Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilan da suka saka mata zaben jam’iyar BJP ta Firaministan Indiya Narendra Modi
- Marubuci, Daga Geeta Pandey
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
Mace ita ce kashin-bayan samun nasarar ko wane namiji, kamar yadda aka saba fada.
Amma miliyoyin mata su ne kashin-bayan samun nasarorin jam'iyar Bharatiya Janata (BJP) ta Firaministan Indiya Narendra Modi a muhimman zabukan da aka gudanar a baya-bayan nan.
Kamar yadda sabbin bincike biyu suka nuna, mata su suka fi zaben jam'iyar BJP fiye da maza a zabukan watan Fabrairu wa zuwa Maris da aka gudanar a hudu daga cikin jihohin kasar da ta samu galaba, da suka hada da Uttar Pradesh mai yawan al'ummar da ta kai kasar Brazil.
Tun a shekarar 1962 - lokacin da Hukumar Zabe ta fara sanar da yawan jinsin mutanen da suka fita kada kuri'a a babban zaben kasar- a ko da yaushe mata ne suka fi zaben jam'iyar Congress a matakin kasa.
Amma tun a shearar 2019, a karon farko, jam'iyar BJP ta zama jam'iya mai wayan adadin kuri'un mata.
Yanzu BJP - kamar sauran jam'iyun kasar Indiya - da wahala ta kasance kunshe da masu goyon bayan mata kana duniya na kallon mata da dama a matsayin marasa tagomashi.
Shugabannin jam'iyyu na yawan fita a kafafen yada labarai don furta kalamai marasa dadi game da mata kana wasu daga cikin gwamnatocin jihohinta sun sha karade manyan labaran duniya kan rashin yin kokari wajen shawo kan aukuwar matsaloli na fyade.
Har ila yau, mata ne suka jagoranci zanga-zangar nan mafi daukar tsawon lokaci da karfi a kan dokar zama dan kasa mai cike da ce-ce-ku-ce.
Amma duk da haka, bayanai sun nuna cewa mata sun fi zabar jam'iyar BJP a yanzu.
Shin ya aka yi BJP ta zama jam'iyyar da matan Indiya suka fi zaba?
"Saboda Mista Modi," in ji Sanjay Kumar na Cibiyar Bincike kan Cigaban Al'ummomi (CSDS), mai mazauni a birnin Delhi.
"Ba wai cikin lokaci kankane ne jam'iyar ya samu karbuwa a wurin matan ba. Tabbas Mista Modi shi ne salsala - babbar salsala," ya kara bayyanawa.
Nalin Mehta, wani masanin harkokin kimiyyar siyasa ne kuma maurbuci wanda ya gudanar da cikakken bincike a sabon littafinsa The New BJP, ya ce a shekarar 1980 ne jam'iyar ta fara samun kai wa ga mata, lokacin da ta kafa bangaren mata.
"BJP na da wasu muhimmai da kasaitattun shugabanni mata kana ta yi gagarumin alkawura kan batuwan da suka shafi harkokin mata na musamman, amma a tsawon shekaru goma mata da yawa ba su zabi BJP ba. Galibi ana kallon jam'iyar a matsayin wacce maza suka fi mamayewa kuma muhimmanci kadan suke bai wa matan.''
Babban sauyin da aka samu a shekarar 2019 a matakin kasa baki daya, ya ce ya samo asali ne daga shekara ta 2007 lokacin da Mista Modi ya nemi dawowa a zabe shi a matsayin babban minista a yammacin jihar Gujarat.
A gangamin yakin neman zabe, ya sha yin magana a kan fadin kirjinsa na inci 56 - irin alfaharin da karfafan maza suka saba yi a fadin jihohi masu magana da harshen Hindu.
"A koda yaushe yakan yi kuri da wannan, a kan samu wani irin ajiyar zuciya mai karfi daga cikin taron jama'ar, musamman a bangaren da mata ke zaune. Kana a ko da yaushe a kan zamu mata fiye da maza a wurin gangamin yakin neman zabensa. Yakan rika yin kira a gare su yana cewa, 'Ni dan uwanku ne, ni danku ne, ku zabe ni kuma zan duba tare da kare muradun ku," Mista Mehta ya ce.
Amma kasancewa cikakken namiji na da iyaka, don haka ya hada da surarasa ta " cikakken namijin da ke gyara al'amura '' tare da tsarin mayar da hankali kan al'amuran mata - hakan ya taimaka masa wajen samun tagomashi da galabar cin jihar Gujarat a shekarar 2007 kana a shekarar 2012.
A lokacin da ya samu galabar lashe zaben shekarar 2014, ya gyara inganta tsarinsa.
A jawabinsa na farko ga kasa a matsayinsa na firaminista a watan Agustar shekarar, ya yi kira ga yaki da zubar da ciki, da yin Allah wadai da ayyukan fyade tare da yin kira ga iyaye da su rika tarbiyyantar da 'yayansu maza.
A matsayinsa na firaminista, Mista Mehta ya ce, Mista Modi ya zama "salsalar kawo sauyi" wanda ke yawan magana a kan abubuwan da suka shafi mata a tarukan jama'a da gagamin yakin neman zabe - a jawabansa daga shekarar 2014 zuwa 2019, sau da dama mata kan fita a cikin manyan batutuwa hudu.
Amma baya ga amfani da kwarjin da yake da shi, jam'iyar BJP ta kuma bai wa mata damar wakilci a cikin harkokin siyasa.
A shekarar 2019, ta kara yawan mata 'yan takara fiye da sauran jam'iyu kana ta bai wa karin mata mukaman ministoci fiye da gwamnatocin baya.
Ta kuma kara wa tsarin jam'iyar karfi, tare da bai wa mata dama da fadada harkokinta cikin al'umma don samun karin mata daga yankunan karkara da kuma al'ummomi matalauta.
A wani muhimmin bangare, magoya bayan BJP mata daga yankunan karkara ne da kuma gidajen iyalai masu karamin karfi, Mista Mehta ya bayyana, tsarin kyautata jin dadin jama'a na jam'iyar ya kuma saka su a ciki.
A kasar da ta kasance wacce maza suka mamaye komai, inda mata ke da 'yancin kadan na mallakar kadarori, da kashi 68 bisa dari na gidaje sama da miliyan daya da dubu dari bakwai na gidajen matalauta da 1.7 ga matalautan da aka amincewa a tsakanin shekarar 2014 da 2019 wadanda aka yi wa rajista da suna mata kadai ko kuma hade da maza.
Gwamnati ta kuma gina miliyotin wuraren ba-haya wa iyalai, tare da taimaka wa miliyoyin mata wajen bude asusun ajiya a bankuna don su rika karnar kudin fansho, da sauran tallafi kai tsaye.
"Ana yawan jin Mista Modi na maganar cewa samar da hanyoyin kyutata jin dadi da zai taimaka wa mata tun daga haihuwarsu ya zuwa mutuwa. Tsare-tsaren ba su zama kammalalu ba, amma ko shakka babu an samu sauyi,'' in ji Mista Mehta.
"Sakamakon haka, mata masu kada kur'a da dama har yanzu suna kallon jam'iyar a matsayin mafi inganci, wacce ta fi sauran.''
Amma wannan goyon bayan da ya shafi jinsi na jam'iyar lokacin kan iya kasancewa gajartacce, in ji Maya Mirchandani, wata babbar 'yar jarida kuma shugabae sashe koyon aikin jarida na Jami'ar Ashoka.
"Mista Modi na da matukar kwarjini kuma yana samun tausayawa daga magoya bayansa da suke masa kallon mai sauki kai. A gare su yana da kyakkyawan fasali saboda ya dace, ba shi da girman kai, yana tafiyar da rayuwar da za a iya koyi da ita. Amma kuma ya riga ya kai shejaru 71 kuma wasu daga cikin irin wadannan abubuwa za su gushe tare da shekarun."
Abin a jira a gani ne kuma, ta ce, ko abubuwan na shi za kawar da matsalolin da Indiya ke fuskanta a halin yanzu.
"A daidai lokacin da rashin aikin yi ke karuwa, hauhawar farashin kayayyaki ke karuwa, kana ga farashin mai da ke kara hauhawa, kana abubuwan da ke hada kawunan jam'iyarsa su ne siyasar addinin. Amma idan tashe-tashen hankula suka kara ta'azzara kana tattalin arziki bai farfado ba, matan da ke kula da al'amuran gida ne za su juya masa baya," in ji ta.
"Wannan mataki ba zo ba tukuna, amma zai iya faruwa.''