Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka da Rasha sun yi kaca-kaca a wajen taron MDD kan Ukraine
An yi faɗa kaca-kaca tsakanin jakadun Amurka da Rasha a wajen taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, bayan da Amurka ta kira wani taro don tattanawa kan yadda Rasha ke girke dakaru a kan iyakarta da Ukraine.
Jakadiyar Amurka Linda Thomas-Greenfield ta ce aikin girke dakarun na Rasha shi ne irinsa mafi girma da aka taɓa gani a yankin Turai cikin gwamman shekaru.
Takwaranta na Rasha ya zargi Amurka da haifar da ruɗani da kuma yin shisshigi a al'amuran Rasha.
Amurka da Birtaniya sun yi alkawarin ƙara ƙaƙaba wa Rasha takunkumai idan har Rasha ta kutsa Ukraine.
Sakatariyar Harkokin Wajen Birtaniya Liz Truss ta ce ana tsara dokokin da za su mayar da hankali kan mutane da kuma harkokin kasuwanci da dama a Rasha fiye da waɗanda ake da su a yanzu.
Wani jami'in Amurka ya ce takunkuman da Fadar Washington za ta sanya na nufin za a cire mutanen da ke da kusanci da gwamnatin Rasha daga tsarin hada-hadar kasuwanci na duniya.
A ƙiyasi Rasha ta girke dakaru 100,000 da tankokin yaƙi da igwa-igwa da makamai masu linzami a kusa da kan iyakar Ukraine.
Ana ci gaba da ƙoƙarin bin tafarkin diflomasiyya, inda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken zai gana da Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov a ranar Talata.
Amurka ta ce ta samu rubutacciar amsa daga Rasha kan wata buƙata da Amurkan ta aika mata ta neman yayyafa wa wutar rikicin ruwa a Ukraine.
Amma sa'o'i bayan hakan sai mataimakin ministan harkokin wajen Rasha ya ce hakan ba gaskiya ba ne, kuma wata majiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Ria cewa, ana nan ana rubuta amsar buƙatar.
Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ya ce, a shirye Amurka take ta tattauna kuma za ta ci gaba da tuntuɓar ƙawayenta na ƙut-da-ƙut da abokan hulɗarta da suka haɗa da Ukraine.
A hannu guda kuma, wasu shugabannin ƙasashen Turai sun kama hanyar zuwa Ukraine a ranar talata don tattaunawa.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai je Kiev bayan alkawarin da ya yi cewa zai yi aiki da shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky don gano mafita ta diflomasiyya kan rikicin Rashan da kuma gudun zubar da jini.
Firaministan Poland Mateusz Morawiecki da kuma Firaministan Holland Mark Rutte su ma sun kama hanyar zuwa Ukraine.
A wajen taron Kwamitin Tsaro na MDD na ranar Litinin, Jakadan Rasha Vasily Nebenzya ya ce babu wata hujja cewa Rasha na da shirin amfani da ƙarfin soji kan Ukraine, kuma MDD ta kasa tabbatar da batun girke dakarun da take yi.
Ya ce Rasha tana yawan girke dakaru a yankinta kuma wannan ba abin da ya shafi Amurka ba ne.
Rasha ta yi ƙoƙarin hana zaman tattanawar kwamitin tsaron a bainar jama'a, amma sai aka rinjaye ta da ƙuri'a 10 inda ita kuma ta tsira da ƙuri'a biyu.
Mr Nebenzya ya ce gwamnatin Biden tana tunzura rikici da tsananta abubuwa.
"Wannan shiga hanci da ƙudundune ne da ake yi wa al'amuran cikin gidanmu, sannan ƙoƙari ne na ɓata mu a idon ƙasashen duniya da kawar da hankalinsu kan ainihin abin da ke faruwa a yankin da kuma dalilan ruɗanin da ake ciki a duniya yanzu," a cewarsa.
Ms Thomas-Greenfield ta ce Amurka na ci gaba da yin amannar cewa za a samu mafita ta diflomasiyya amma ta yi gargaɗi cewa Amurka za ta ɗauki matakin da ya dace idan har ta kutsa Ukraine, matakan da ba za su yi "daɗi ba."
Ta ce: "Wannan ne gagarumin... girke dakaru da aka taɓa yi a Turai cikin gwamman shekaru.
"Kuma a yanzu da muke magana, Rasha na aika ƙarin dakaru yankin."
Fadar Moscow na shirin ƙara yawan dakarunta da ke girke a maƙwabciyarta Belarus, a kan iyakar arewacin Ukraine, zuwa 30,000, in ji ta.
A ranar Litinin da yamma, Amurka ta yi umarnin cewa ma'aikatan gwamnatinta d aiyalansu su bar Belarus, tana mai cewa "akwai damuwa sosai kan girke dakarun da Rasha ke yi.
Sannan ta bayar da irin wannan umarnin ga ma'aikatan gwamnatin Amurka da iyalansu na Ofishin Jakadancin Amurka da ke babban birnin Ukraine wato Kyiv.
Rasha na son ƙasashen yamma su yi alkawarin cewa ba za su taɓa haɗa kai da ƙawance Nato ba - inda mambobinta suka yi alkawarin taimakon juna idan an kar hari - amma Amurka ta yi watsi da buƙatar.
Mambobin Nato 30 ne da suka haɗa da Amurka da Birtaniya da Lithuania da Latvia da Estonia - da kuma tsohuwar tarayyar Sabiyet da ke kan iyakar Rasha. Rasha na ganin dakarun Nato a gabashin Turai a matsayin wata barazana ga tsaronta.
Mista Purin ya daɗe yana ja in ja da Amurka kan cewa ta karya alkawarin da ta yi a 1990 cewa Nato ba za ta ƙara faɗaɗa ayyukanta ta gabas ba, duk da cewa kowa da irin fassarar da ya bai wa hakan.
Rasha ta mamaye yankin Crimea na kudancin Ukraine a 2014. Tana kuma goyon bayan ƴan awaren da suka ƙwace iko da manyan yankuna a yankin gabashin Donbas, kuma mutum 14,000 ne suka tsere tun farkon fara faɗan.