Yadda 'yan bindiga suka kashe wani dan kasuwar Kano bayan sun karɓi kudin fansa

Bindiga

Asalin hoton, Other

Ana ci gaba da alhinin mutuwar wani ɗan kasuwa a Kano arewacin Najeriya da masu garkuwa da mutane suka kama kuma suka kashe shi duk da cewa sun karɓi kuɗin fansa.

An sace Yahaya Hassan Musa yana kan hanyarsa ta dawo wa daga Cotonou a Jamhuriyar Benin a yankin Mopa na jihar Kogi.

'Yan bindigar sun sace Yahaya Hassan Musa ne kusan makonni biyu da suka gabata a dajin Mopa na jihar Kogi lokacin da yake komawa Kano daga harkokin kasuwancin da je jamhuriyar Benin.

Dan uwan mamacin ya shaida wa BBC cewa masu garkuwar sun kashe shi sannan suka jefar da gawarsa a daji.

Ya ce bayan ya ba su kudin suka zaunar da shi a dajin ba tare da yi masa bayanin halin da ɗan uwansa ke ciki ba.

"A dajin muka tsinci gawarsa muka yi masa jana'iza," in ji shi.

Wannan na zuwa ne bayan da aka samu gawar wasu mutum uku a yankin Chikun na jihar Kaduna wadanda su ma 'yan bindigar suka kashe su duk da cewa suna tattaunawa da 'yan uwansu.

Mazauna garin Unguwar Bulus sun bayyana cewa 'yan bindiga ne suka kashe mutanen cikin wadanda suka sace kwanakin makonni biyu da suka gabata.

Al'amarin ya auku ne a dai-dai lokacin da mutanen garin ke tattaunawa da 'yan bindigar.

Rev Josep John Hayap wani jagoran al'umma a jihar Kaduna, ya ce al'ummar da lamarin ya shafa suna cikin tashin hankali da rashin tabbas.

"Ba mu san yawan adadin mutanen da suke hannun ƴan bindiga ba, domin suna da yawa," in ji Rev Josep John Hayap

Rahotanni sun ƴan bindigar sun nemi a biya su naira miliyan 20 ga duk mutum ɗaya da ke hannunsu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ASP Mohammad Jalinge bai ce komi ba game da al'amarin kuma BBC ta tuntube shi amma bai amsa kiran waya ba.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da 'yan bindiga suka sace ke cika mako uku a hannu wadanda suka yi garkuwa da su, wadanda ake fargabar sun fi mutum ɗari.