Rikicin Ukraine: Shin Afrika za ta iya cike giɓin gas ɗin da Rasha ke samar wa Turai?

    • Marubuci, Daga Ijeoma Ndukwe
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Business

Ƙasashen Afrika na daga cikin waɗanda ke son ƙara adadin gas ɗin da suke fitarwa zuwa Tarayyar Turai, bayan da Tarayyar Turan ta ce za ta rage dogaron da take yi kan kayayyakin Rasha sakamakon yakin da ta kaddamar a Ukraine.

Dakatarwar da Rasha ta yi na kai kaya Poland da Bulgaria kan ƙin daina biya da kuɗin roubles wato kuɗin Rasha. Rasha ta fi kowa yawan gas a duniya kuma ta fi kowa fitar da shi inda ita ce take fitar da kashi 40 cikin 100.

Tarayyar Turai na son rage adadin gas din da ake shigar mata da shi da kashi biyu bisa uku zuwa ƙarshen shekara inda take sa ran zama mai samar da makamashinta na ƙashin kai zuwa 2030.

Sai dai masanin harkokin tattalin arzikin makamashi Carole Nakhle ya bayyana cewa idan manyan masu fitar da gas na ƙasashen Afrika da suka haɗa da Algeria da Masar da Najeriya - inda adadin ya kai rabin abin da Rasha ke kai wa Turai.

"Labarin mai daɗi shi ne za a fi mayar da hankali ga ƙasashe waɗanda ke da tulin albarkatu domin maye gurbin gas ɗin Rasha da Afrika a yanayi mai kyau. Za mu ga ƙarin zuba jari," in ji shi.

Aljeriya da alama a shirye take domin samun wannan garaɓasa daga wannan matakin na Tarayyar Turai. Ƙasar da ke arewacin Afrika ita ce ta fi kowace ƙasar yankin samar da iskar gas kuma tana samun tagomashi sakamakon irin yadda take da hanyar shiga da gas ɗin Turai.

A watan da ya gabata, Firai minista Mario Draghi ya saka hannu kan sabon yarjejeniya ta samar da gas da Aljeriya domin ƙarin samun shigar da gas da kashi 40 cikin 100.

Wannan ce yarjejeniya ta farko mafi girma domin neman wata sabuwar hanya ta samun gas bayan kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine.

Sai dai akwai damuwa matuƙa kan batun Aljeriya ta ƙara yawan gas ɗin da take samarwa sakamakon adadi mai yawa da ake amfani da shi a cikin gida da ƙarancin zuba jari a ɓangaren da kuma rashin tabbaci na siyasa, in ji Uwa Osadieye wanda shi ne babban mataimakin shugaban bincike a FBNQuest Merchant Bank.

Ya bayyana cewa adadin gas ɗin da ake fitarwa daga Aljeriya zuwa Turai ya ragu matuƙa sakamakon rikicin da take yi da Morocco, wanda hakan ya yi sanadin kulle wani bututu mai muhimmanci zuwa Sifaniya.

"Wannan yarjejeniyar za ta bayar da dama domin samun tagomashi a fitar da gas ɗin ta bututu kuma da alama za a iya samun ƙarin gas ɗin zuwa cubic meter biliyan tara a duk shekara a 2023 da 2024. Sai dai babu masaniya kan yadda Aljeriya za ta yi sauri wurin ƙarin yawan gas din da take samarwa."

Ministocin Italiya sun yi takakkiya har zuwa Angola da Congo-Brazzaville inda suka amince kan sabbin yarjejeniyoyi kuma Italy na hararar ayyuka a Mozambique a yunƙurinta na kawo ƙarshen dogara kan Rasha zuwa tsakiyar 2023.

Sai dai kamfanin da ke samar da gas na LNG wanda na Najeriya ne na ta samun buƙatu daga ƙasashen Turai na tura gas tun bayan soma rikicin Ukraine.

A halin yanzu, Sifaniya da Portugal da Faransa na daga cikin manyan kasuwanni ga kayayyakin kamfanin LNG kuma kamfanin na hulɗa ne kawai da masu saya wurinsa, kamar yadda wani da ba ya so a bayyana sunansa ya shaida wa BBC.

"Akwai damar ƙara yawan gas ɗin da ake samarwa. A yau, kamfanin LNG na Najeriya na samar da kashi 72 ne kacal na abin da zai iya samarwa, wanda hakan na nufin akwai sauran kashi 28 cikin 100 rara wanda za a iya samarwa wanda a halin yanzu wannan ne babban ƙalubale a halin yanzu," in ji shi.

Ya bayyana irin matsalolin da ke kawo wa kamfanin cikas wurin ƙarin adadin gas din da ake samarwa, ciki har da raguwar albarkatu daga rijiyoyin mai da kuma raguwar samar da kudi a ɓangaren samar da mai.

"Akwai abubuwan da za a iya kawo gyaransu a ƙanƙanin lokaci - tsakanin wata shida zuwa 18."

Kamar yadda Andy Odeh ya bayyana, Shugaban harkokin waje da ci gaba mai ɗorewa na kamfanin LNG ya bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa a halin yanzu da masu samar da iskar gas domin kawo ƙarshen waɗannan matsaloli kuma yana sa ran za a samu ƙaruwa a adadin da LNG ke samarwa "daga ƙarshen shekarar nan zuwa sama," in ji shi.

Wani sabon aikin gas na LNG Nigeria mai suna Train 7 zai haɓaka samar da gas da kashi 35 cikin 100 daga tan miliyan 22 da ake samarwa a duk shekara daga 2025.

Sai dai yarjejeniyoyi da masu saya akasari waɗanda ke a Turai tuni aka fara su. LNG na Najeriya na gudanar da bincike kan wani sabon aiki mai suna Train 8 domin haɓaka samar da iskar gas.

Ƙasar da ke yammacin Afrika na taka muhimmiyar rawa a aikin bututu na Afrika mai tsawon kilomita 4,400 da zai tashi daga Najeriya ya ratsa zuwa Nijar da Aljeriya.

Bututun zai haɗe da wanda ke da akwai a Aljeriya wanda ke da alaƙa da ƙasashen Afrika zuwa Turai.

An soma tattaunawa kan wannan aikin tun a shekarun 1970 sai dai barazana ta tsaro da kuma barazanar muhalli da ƙarancin samar da kuɗi su ne suka kawo cikas.

A wata tattaunawa da aka yi a watan Fabrairu, jami'an yankuna sun yi alƙwarin za a ci gaba da aikin.