makaranta, da samun maganin tsarin iyali ya sanya an samu raguwar haihuwa, dan haka matukar adadin ya yi kasa da kashi 2.1, to an samu raguwar haihuwa baki daya.

Ga kasa mai al'umma biliyan 1.3, ba zai zama abin damuwa, sai da kwararru na cewa, idan ana son samun ingantacciyar al'umma ya kamata Indiya ta duba batun haihuwa a kasar.

Karin labaran da za ku so