Yadda aka yi wa ɗan luwadi rukiyya don sauya daɓi’arsa

Asalin hoton, Danne Aro Belmont
- Marubuci, Norberto Paredes
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
"'Iyayena sun kai ni cocin Katolika, inda suka yi min rukiyyar awowi da dama da nufin cire aljanin da ke jikina, da aka gama suka tambaye ni har yanzu ina jin cewa ni dan luwadi ne?"
Wannan shi ne abin da Danne ya iya tunawa, daga cikin azabar da aka gana masa saboda fitar da shi daga harkar luwadi kamar yadda iyayensa ke cewa shafar aljanu ce.
"Sun watsa min toka a fuska, tare da rirrike ni, sun ce sai an yi min wankan-tsarki saboda aljanun da ke jikina su ke sanya ni luwadi," in ji matashiyar mai shekaru 29 'yar Colombia, wadda ke daukar kanta mai jinsi biyu.
Tana daga cikin masu auren jinsi daya da ake tilastawa shiga wani sirrin sauya tunani, wanda yanzu kasashe da dama ke amfani da shi ciki har da inda aka haramta yi.
Danne ta ce tun tana shekara 11 suka fara yi mata, lokacin da ma ba ta san kanta ba, ba ma ta san abin da ke faruwa ba kuma lokacin da take amsa sunan namiji da aka rada mata suna tun lokacin da aka haife ta.
"Abin da kawai na sani shi ne ina son yara maza, kuma abin da nake so daban da abin da 'yan uwa na maza ke so," a hirar ta da BBC.
"Iyayena sun ji hirar da muke yi da abokaina, daga nan sai suka fara jero min tambayoyi."
Bayan tabbatar da dansu dan luwadi ne, sai iyayen Dane suka fara bincike domin sanin yadda za su sauya masa tunani.
"Sai aka bai wa iyayena shawarar cewa akwai wasu sinadarai a jikina da suka yi kadan, don haka aka fara ba ni kwayar magani, wai saboda mahaifiyata ta shagwaba ni, ko kuma an taba yi min fyade amma ban taba fada ba, kuma ba haka ba ne," in ji ta.
Bayan gwada hanyoyi da dama, a karshe iyayenta sun samu wata hanya da suka kira "amfani da addu'a domin sauya tunaninta na luwadi," wata zuwa wajen malaman coci.
Wani mabiyin addinin Kirista masanin halayyar dan adam, shi ya yi wa iyayenta bayani kan yadda tsarin yake.
Ba su fahimci yadda abin yake ba sosai, amma duk da haka suka amince a taimaka musu. A lokacin shekarun Danne 16.
Matakin farko
Ta ce wata rana, sai iyayenta suka ce ta raka su wata unguwa.
Abin mamaki a lokacin da suka tsaya gaban wata coci, saboda iyayenta ba mabiya darikar Katolika ba ne.
Suna shiga, sai ta fahimci an kai ta ne domin wani dalili da ba su fada mata ba.

Asalin hoton, Danne Aro Belmont
"Malamin cocin ya san komai akaina. Sun kai ne wani daki, sai aka fara yi min addu'a, ga kuma tarin mutane a wurin," in ji ta.
"Na ga yadda mutane ke taba kansu, da yin gaba da baya. Sai kuma su damko kaina, tare da angiza ni gaba, amma ban ji alamun ina son matsawa ba. Abin da ban-mamaki."
"Sai uka tambaye ni ko har yanzu ni dan luwadi ne, sannan ko aljanun da ke jikina sun fita."
Wannan ita ce hanya ta "farko" da aka dauki sama da awa daya ana yi.
Ta tuna yadda ta yi matukar gajiya bayan an gama wannan, sun kuma shaida ma ta "shaidanun aljanun da ke jikin ta sun fita, yanzu za ta samu lafiya."
''Zuki ta malle ce kawai. A hankali suna sanya maka tunanin akwai wani abu a jikinka maras kyau, sannan wai suna yi maka wankan-tsarki," ta kara bayani.
Daga karshe, sai ta yanke shawarar shaida musu cewa ita yanzu ba 'yar luwadi ba ce.
"Na sheka musu karya, kawai domin na fita daga wurin. Na san idan na ce har yanzu ni 'yar luwadi ce ba za su daina wahalar da ni ba."
Bayan sun koma gida, babu wanda ya kara tayar da zancen. "Amma gaskiya ina jin tsoro," in ji ta.
Ta ce a lokacin ba ta san komai da ya danganci hakkin dan adam ba, a makaranta ba ta samu goyon bayan malamai ba, kuma ba ta da kwarin gwiwa gaya wa iyayenta abin da suke yi ba daidai ba ne.
Wadannan abubuwan sun taru sun zame mata matsananciyar damuwa, har da tunanin kashe kanta.

Wani bincike da Jami'ar Coventry ta wallafa a shekarar 2021, inda ta tattauna da gwamman mutanen da aka yi amfani da hanyar tattaunawa da 'yan luwadi a matsayin magani, ta gano cewa babu wata shaidar hakan ya yi tasiri, amma sun gano yadda hakan ya shafi lafiyar kwakwalwar mutane.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 2020, wani rahoton da cibiyar bincike ta Williams da ke jami'ar koyon shari'a da ke California, sun gano wadanda ba mata maza ba na kungiyar 'yan luwadi da madigo LGB da akai musu amfani da hanyar tattaunawa a matsayin magani, akwai yiwuwar sun yi kokari ko yunkurin kashe kan su, idanaka kwatanta da wadanda ba ayi musu amfani da wannan hanyar ba.

'Rukiyyar cire aljanu'
Wata da watanni bayan yin rukiyyar farko, an sake mayar da Danne a karo na biyu, wani yanayi na tashin hankali fiye da na baya, kuma cocin da aka kai ta farko nan aka sake mayar da ita, anan ne aka rada mata suna tana jaririya kuma nan aka yi auren iyayenta.
They performed exorcisms on me, throwing holy water. They put candles everywhere, drew crosses with ashes on me and talked about what was wrong with me and my sexual orientation."
"Tare da 'yar uwata muka je, sun kuma shaida mana taron matasa ne, hakan bai ba ni mamaki ba saboda na saba zuwa tarukan yara da kamfanin da iyayena ke aiki sukan shirya."
Ana sanya su a cikin motar bas da 'yan uwa da iyayensu, a kuma kai su can wani yanki da ke wajen birnin Bogotá.
Abin da ake kira convivencia - a turance, wata hanya ce da ake bi a addinance, mai tsauri. Bayan kwanaki shida an sake yi mata irin na farko.
Kullu da sassafe suke tashin ta daga bacci a yi mata addu'a kafin karin-kumallo. "Daga nan sai na ci gaba da addu'a a tsawon rana, domin korar shaidanin da ke kaina, sannan matukar ban bi abin da suka fada ba, to kuwa ba za a ba ni abinci ko bari na bacci ba," kamar yadda ta bayyana.
"Suna wasu surkulle, da fesa min ruwan albarka. Sun kunna kyandira zagaye da inda muke zaman addu'ar da kuma kuros, ana kuma shafa mana toka a goshi, sai su yi da tsatsube-tsatsube suna fadin abin da ya sa nake yin luwadi saboda shaidanin da ke jikina ne."

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da mutane suka fara tuba daga aikata zunubi, sai a sanya su yin bayani a kan wasu mutanen da suka taba yin zunubin tare, a kuma ce suna auna su.
Idan su na son a bari su kwanta bacci, sai sun shekar karyar suna jin su wasai, babu wani shaidani da ke jikinsu.
"'Yar uwata ta roke ni don Allah na sauya hali na. Tana jin babu dadi kasancewarta 'yar uwar mata maza," in ji ta.
'Ba na son ci gaba da fada'
A karshe Danne ta ba da kai bori ya hau, kamar dai maganin farko, sai ta sake shaida musu ta bar luwadi.
A kan hanyarsu ta komawa gida, iyayenta su tambaye ko tana jin wani sauyi.
They make you feel that if you're gay, the only life options you have are to be a hairdresser or a prostitute. I didn't want that as a life project. I wanted to study astrology."
"Na shaida musu cewa na sauya. Ba na son ci gaba da fadan, idan na shaida musu har yanzu ban ji wani sauyi ba, za a ci gaba da kai ni cocin na ci gaba da fuskantar azaba."
Danne ta yi bayanin a lokacin da ta bar wuri rukiyyar, sai ta ji kamar kanta ya juye.
"Kana son warkewa da komawa harkokin da ka saba, saboda suna sanya ka tunanin abin da kake yi ba shi da kyau," in ji Dane.
''Suna sanya ka tunanin tamkar kai daya ne kake luwadi, tamkar kai daya ne kake aikatawa, ko kuma kai ka sanya kan ka a ciki ba wai halittar ka aka yi da shi ba,'' in ji Danane.
Daga nan ne sai ta fara bincike kan matsalar domin gano ko tana aikata sabo, bayan nan sai ta zauna da iyayaenta ta shaida musu gaskiyar halin da ta ke ciki.
Ta tabbatar mu su da gaskiyar cewa ita fa har yanzu 'yar luwadi ce, ta kuma yi musu bayani kan hakkin dan adam, ta kuma yanke shawarar shiga kungiyar LGBT da ke fafutukar karbowa mutane irin ta hakki.
A makaranta sai ta fara bayani akan batun da halin da mutane ke shiga idan ana tsangwamarsu.
Shekaru bayan nan, iyayenta suka ba ta hakuri, sannan suka raka ta tattakin kwato wa mutane irin ta 'yanci.
A yau Danne na aiki kai-tsaye ita ce daraka a kungiyar Gaat Foundation, wadda ke taimaka wa miliyoyin mutane da ake yi wa rukiyyar sauya jinsinsu, a Colombia da yankin Latin Amurka.
I used to say at school as a joke that they had performed an exorcism on me, that it hadn't worked for them and I was still the queer in the story."
"Ban san cewa ni ma an kai ni wajen rukiyya ba sai da na fara gangamin yaki da hakan," in ji ta.
"A makaranta cikin barkwanci na ce an taba min rukiyya, kuma ba tai min aiki ba, amma duk da hakan ina nan amatsayin sha kallo tsakanin mutane'."


Asalin hoton, Danne Aro Belmont
A karni na 20 ba sabon abu ba ne ayi amfani da masana halayyar dan adam domin magani ga 'yan luwadi, wasu daga ciki kuma na amfani da wutar lantarki domin azabtar da su da niyyar wai za su daina.
Amma a shekarar 1970, Kungiyar masana halaiyar dan adam ta Amurka ta shiga lamarin tare da ayyana l
uwadi a matsayin cuta. Sai kuma shekarar 1990, aka cire luwadi daga rukunin cutukan da Majalisar Dinkin Duniya ta ware.
Daga Majalisar Dinkin Duniya har Hukumar Lafiya ta Duniya da sauran kungiyoyi da hukumomin lafiya a fadin duniya suka yi gargardin cewa duk wata hanya da ake amfani da wajen sauya wa 'yan luwadi halayya ka iya zama mai cutarwa a gare shi.












