Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Vladimir Putin: Masu tsananin goyon bayan shugaban Rasha a Facebook
- Marubuci, Daga Jack Goodman & Olga Robinson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilan BBC
Kutsawar kasar Rasha cikin Ukraine ta gamu da yin Allah-wadai a sassan duniya da dama, amma kuma wasu kungiyoyin mutane maso bibiyar shafin Facebook da mutane masu jan ra'ayi a kaikace ke son sauya tunanin jama'a game da shugaban kasar.
Miliyoyin mutane sun kalli hotunan da aka yada da ke nuna Shugaba Vladimir Putin a matsayin mai murmushi, mai dattaku da kuma kaunar zaman lafiya.
Wadannan su ne masu matukar goyon bayan Putin - kuma mun bi diddigin abubuwan da suke yi daga kuma inda suka fito.
Adadi masu yawa
BBC ta gudanar da bincike kan wadannan kungiyoyi masu goyon bayan Putin tare da taimakon kwararru daga cibiyar bincike ta Institute for Strategic Dialogue (ISD).
Kwararrun a cibiyar ta ISD sun gano kungiyoyi Facebook goma, na yin alfahari da sunaye irin su Vladimir Putin - Gwarzon Shugaban Duniyar 'Yanci. Kungiyoyin na da mambobi fiye da 650,000 a tsakaninsu.
Abubuwan da suka kunsa sun hada da hotuna da sakonni da ke yaba wa da shugaban Rasha, da aka rubuta da harsuna da dama da suka da Turanci, da Farsi, da Larabci, da kuma Khmer.
Ba fice kawai suka yi ba, har ma da kasancewa cikin aiki a ko da yaushe. A cikin watannin da suka gabata masu binciken sun lissafa hotuna da sauran abubuwan da aka yada kimanin 16,500, tare da samun mutanen miliyan uku da dubu dari shida da suka tattauna a kai.
Daukacin bukatar kungiyoyin da alamu shi ne su tallata Mista Putin a matsayin wani gwarzo da ya jajirce wa kasashen Yamma, da kuma goyon bayan kasashen waje mai matukar yawa.
Hotunan suna yawan nuna shugaban Rasha ''na tafiyar kasaita da karfin guiwa, rike da 'yan kwikwiyo, yana kallon kyamara, tare da jijina wa dakaru.
Wadannan kungiyoyi sun kara samun sabbin mutane fiye da 100,000 tun bayan fara kutsawar Rasha kasar Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.
Bayan bin diddigin cikakkun bayanai game da mutanen da ke yada akasarin hotunan da bidiyon, abubuwa sun bayyana cewa akasarin magoya bayan da aka bayyana a matsayin masu jagorantar kungiyoyin na da shafuka da yawa da suka bude da suna iri daya.
Masu binciken sun gano shafuka akalla 100 a shafin na Facebook.
Galibi wadannan shafuka na bibiyar juna kum a wasu lokuta su kan wallafa sakonni gaisuwa ko kuma su tura wa junansu alamomin gaisuwa na emojis.
Sannan sukan tafiyar da wadannan shafuka na goyon bayan Putinn tare da sauran suna nuna kamar na hukumar tsaro ta kasar Rasha ko na gwamnatin kasar Rasha ne, wanda duka a bayyane ta ke cewa karya ne.
Amfani da shafuka biyu karya dokokin shafin na Facebook ne kan halayyar rashin gaskiya, in ji ISD.
Jagoran masu binciken Moustafa Ayad ya danganta dabi'ar a matsayin "yaudara" - gudanar da abubuwa a shafin intanet da suka kunshi amfani da shafuka da dama da ke nuna cewa mutum da na goyon baya mai yawa, amma duka karya ne.
Kamfen "na kirkirar nuna gagarumin goyon baya ga shugaba Putin da fadar Kremlin a yayin kutsawar Rasha cikin Ukraine kuma ya dogara kan …shafukan karya don cimma buri,'' kamar yadda rahoton ISD ya bayyana.
Masu amfani da shafin a koda yaushe
Binciken kwakwaf kan wasu daga cikin kungiyoyin ya nuna wasu ayyuka da ba a saba gani ba.
Daya mai suna Marine, wacce ta ce tana zaune a Syria, na amfani da wasu shafuka daban wajen samar wa shugaban kasar goyon baya. Shafukanta uku, da harshen Larabci da ta ke yadawa a lokaci guda a kullum.
Wata mai gudanarwar, Victoria daga kasar Cambodia, ta yi ta yada abubuwan a cikin kungiyar harshen Khmer. Tun a ranar 4 ga watan Fabrairu abubuwan da ta wallafa suka samu martani fiye da 34,000 kama an yada su sau fiye da 4,000.
Kuma Marine da Victoria sun yi hadin guiwa wajen tafiyar da shafin Facebook da harshen Khmer, bangaren fadadar hadewa da wasu daga cikin shafukan.
Mun yi kokarin tuntubar mutanen da ke da alhakin bude duk wadannan shafuka don ji daga gare su, amma ba mu taki sa'a ba.
Amma wani mutum a kasar Kenya da ake kira Raj, da ke cikin irin wadannan kungoyoyi da dama wanda ya hada da sunan "Putin" a karshen sunansa na shafin Facebook, ya amsa wayar da muka buga.
A wata gajeriyar tattaunawa ya ambaci shugaban kasar a matsayin ''gwarzon shugaba'' amma ya ki a tattauna da shi game da batun yakin.
Mun aike masa da karin tambayoyi game da dalilan da suka sa yake kaunar Rasha, amma bai bayyana komai ba.
Hasmik daga Armenia, ta bayyana cewa ita 'yar jarida ce kuma yanzu tana taimakawa wa wajen tafiyar da kungiyoyi shida. Mun tambaya ko wane ne ya gayyace ta don gudanar da hakan.
Ta shaida mana cewa mutanen da suka riga suka bude shafukan kungiyoyin ne amma ba ta bayar da sunaye ba, amma ta tabbatar da cewa ba kudi aka biya ta ba kan kokarin da ta ke yi.
Alaka da Rasha?
Yana da matukar wahala ka iya gano abubuwan da suka ja ra'ayin wadanda ke da hannu wajen bude shafukan.
Babu wani abu a fili da ya nuna alakarsu da gwamnatin Rasha, kuma ba kamar sanannen rudun tallata kasar Rasha ba, kungiyoyin ba su da wasu dabaru; haka mutanen da ke ciki ba sa boye aniyarsu.
Amma ba za mu iya kauce wa yiwuwar cewa kungiyoyin na da alaka da mahukuntan kasar Rasha ko wasu magoya bayan Putin a cikin kasar Rasha ba.
Mutane da dama a fadin duniya hankulansu sun karkata kan Mista Putin da matsayinsa a kan kasashen Yammacin duniya.
Mun tuntubi kamfanin Facebook, wanda ya bayyana cewa yana da dokoki a kan shafukan bogi kuma ya dakatar da shafuka da dama da ya gano a wani rahoto da aka tura masa kana daga wasu daga irin bincikensu.
Shafukan bogi na Putin
A yayin gudanar da binciken, mun ci karo da wani abu mai ban-mamaki - shafukan bogi na Vladimir Putin.
Mista Putin daya daga cikin shugabannin kasashen duniya kadan ne da ba sa amfani da shafukan sada zumunta, kuma babu wani shafin Facebook a hukumance da sunansa.
Ya kuma musanta mallakar wayar zamani ta komai-da-ruwanka.
Kamar yadda mai magana da yawunsa ya bayyana, Mista Putin ''ba ya bukatar'' shafukan sada zumunta saboda ''ba zai ba shi duk wani abu da bai riga ya mallaka ba''.
Amma wasu sun cike gurbin da ya bari na rashin kasancewarsa a intanet. Shafin Facebook da aka nuna a sama, na da mabiya fiye da miliyan uku kafin a toshe shi jim kadan bayan mamayar kasar Ukraine a karshen watan Fabrairu.
Adadi mai yawa na masu amfani da shafin - fiye da 700,000 - sun shiga ne lokacin annobar korona, a lokacin da shafin ke magana kan cewa Russia ta kirkiri allurar rigakafin korona.
A baya-bayan nan, shafin na wallafa sakonni da ke kara fadada ra'ayin fadar Kremlin game da yakin, kuma da dama martani da suka mayar a kai ya nuna amannar ya kunshi sahihan kalamain shugaban kasar Rasha.
Jim kadan bayan kutsawar, wani abu da aka wallafa ya ayyana burin ''ayyukan sojin'' shi ne ''neman zaman lafiya …na burin rage wa kasar makwabciya karfin soji''. An yi ta yada wannan sako tare da danna alamar like har fiye da 200,000.
Kana shafin na da halayyar tura wa mutane sakonni a kan shafukansu game da Mista Putin, da suka hada da masu amfani da shafukan da masu binciken suka gano na kara kofin shafukan.
Ta wani gefen kuma, yana tattauna wa da masu tsananin goyon bayan Putin.
Ba mu san ko su wane ne suka bude wannan shafi ba. Mutanen da ke tafiyar da shi na zaune ne a kasashen Russia da Latvia, kamar yadda bangaren nuna gaskiya na shafin ya nuna.
Shafukan magoya bayan dandali ne ma kyua na kada gangar neman samun goyon baya ga fadar Fan Kremlin daga kasashen duniya, in ji Nika Aleksejeva, wata mai bincike a dakin cibiyar binciken kimiyyar masu aikata laifi ta (DFRLab).
"Za su iya taimakawa wajen samun goyon bayan jama'a ga kasar Russia a kasashen waje kan ayyukan sojinta a kasar Ukraine, muddin ba dakatar da shi manyan shafukan sada zumunta suka yi ba,'' ta ce.
Cibiyar binciken ta DFRLab ta tattara bayanau kan yadda wani shafin Putin na sojan-gona da ke gudana da harshen Larabci ya biya tallace-tallce da ke kalubalantar masu amfani da shafuman a kasashe da dama da suka hada da Algeria, da Libya, da Masar, da Yemen, da Morocco,da Lebanon da kuma Tunisia. Wannan shafi na da mabiya fiye da miliyan daya, amma tuni aka goge shi.
Wani sanannen shafin Putin, da ake tafiyarwa da harshen Larabci na karkashin kulawar wani mutum wanda shi ma wani babban mai goyon bayan shugaban kasar Syria Bashar al Assad ne. Ya kuma samu mabiya kusan miliya daya kafin a cire shi..