Yakin Ukraine: Yadda 'yan Rasha ke jin radadin takunkuman tattalin arzikin da aka saka wa ƙasarsu

    • Marubuci, Daga Anastasia Stognei a Moscow da Simon Fraser a London
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

"Idan da zan iya barin Rasha a yanzu haka, da na tafi. Amma ba zan iya barin aikina ba," a cewar Andrey.

Ba zai iya biyan bashin sayen gida da ake bin sa ba a Moscow a yanzu da kuɗin-ruwan da ke kai ya ƙara yawa.

Miliyoyin ƴan Rasha kamarsa sun fara jin tasirin takunkuman tattalin arzikin da ƙasashen Yamma suka ƙaƙaba wa ƙasarsu a jikinsu, waɗanda aka tsara su don ladabtar da ƙasar kan kutsen da ta yi wa maƙwabciyarta Ukraine.

"Ina tsara yadda zan samu sabbin abokan ciniki a ƙasashen waje da gaggawa don na bar Rasha da ɗan kuɗin da na yi ta tarawa a kason farko," in ji mai tsara masana'antun mai shekara 31.

"Ina jin tsoro a nan - ana kama mutane saboda sun yi magana a kan wannan batun. Na kunyata don ma dai dama ban zaɓi shugabannin da ke kan mulki a yanzu ba."

Kamar waɗanda aka yi hira da su a wannan maƙala, ba mu yi amfani da cikakken sunansa ko nuna fuskarsa ba saboda dalilai na tsaro, an sauya wasu sunayen.

An bayyana takunkuman da aka ƙaƙabawa Rasha a matsayin tattalin arzikin yaƙi - waɗanda aka sa su don mayar da ƙasar saniyar-ware da kuma ƙirƙirar matsananciyar masassarar tattalin arziki.

Shugabannin ƙasashen Yamma na fatan waɗannan matakan da ba a saba gani ba za su kawo wani sauyin tunani a Fadar Kremlin.

Ƴan ƙasar Rasha suna fuskantar matsalar ɓacewar kuɗaɗen ajiyarsu. Tuni an hargitsa al'amuransu na yau da kullum.

Takunkuman da aka sanya wa wasu bankunan Rasha sun haɗa da cire su daga tsarin amfani da katunan cira da aika kuɗaɗe na Visa da Mastercard, da kuma amfani da manhajojin Apple Pay da Google Pay.

Daria, mai shekara 35, wani manajan tsara ayyuka a Moscow, ya ce ba ya iya amfani da jirgin ƙasa.

"Da ina iya biyan kuɗi da wayata amma yanzu ba ya aiki sam. Akwai ma wasu mutanen da suke fuskantar irin wannan matsalar.

Abin yana aiki ne a ƙarƙashin bankin VTB wanda yake cikin waɗanda takunkuman suka shafa don ba ya iya karɓar kuɗin da aka biya ta manhajar Google Pay da Apple Pay.

"Dole ta sa na sayi katin zirga-zirgar jiragen ƙasa a maimakon hakan," ya shaida wa BBC. "Kuma ko yau ma ban iya sayen komai a kanti ba - saboda dai wannan dalilin."

Idan ku 'yan Najeriya ne mazauna Rasha, ku aiko mana da labarin halin da kuke ciki na yadda takunkuman da aka sanya wa ƙasar ke shafarku, ta hanyar cike fom ɗin da ke ƙasa.

A ranar Litinin ne Rasha ta ƙara yawan kuɗin ruwanta zuwa kashi 20 a matsayin mayar da martanin kan takunkuman bayan da darajar kuɗinta na rouble ya faɗi ƙasa warwas.

Kasuwar hannayen-jari ta kasance a rufe yayin da ake tsaka da fargabar sayar da hannayen-jari.

Fadar Kremlin ta ce tana da isassun abubuwan da za ta kauce wa dukkan takunkuman da aka saka mata, amma sai an yi muhawara kan hakan.

A ƙarshen mako ne babban banki ya yi kira da a kwantar da hankali a yayin da ake tsaka da fargabar kar kuɗaɗe su ƙare a bankuna, saboda yadda mutane ke rububin cire kuɗi.

"Babu daloli, babu rouble - ba komai! Ko akwai roubles ba su nake buƙata ba," in ji Anto (wanda aka musanya sunansa), wanda ke cikin shekaru 20 muka kuma same shi a kan layin cirar kuɗi a Moscow.

"Ban san me kuma zan yi ba. Ina tsoron cewa mun koma tamkar Koriya ta Arewa ko Iran a yanzu haka."

Ƴan Rasha na kashe fiye da kashi 50 cikin 100 wajen sayen kuɗaɗen ƙasashen waje fiye da yadda suka yi a makon da ya gabata - idan ma har za su samu ɗin kenan.

A farkon shekarar 2022 ana sayar da dala ɗaya a kan rouble 75, euro kuma a kan rouble 80. Amma yaƙin ya taimaka wajen kafa sabon tarihi na tsadar kuɗaɗen - a ranar Litinin sai da aka zo gaɓar da dala ɗaya ta kai rouble 113, yuro kuma ya kai 127.

Ga Rashawa, dama batun farashin dala da rouble abu ne da ya daɗe yana damunsu.

A shekarun 1990 bayan rushewar Tarayyar Sobiyet, dala ce kawai kuɗin ƙasashen wajen da Rashawa ke adanawa - a can ƙarƙashin katifunsu.

A lokacin da gwamnatin Shugaba Boris Yeltsin ta gaza biyan bashinta a shekarar 1998, waɗanda suka dinga bacci da kuɗaɗensu a ƙasan katifunsu suna jin kamar gaskiyarsu ta tabbata.

Sai dai, a cikin gomman shekarun da suka biyo, matakan babban banki da dama sun taimaka wajen bai wa Rashawa ƙwarin gwiwa a kan rouble.

Yawan kuɗaɗen da ake ajiyewa na Rasha ya yi ta bunƙasa haka ma kuɗaɗen da Rashawa suka zuba jari a kasuwannin hannayen jari na kamfanonin Rasha.

Sai dai duk da haka, a duk lokacin da Rashawa suka ga alamu na rashin tabbas, sukan garzaya na'urorin ATM mafi kusa don cire daloli.

Ko a wannan lokacin ma ba abin da ya sauya daga hakan.

Ɓarkewar yaƙi ke da wuya a Ukraine a makon jiya, Rashawa suka durfafi wuraren cire kuɗi, suna tunawa da darussan da suka koya a rikice-rikicen baya.

Ilya (an sauya masa suna), wanda ke cikin shekarunsa na 30, kwanan nan ya kammala biyan bashin gidan da ya karɓa a moscow. Ya ce ya kasa tarewa nan kusa.

"A lokacin da aka fara rikicin a Donbas na tafi ATM na cire kuɗaɗena da suke ajiye na daloli a Sberbank. A yanzu suna ƙarƙashin filona da su nake kwana.

"Sauran kuɗaɗen ajiyata na bankuna: rabi daloli ne sauran kuma rouble ne. Idan abubuwa suka rincaɓe, zan cire sauran. A tsorace nake saboda ina zaton za a samu kwararar ɓarayi."

Hotunan da suka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna dogwayen layuka a na'urorin ATM da kuma yadda ake ta musayar kuɗaɗe a kwanakin nan, inda mutane ke cikin damuwar cewa katunan bankinsu za su daina aiki ko za a ƙayyade yawan kuɗaɗen da za su iya cirewa.

Daloli da yuro sun fara yin ƙaranci cikin awanni biyu da yin kutsen. Tun daga sannan, waɗannan kuɗaɗe kaɗan kawai ake samu kuma an ƙayyade yawan rouble ɗin da mutum ke iya cirewa.

Evgeny (wanda aka sauya sunansa) mai shekara 45 wanda muka isko a tsaye a kan layi a Moscow, ya ce yana son cire kuɗi ne don biyan bashin gidansa.

"Duk wanda na sani na cikin ƙaguwa. Kowa a galabaice yake. Babu shakka rayuwa za ta ƙara tsanani. Yaƙi bala'i ne.

"Ina jin dukkan ƙasashen sun zama bakin ganga kuma a yanzu manyan ƙasashe na auna ƙarfin kowacce, don su ga wacce ce ta fi ɗan sauƙi-sauƙi. Amma kowa na jin jiki."

Marat ami shekara 35 ya ce: "Yau ce rana ta farko da na yanke shawarar cire kuɗi, kuma ban gamu da wani cikas ba. Na cire rouble ne ko da wani abu zai faru.

"Ban ƙware wajen hasashe ba amma ina zaton rayuwarmu za ta ƙara rincaɓewa. Lokaci ne kawai zai nuna hakan."

Ba a Moscow kawai ake fama da matsalar rashin kuɗaɗe laƙadan ba: ko a garuruwan Perm da Kostroma da Belgorod da ma sauran manyan biranen Rasha mutane na ta rububin cire daloli da yuro, kamar yadda rahotannin BBC suka nuna.

Wani ƙwararre a harkar fasaha da aka ɓoye sunansa har wata fasaha ya ƙirƙira a Tekegram da ke neman jin ko akwai yuro da daloli a ATM na bankin Tinkoff, wani banki mai zaman kansa, kuma idan akwai ɗin, sai ya aika wa mutanen da suke amfani da shafin adireshin.

Mutane da dama sun yi ta ƙoƙarin samun kuɗaɗe laƙadan ta hanyar amfani da manhajojin bankinsu.

A ranar Lahadi da yamma, a lokacin da aka sanar da takunkuman da aka sanya wa bakunan Rasha, har a lokacin za ka iya amfani da wata manhaja don neman dala har ta rouble 140, da kuma yuro har na rouble 150.

Amma zuwa ranar Litinin, abokan hulɗa a banki mafi girma na Rasha Sberbank, sun shaida wa sashen BBC Rasha cewa sun kasa buƙatar kuɗi ta manhaja kwata-kwata - dole sai da suka je ofishin don cike fom don yin hakan.

Bankunann sun ƙaryata cewa akwai ƙarancin kuɗi - kuma ƙwararru sun yarda cewa rashin kuɗaɗe a ATM na nuna ƙoƙarin hana ƙarewar kuɗi a bankunan ne.

Fadar Kremlin ta ce dama Rasha ta tsammaci wadannan takunkuman kuma ta shirya musu, duk da cewa dai ba ta bayyana ko za a taimaka wa ƴan kasuwa ba, kamar yadda aka yi a lokacin annobar cutar korona.

Amma Rashawa, waɗanda da yawansu kan samu bayanai ne daga gidan talabijin na ƙasar inda aka yi ta maimaita matsayar gwamnatin, suna sa ran za su fara ganin bambani a rayuwarsu nan ba da daɗewa ba.

Tuni dai mazauna a Moscow sun ba da rahotannin cewa ana samun layuka a kantunan sayar da abinci a yayin da mutane ke ta sayen abubuwan da suke tunanin za a iya rasa su ko kuma farashinsu ya ƙaru ko takunkuman kasuwanci ya shafe su.

Kamfanonin Rasha ka iya rage awannin samar da abubuwa a yayin da takunkuman ke ci gaba da aiki. Sannan ganin yadda kuɗaɗen ajiyarsu ke rage daraja, Rashawa da dama na hasashen za su rasa ayyukansu musamman ganin yadda tattalin arzikin ke shan kashi sakamakon cire shi daga tsarin hada-hadar kasuwanci da Ƙasashen Yamma suka yi.

Ga Rashawa, wannan zai dawo musu da abubuwan da suka faru a baya a lokacin da Shugaba Putin ya mamaye Crimea a shekarar 2014 inda mutane suka dinga bin dogwayen layuka don cirar kuɗaɗe.

A wancan lokacin ana sayar da dala ɗaya a kan rouble 30 zuwa 35 - wanda a yanzu ya nunka haka.

Karin masu rahoto, Amalia Zatari, BBC Russia a Moscow