Amurka ta gargadi Rasha ta zabi zaman lafiya ko tashin hankali

Amurka ta gargadi Rasha da cewa dole ne ta zabi abu daya ko dai zaman lafiya ko kuma fito-na-fito da kasashen Yammacin Duniya a kan Ukraine.

Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurkar Wendy Sherman ce ta yi gargadin a yayin da take jawabi, bayan tattaunawa tsakanin kungiyar tsaro ta Nato da Rasha.

Ganawar da ke zaman daya daga cikin abubuwa uku na diflomasiyya da aka tsara a makon nan, da nufin rage zaman tankiya da kallon hadarin-kaji da ake yi tsakanin Rasha da kasashen Yamma kan Ukraine.

Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen na Amurka, Ms Sherman a yayin wannan jawabi inda ta gargadi Rashar kan take-takenta a kan Ukraine, ta jaddada cewa Amurka da sauran kawayenta mambobin kungiyar tsaro ta Nato ba za su taba yarda da hawa kujerar na-ki ba kan karbar Ukraine a cikin kungiyar ba.

Inda ta yi nuni da cewa kawancen na tsaro yana da tsari na bayyane na karbar mai son shiga.

Shiga kungiyar tsaro ta Nato wani buri ne da ke cikin kundin tsarin Mulki na Ukraine.

Ms Sherman ta ce duk da yadda lamari yake akwai fannonin da za a iya samun ci gaba, wanda kuma dole ne Rasha ta zabi abin da take son ganin ya faru nan gaba,

Ta ce, game da Rasha dole ne yawanci su duba su gani tare da yanke shawara idan lalle kan batun tsaro ne, wanda idan hakan ne to za su yarda da tattaunawar, idan kuwa baba-rodo ne kawai ake yi, an fake da batun tsaron ne abin da ba za a iya sani ba a yanzu lalle.

Ta ce duka ma dai yadda abu ya kasance Amurka da Nato a shirye suke.

Sai dai a martaninta, Rasha ta bakin Mataimakin Ministanta na Waje Alexander Grushko, ta ce kungiyar Nato ba za ta yi wa bukatun rasha tankade da reraya ba, ta zabi wadanda take gani su ne na-gari, sannan ta yi watsi ta sauran,

Daga cikin bukatun dai akwai cewa Ukraine ba za ta taba shiga kungiyar tsaro ta Nato ba.

Mista Grushko ya yi gargadin cewa muddin dangantaka ta kara tabarbarewa a tsakaninsu to fa hakan ba zai yi wa harkar tsaron Turai dadi ba.

Wanda wannan kalami ne da ya zo daidai da abin da Babban Sakataren kungiyar Nato Jens Stoltenberg, wanda ya ce akwai hadari nag aske na samun sabon rikicin makamai a Turai.

Rahotanni dai na cewa akwai kusan dakarun Rasha dubu dari daya da ke girke a kusa da iyakarta da Ukraine, abin da ke sa ana fargabar cewa ko Rasha za ta yi mamaya ne.

Ganin cewa a shekara ta 2014 Rasha ta kwace, sannan ta mamaye yankin Crimea na Ukraine, bayan da 'yan Ukrain din suka yi wa shugaban kasarsu mai bin ra'ayin Rasha,

Sannan kuma dadin dadawa gaba a cikin wannan shekara 'yan aware da ke samun goyon bayan Rasha suka kama yanki mai yawa a gabashin Ukraine.

Ita dai Rasha ta bayyana jerin bukatu da take so da nufin kare kungiyar Nato ta kara fadada zuwa gabas, tare kuma da ganin an rage kasancewar kungiyar a kusa da iyakar Rashar.

To amma kuma nan take Nato ta sanya kafa ta yi watsi da bukatu ko sharuddan na Rasha, said ai ta ce a shirye take ta tattauna a kan wasu batutuwan, da suka hada da takaita yawan makamai da kuma atisayen soji.

Nato kungiya ce ta tsaro ta kasashen da ke yankin arewacin tekun Atalantika, wadda aka kafa ta a shekarar 1949, kuma ta kunshi kasashe 30.

Idan har Rasha ta yi watsi da tayin tattauna batun tsaro da Nato da za a yi a makon nan, to hakan zai sa a ga yadda hadin kan Turai da Amurka zai karke,