Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Ukraine: Wadanne makusantan Putin ne ke jagorantar yakin?
- Marubuci, Daga Paul Kirby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Ana iya cewa Vladimir Putin ne shi kadai ke jagorantar mamaya mai matukar sarƙaƙiya da Rasha ke kai wa Ukraine, yakin da ka iya yin illa ga tattalin arzikinta.
Ba a saba ganinsa cikin wannan halin na kadaici ba, inda a cikin wasu tattaunawa biyu da ya yi da aka gansa yana zaune a nesa da makusantansa.
A matsayinsa na babban kwamandan sojojin kasar, shi ke da ikon yanke hukuncin kai hari wata kasa, sai dai dama ya dade yana dogara da wsu makusantan nasa, wadanda yawancinsu sun fara aiki ne a hukumomin tsaro na kasar.
Tambaya a nan ita ce: Su waye Putin ke jin maganarsu a wanna lokaci mafi muhimmanci na mulkinsa?
Idan akwai wanda Putin ke saurara, tilas a saka tsohon na hannun damansa Sergei Shoigu, wanda ke tallata kalaman Mista Putin na raba Ukraine da makamai da kuma kare Rasha daga abin da take cewa hatsarin ƙyale yammacin Turai ta jibge makamai a maƙwabciyar kasar ta Ukraine.
Shi ne mutumin da ke tafiya yankin Saberiya tare da shugaban kasar domin su yi farautar namun daji ko kamun kifi, kuma a shekarun baya an rika hasashen shi ne zai gaji Putin.
Amma idan ka kalli hotonsa yana zaune a karshen wani dogon tebur tare da babban hafsan sojojin kasar, ba shakka za ka fara yin tantama ko yana da sauran fada a wannan lokacin.
An dauki wannan hoton ne kwana uku bayan da Rasha ta fara mamaye Ukraine, inda ta fuskanci cikas daga dakarun kasar.
"An sa ran cewa Shoigu zai kwace birnin Kyev ne cikin wani kankanin lokaci," kamar yadda Vera Mironova wacce kwarariya ce a batutuwan tsaro.
Shi ne kuma ya jagoranci mamayar da Rasha ta yi wa Crimea a 2014. Ya taba zama shugaban hukumar leken asiri ta sojojin kasar, GRU.
Lamarin ya fi bayyana sosai idan aka janyo hoton kusa. "Sun yi kama da wadanda aka sanar cewa wani ya mutu - kamar suna halartar jana'iza ce," in ji Ms Mironova.
Sai dai duk da yadda ya bayyana a hoton, amma wani masani kan tsaro kuma marubuci Andrei Soldatov na ganin ministan tsaron hi ne mutumin da yafi kowa samun fada.
"Ba sojoji kawai Shoigu ke kulawa da su ba, har ma da wasu batutuwa kamar makomar Rasha a tarihin duniya."
Valery Gerasimov shi ne shugaban ma'aikata, kuma aikinsa ne gudanar da mamayar Ukraine cikin hanzari kuma da alama ya gaza.
Wasu rahotanni na cewa an ware shi guri guda saboda yadda harin na Ukraine ke gudana da rahoton da ke cewa wai sojojin Rasha sun karaya.
Ana bayyana Janar Gerasimov a matsayin wanda ya taka muhimmiyar rawa a harin na Crimea da na Chechniya a 1999 kuma yana cikin jami'an da suka shirya mamayar da ake kai wa Ukraine, inda ya sa ido kan rawar dajin sojojin Rasha a kasar Belarus a watan jiya.
"Patrushev mutum ne mai son a dauki tsauraran matakai, kuma yana cikin masu tunani cewa kasashen yammacin Turai sun dade suna son ganin bayan Rasha," inji ben Noble, wanda malami ne mai koyar da siyasar Rasha a jami'ar University College ta birnin London.
Yana cikin makusantan Putin uku da suka yi aiki tare da shi tun shekarun 1970 a birnin St Petersburg, lokacin da ake kiran birnin da tsohon sunansa na Leningrad.
Da wuya a sami wanda ke da karfin fada a ji kan shugaba Putin kamar Nikolai Patrushev.
Ya yi aiki a tsohuwar hukumar leken asiri ta KGB tare da shi a shekarun da jam'iyyar kwaminisanci ke mulki, kuma shi ne ya gaje shi a hukumar da ta maye gurbin ta wato FSB daga 1999 zuwa 2008.
Nikolai Patrushev ba shi da matsala. "Shi ne ke gaba-gaba cikin masu fara daukan matakin yaki, kuma ana ganin Puti na amfani da shawarwarinsa sosai," inji Ben Noble.
Masu nazarin siyasar Kremlin na cewa shugaba Putin ya amince da dukkan bayanan da yake samu daga hukumomin tsaron kasar fiye da wanda yake samu daga wasu wuraren, kuma ana kallon Alexander Bortnikov cikin makusantan da Putin yafi saurara.
Shi ma tsohon hannu ne wanda tun zamanin da Putin ke aiki a ofishin KGB na Leningrad suke tare, kuma shi ne ya gaji Nikolai Patrushev bayan da ya bar mukaminsa a hukumar ta FSB.
Hukumar FSB na da iko sosai kan sauran hukumomin tsaro na Rasha kuma tana da dakarunta na musaman.
Wannan ne mutum na uku cikin mutanen da suka yi aikai tare da Putin a Leningrad, kuma sun dade suna tare da shi.
Ben Noble ya shaida wa BBC cewa babu alama yana jin dadin dangantakarsa da Shugaba Putin, musamman idan aka tuna da yadda shugaban ya rika sukarsa a bainar jama'a yayin wani taron majalisar tsaron kasar.
Yayin da Putin ya tambaye shi abin da zai ce, sai ya rika kame-kame, har sai da Putin ya ce masa: "Ba wannan batun muke tattaunawa akai ba."
"Abin al'ajabi ne. Mutum ne natsattse, saboda haka sai mutane suka rika tambayar abin da ke faruwa," inji Ben Noble.
Amma Andrei Soldatov na ganin yana wsa da hankulan mutane ne kawai: "Putin na son yin wasa da hankalin jami'ansa, abin da yasa ake ganin kamar ya muzanta Naryshkin ne."
A bara ya tattauna da wakilin BBC na birnin Moscow Steve Rosenberg inda ya musanta cewa Rasha ce ta kai hare-haren guba kan wasu 'yan kasar da kuma hare-haren intanet da yin katsalandan a tsarin demokradiyyar wasu kasashe.
Sergei Lavrov ya shafe shekara 18 yana jagorantar ayukan diflomasiyyar Rasha da kasashen duniya duk da cewa wasu na ganin ba ya taka rawa kai tsaye wajen hukunce-hukuncen da gwamnatin Rasha ke dauka.
Sergei Lavrov mai shekara 71 alama ne cewa Putin na dogara da jami'an da ya dade yana mu'amulla da su.
Mutum ne mai wayo matuka: A watan jiya ya yi kokarin muzanta sakatariyar harkokin waje ta Birtaniya Liz Truss domin rashin kwarewarta kan taswirar Rasha, kuma a bara ya so ya tozarta shugaban bangaren harkokin waje josep Borrell.
Sai dai da alama ba a yi da shi kan batutuwan da suka shafi mamayar Ukraine, duk da cewa ba ya nuna haka.
Kuma babu alamar ya damu da ficewar da yawancin jami'an hukumar kula da 'yan gudun hijira suka yi yayin da yake gudanar da jawabi ta intanet domin kare mamayar da Rasha ke kai wa Ukraine.
Akwai kuma Valentina Matviyenko wadda ita ce mace daya tilo da ke cikin makusantan shugaban na Rasha.
Ita ce ta tabbatar da majalisar dattawan kasar ta amince da tura dakarun Rasha zuwa kasashen waje, matakin da ya ba su damar yin mamayar. ta Ukraine
Valentina Matviyenko ma tun shekarun da Putin ke aiki a St Petersburg suka saba kuma ta taimaka masa wajen kwace yankin Crimea da Rasha ta yi a 2014.
Su wane ne kuma Putin ke jin maganarsu?
Firaminista Mikhail Mishustin ne aka dora wa jan aikin farfado da tattalin arzikin kasar kuma ba ya taka rawa kan batutuwan yaki.
Magaji Garin Moscow Sergei Sobyaninda shugaban kamfanin man fetur na kasar Igor Sechin makusantan shugaban na Rasha ne, kamar yadda wani mai nazarin siyasar kasar, Yevgeny Minchenko ke cewa.
Sai kuma attajiran nan 'yan uwan juna Boris da Arkady Rotenberg, wadanda abokansa ne tun suna yara. A shekarra 2020, mujallar Forbes ta saka su cikin attajirai mafi yawan kudi a Rasha.
Akwai karin bayanai daga Olga Ivshina da Kateryina Khinkulova na SashenRashanci na BBC.