Jirgin ruwan yakin Rasha Moskva ya nitse a Bahar Aswad

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce jirgin ruwanta na yaki da aka lalata yayin wata fashewa ranar Laraba ya nitse.

Jirgin ruwan mai suna Moskva, wanda babba ne, ana janye shi ne lokacin da "guguwar teku" ta sa ya niste, a cewar wani sako da ma'aikatar ta fitar.

Jirgin mai iya daukar mutum 510 wata alama ce ta karfin sojin Rasha, wanda yake jagorantar yaki ta ruwa da ake yi da Ukraine.

Sai dai hukumomi a Kyiv sun ce makamai masu linzami ne suka fada kan jirgin ruwan na yaki. Jami'ai a Moscow ba su bayya cewa an kai masa hari ba - sai dai sun ce jirgin ya nitse ne bayan wata wuta ta tashi.

Gobarar ce ta sa makama da abubuwan fashewar da ke cikinsa suka kama da wuta, a cewar Rasha, inda ta kara da cewa sojojin ruwanta sun kwashe dukkan mutanen da ke cikin jirgin a wasu kwananana jiragen ruwa da ke Bahar Aswad.

Da farko Rasha ta ce jirgin yana cikin teku, amma ranar Alhamis ma'aikatar tsaronta ta ce Moskva ya nitse.

Jirgin mai nauyin tan 12,490 shi ne jirgin ruwan yakin Rasha mafi girma da ya nitse a teku tun bayan Yakin Duniya na Biyu.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce "a yayin da ake janye shi zuwa... gabar teku, jirgin ya nitse saboda lalacewar da ya yi sakamakon gobarar da ta tashi bayan abubuwan fashewa sun yi bindiga." t

Rundunar sojan Ukraine ta ce ita ce ta kai hari kan Moskva da wasu makamai masu linzami da kasar ta kera masu suna Neptune - makaman da aka kera bayan Rasha ta kwace yankin Crimea a 2014.

Amurka ta bayyana 'nitsewar' jirgin ruwan yakin a matsayin wani "babban koma-baya", sai dai jami'an gwamnatin Amurka ba su tabbatar ko makamai masu linzamin Ukraine na Neptune ne suka lalata jirgin ruwan ba.