Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iyaye sun yi ƙarar ɗansu a Indiya don biyansu ɗawaniyar da suka yi masa don bai haihu ba
- Marubuci, Daga Patrick Jackson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 2
Wasu iyaye a jihar Uttarakhand da ke arewacin indiya sun kai ƙarar ɗansu ɗaya da suka mallaka kotu shi da matarsa don gaza samar musu da jika bayan shekara shida da yin aure.
Sanjeev da Sadhana Prasad masu shekara 61 da 57, sun ce sun kashe dukkan kuɗaɗen da suka rayu suna tarawa don ɗaukar ɗawainiyar ɗan nasu da kuma yi masa aure mai gagarumin biki na gani na faɗa.
Suna buƙatar ɗan ya biya su diyyar kusan dala 650,000 idan har bai haihu ba a cikin wannan shekarar.
Ɗan nasu da matarsa har yanzu ba su ce komai ba.
Iyayen sun ce dalilin shigar da ƙarar irin wacce ba a saba gani ba shi ne don "lamarin na damunsu matuƙa."
Mista Prasad ya ce ya kashe dukkan abin da ya mallaka a kan ɗan nasa, inda ya tura shi Amurka a shekarar 2006 don ya yi karatun neman ƙwarewa a tuƙin jirgin sama kan kuɗi dala 65,000.
Ya koma Indiya a shekarar 2007, amma sai ya rasa aikinsa sannan iyayensa sun shafe fiye da shekara biyu suna taimaka masa, kamar yadda wata jarida ta Times of India ta ruwaito.
A ƙarshe dai ɗan nasu Shrey Sagar mai shekara 35 ya samu aiki a matsayin matuƙin jirgin sama.
Iyayensa sun ce sun yi masa aure ne da matarsa Shubhangi Sinha mai shekara 31 a yanzu, tun a 2016, da fatan cewa za su samu "jikan da za su dinga wasa da shi" idan suka yi ritaya daga aiki.
Iyayen sun ce sun yi gagarumin bikinsa a wani katafaren otel, da saya masa mota ta kece-raini ta dala 80,000 tare da kai shi da matar yawon shaƙatawa na amarci a ƙasar waje.
"Shekara shida kenan da auren ɗana amma har yanzu ba su shirya haihuwa ba, in ji Mista Prasad.
"A ƙalla idan muna da jikan da za mu dinga wasa da shi, damuwarmu za ta ragu sosai."
Lauyan iyayen, AK Srivastava, ya shaida wa jaridar told The National cewa iyayen sun nemi ɗan nasu ya biya su diyyar kudin ne saboda "tsananin damuwar da suke ciki".
"Burin duk iyaye shi ne su zama kakanni. Sun jira tsawon shekaru don su zama kakanni."
Ana sa ran za a saurari ƙarar ranar 17 ga watan Mayun 2020 a Haridwar inda aka shigar da ƙorafin.