Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Ukraine da Rasha: Farashin man fetur ya tashi saboda fargabar yaƙi
Farashin iskar gas da na ɗanyen man fetur na hauhawa sakamakon fargabar da rikicin Rasha da Ukraine ke haifarwa game da jigilar makamashin a faɗin duniya.
Farashin ɗanyen mai samfurin Brent, wanda aka fi amfani da shi, ya yi tashin da bai taɓa yi ba cikin shekara bakwai zuwa dala 99.38 kan kowace ganga ɗaya a ranar Talata.
Kamfanin makamashi na Birtaniya RAC ya yi gargaɗin cewa lamarin zai sake harzuƙa farashin mai a Birtaniya bayan ya kai fan 149.12 kan kowace lita ranar Lahadi.
Rasha ta umarci dakarunta su shiga yankuna biyu na Ukraine waɗanda suka ayyana kansu a matsayin masu 'yancin kai bayan ta amince da iƙirarin nasu.
Kasuwar hannun jari a yankin Asiya ta tashi babu riba sannan ta Amurka na shirin faɗuwa.
Gwamnatocin ƙasashen Turai sun yi barazana ko kuma sun saka wa Rasha takunkumai, wadda ita ce ta biyu a yawan fitar da man fetur kasuwar duniya bayan Saudiyya. Kazalaika, Rasha ce mafi arzikin iskar gas a duniya.
A ranar Talata, Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ɗauki matakin dakatar da gina bututun iskar gas tsakaninsa da Rasha mai suna Nord Stream 2 wanda aka tsara zai samar da gas ɗin kai-tsaye daga Rasha zuwa Jamus.
Tuni farashin gas ɗin ya tashi sakamakon haka.
'Babbar mai haja'
Saka wa Rasha takunkumin da zai hana ta fitar da fetur da gas masu yawa zai yi "babban tasiri" a kan farashinsu a faɗin duniya, a cewar Sue Trinh na kamfanin Manulife Investment Management.
Farashin man wanda ya dinga tashi a 'yan watannin nan, ya tashi da kashi 10 cikin 100 tun daga farkon watan Fabarairu.
Wata darakta a kamfanin Fidelity International, Maike Currie, ta ce farashin mai zai iya kaiwa dala 100 kan kowace ganga ɗaya saboda rikicin Ukraine da lokacin hunturu a Amurka da kuma ƙarancin jari a harkar gas da fetur a faɗin duniya.
"Rasha ce ke samar da ɗaya cikin duk ganga 10 ta man fetur a faɗin duniya, saboda ita ce babbar mai haja idan ana maganar farashin fetur, kuma tabbas hakan zai baƙanta wa masu amfani da shi," in ji ta.
Akasarin man da Birtaniya ke saya ba daga Rasha yake fitowa ba, amma idan ƙasar ta rage fitar da shi zai shafi yawansa a faɗin duniya.
"Matakin Rasha na afka wa Ukraine tuni ya fara haddasa hauhawar farashi kuma tabbas zai sa farashin ya kai fan 1.50 kan kowace lita a Birtaniya," a cewar mai magana da yawun kamfanin RAC Simon Williams.