Batun Ukraine: Putin ya faɗa wa Biden cewa sanya wa Rasha ƙarin takunkumi zai zama babban kuskure

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya gargaɗi takwaransa na Amurka Joe Biden a kan sanya wa ƙasarsa ƙarin takunkumi, abin da ya ce yana iya rusa alaƙar ƙasashen biyu ɗungurungum.

Yayin wata tattaunawa ta waya a ranar Alhamis, shugaban na Rasha ya ce irin wannan mataki yana iya mayar da hannun agogo baya a dangantakar da ke tsakaninsu.

A nasa ɓangaren shugaban Amurka Joe Biden ya faɗa wa Putin cewa Amurka da ƙawayenta za su mayar da martani da kakkausar murya idan Rasha ta yi yunƙurin mamayar Ukraine.

Kiran wayar wanda Rasha ta buƙaci a yi, shi ne irinsa na biyu a wannan watan, kuma an shafe kusan awa guda ana yinsa.

Wannan dai shi ne yunƙuri na baya-bayan nan na shawo kan balahirar da ta kunno kai a iyakar Rasha da Ukraine, inda dakarun Rasha fiye da dubu 100 suka hallara a wajen suna zaman jiran ko-ta-kwana.

Ita dai Rasha ta bayyana rahotannin cewa tana shirin yin kutse a Ukraine a matsayin ƙalen sharri, tana cewa dakarun na ta na kan iyaka ne don atisaye, kuma tana da ikon yin hakan.

Ko da yake shugabannin biyu sun ja kunnen juna yayin tattaunawar, mai bai wa shugaba Putin shawara kan harkokin difilomasiyya Yuri Ushakov ya ce uban gidan nasa ya amince da tattaunawar, kuma ta buɗe kofa ga wata tattaunawar a gaba.

Shi ma wani babban jami'i a Amurka da ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce shugabannin biyu sun yi magana irin ta girmama juna, kuma mai amfani.

A watan gobe ne ake sa ran jami'an ƙasashen biyu za su haɗu a Geneva don tattaunawa gemu da gemu, a don haka ne fadar White House ta Amurka ta buƙaci Rasha ta rungumi sasantawa.

Sharhi - daga Tara McKelvey,Wakiliyar BBC a fadar White House

Yanzu dai hankalin jami'an fadar White House ya dan kwanta musamman idan suna tattaunawa a wajen ɓangaren shugaban ƙasa.

Kiran wayar da aka yi tsakanin Shugaba Biden da Shugaba Putin ranar Alhamis, kamar yadda wani babban jami'in gwamnati ya shaida wa manema labarai da yammacin jiya, "wata tattaunawa ce mai muhimmanci, kuma mai ma'ana".

''Alamun da ake gani daga Rasha ba masu daɗi ba ne'' kamar yadda wani jami'i ya shaida mini, don haka an ƙara zage dantse don cimma maslaha.

A ranar Alhamis, aƙalla, shugabannin biyu suna magana kuma waɗanda ke Fadar White House suna ganin hakan a matsayin wata alama mai kyau. A yanzu. suna ƙoƙarin yin duk abin da za su iya don tabbatar da cewa sun ci gaba da magana a cikin sabuwar shekara.

Ministan tsaron Ukraine ya shaida wa majalisar dokokin kasar a farkon watan Disamba cewa, Rasha ta tara dubunnan dakaru a kusa da kan iyaka, kuma za ta iya yin shirin kai wani gagarumin farmakin soji a karshen watan Janairu.

Rasha dai ta yi nuni da cewa sojojin da aka girke a kan iyakar wani mataki ne na kariya daga kungiyar tsaro ta Nato, wato kawancen sojojin kasashen yamma, ko da yake tana son a bata tabbaci bisa doka cewa NATO ba za ta fadada harkokinta zuwa gabas ba, kuma ba za a aika wasu makamai ga Ukraine ko wasu ƙasashe maƙwabta ba.

Amurka ta yi watsi da abin da ta kira yunkurin Kremlin na sarrafa makomar ƙasashe masu cin gashin kansu.

Ba a bai wa Ukraine tayin zama mamban kungiyar Nato ba, amma tana da alaka ta kut-da-kut da kungiyar.

Luguden laɓɓa tsakanin Rasha da Ukraine ba wani sabon abu bane. Domin a 2014 ma sai da Rasha ta ƙwace iko da yankin Crimea na Ukraine, sannan daga bisani ta fara goyon bayan wata ƙungiyar ƴan aware a Ukraine, rikicin da ya janyo rasa rayuka dubu goma sha huɗu.

Amurka da ƙwayenta sun ja kunnen Rasha, ta kwana da sanin cewa za su kafa mata ƙahon-zuƙa labudda dakarunta suka sake yin gangancin ƙetarawa Ukraine.