Rikicin Ukraine: Halin da 'yan Najeriya suka shiga a Ukraine da Rasha

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta kwashe duk wani ɗan ƙasarta da ke Ukraine kuma ke burin barin kasar sakamakon tashin hankalin da ake ciki a kasar.

Sanarwar gwamnatin na zuwa ne yayin da zaman zullumi ke karuwa kuma mutane na neman mafaka saboda hare-haren Rasha bayan mamayar da ta yi wa Ukraine.

Ita ma majalisar wakilan Najeriya ta ce za ta yi aiki tare da ma'aikatar harkokin wajen, wurin dawo da 'yan Najeriyar da ke wadannan kasashe biyu gida.

Jama'a da dama sun shiga a birnin Belgorod na kasar Rasha wanda ke kusa da kan iyakar kasar Rasha da Ukraine.

An shiga halin zullumi saboda karar harbe-harbe rokoki da Rasha ke harbawa zuwa kasar Ukraine babu kakkautawa

Ana kuma iya ganin yadda mutane suka kauracewa tittunan birnin saboda fargabar abubuwan da ka iya faruwa.

Mun ji ta bakin wasu 'yan Najeriya da dama mazauna can kan halin da suka samu kansu a ciki.

Wasu daga cikinsu ta waya muka yi magana wasu kuma sun aiko mana sakonni ta imel bayan da muka bukaci hakan.

Dalibi ɗan Najeriya daga Rasha

Sadiq Shehu Masala wani dalibi ne ɗan Najeriya da ya shafe shekaru goma yana karatu a Jami'ar jihar Belgorod a kasar ta Rasha, kuma a hirarsa da BBC ya bayyana cewa da misalin karfe biyar na safiyar Alhamis agogon Moscow suka fara jin kara mai karfin gaske da ta tayar da hankulansu.

''Makamin roka ne da ake harbawa zuwa Ukraine da yake daga nan birnin da nake ciki (Belgorod) yana kusa da kan iyakar Ukraine, suna ta wucewa babu kakkautawa sai ka ce ana soya gurguru lokacin yana fashewa,'' in ji dalibi Sadiq.

Ya kuma kara da cewa rokokin na ta wucewa da karfi sosai ta yadda ko mutum barci yake dole sai ya tashi saboda karfin karar.

''Gaskiya ba mu iya samu mun runtsa ba, saboda tsoro ba mu san abin da ka iya biyo baya ba saboda kamar yadda na fada muna kusa da Ukraine din.''

Ɗalibi Sadiq ya kuma bayyana cewa 'yan kasar Rasha ko kadan ba sa wani jin tsoro, don haka suna ma ci gaba da harkokinsu.

Sai dai ya shaida cewa akwai 'yan gudun hijira da suka kwararo daga Ukraine zuwa cikin birnin na Belgorod da aka sama musu da wurin zama.

"Akwai makarantu da aka rufe, sannan jiragen sama ne kawai suke ta shawagi tare da ruwan harsasai a saman birnin na Belgorod, mun wayi gari an shiga wani yanayi na yaƙi.

Mutane a birnin na Belgorod kowa na cikin gida saboda fargaba, babu kowa a kan titunan birnin sai jiragen yaƙi ne kawai da sojoji, kuma kana an rufe filin sukar jiragen sama na birnin," in ji ɗalibin.

'Mutanen Rasha na nuna goyon bayansu'

Yayin da Rasha ke biris da kiraye-kirayen rungumar sulhu da zafafa farmaki a Ukraine 'yan kasarta na nuna goyon bayansu da matakin shugaba Vladimir Putin, kuma Malam Sadiq Shehu ya tabbatar wa da BBC hakan.

Ya shaida yada samari suka fito tittuna suna daga tutar Rasha da nuna mubaya'a.

''Gaskiya 'yan kasar na nuna goyon bayansu sosai, saboda a lokacin da ake harba wadannan rokokin zuwa Ukraine samari ne ke fitowa kan titi suna daga tutar Rasha don nuna jindadinsu.

''Mutane ne da suke nuna goyon baya ga shugaba Putin sosai, kuma sun san wannna faɗan da ake yi, kamar yadda ya faɗa musu, yana yi ne saboda 'yan kasar ba wai don wani abu ba.''

A cewar dalibin, yanzu haka idan faɗan ya ci gaba zai koma birnin Moscow da zama saboda yana da nisa sosai daga ƙasar Ukraine.

Birnin Kyiv Ukraine

Mutane na ci gaba da tserewa daga Kyiv babban birnin kasar Ukraine, kuma ana ta ganin gidajen mai cike da mutane don su samu man da za su fice daga garin saboda fargaba.

Wani dalibi ɗan Najeriya Muhammad Kabir da ke zaune a can ya shaida wa BBC halin da suka shiga da cewa, yanzu haka hankulan mutane a tashe yake saboda rikicin.

"Gaskiya mun wayi gari cikin tashin hankali da fargaba, kowa hankalinsa ba a kwance yake ba, mutane daga baki har 'yan kasar ana ta barin garin," in ji Muhammad.

Ya kuma shaida yada suka rinka jin karar fashewa har sau uku wanda ya ce da fari sun yi tunanin ma wasan wuta ake yi.

''Da farko mun yi tsammani wasan wuta ne, da yake an saba harbawa, to sai muka sake ji, daga nan ne kowa ya tashi sai muka bude tagogi muka ga kowa ya fito waje ba lokacin da ka saba tashi ba."

Kuma a cewarsa akwai mutane da dama a kan dogayen layukan manyan shaguna don samu su sayi kayan abinci da yawa saboda abubuwan da ka iya faruwa da zai hana su fita waje.

''Ko da yake ina da kayan abinci, amma sai da nima na shiga shaguna na kara," a cewar ɗalibin.

'Yan kasar Ukraine na nuna matukar rashin jin dadinsu a kan abubuwan da ke faruwa kamar yadda dalibin ya shaida wa BBC.

''Suna cewa an zalunce su, an kwace musu wurare biyu da Donesk da Luhansk, kowa ba ya jin dadi, da ka duba fuskokinsu za ka ga kowa da jakarshi cikin shirin ko-ta-kwana."

Ya kuma ce sun tuntubi ofishin huddar jakadancin Najeriya a kasar ta Ukraine sun ce za su yi magana da su.

''Amma yanzu haka ni da abokaina mun riga mun sha mai akwai wani gari Libib, gaskiya da mun samu hanya za mu wuce saboda tana kusa da kan iyaka".

Sakonnin mutane da suka aiko wa BBC

  • Sunana Yahya Rabi'u akwai kanwata mai suna Fadila Rabi'u nakira wayarta ba ta shiga
  • Sadiq Musa Abdullahi: Abokina saleem Ahmad wanda ke karatu a birnin kviv ya bayyana mun cewa ya zuwa yanzu an tsananta tsaro a cikin birnin na kyiv ya kuma ce an sa dokar hana fita
  • Ahmed musa: Gaskiya muna cikin wani Hali mara kyau ku taya mu da addu'a Dan Allah
  • Sadiq Ado: Slm sunana Sadiq Ado Ina karatu ne anan, amma yanzu sakamakon firgita da tsoro da muke ciki a yanzu Inaso na dawo gida
  • Wallahi yanzu haka muna cikin fargaba Muttaka, Almustapha

Abin da ofishin huldar jakadancin Najeriya a Rasha ke cewa

Ofishin jakadancin Najeriya a ƙasar Rasha ya buƙaci 'yan ƙasar mazauna can su fiye da dubu ashirin da biyar (25,000) da su yi taka-tsantsan yayin da ya ke ci gaba da nazarin halin da ake ciki a wannan rikici.

Jakadan Najeriya a Rasha, Ambasada Abdullahi Shehu Yibaikwal ya shaida wa Ishaq Khalid na BBC cewa ko da yake ana zaman zullumi to amma lamarin bai yi munin rahotannin da wasu kafofin labarai ke nunawa ba. Ga yadda hirar ta kasance:

Ambasada: "Akwai fargaba, an ji wasu harbe-harbe a tsakanin kasar Rasha da Ukraine. Mu kuma 'yan Najeriya, mu muna Moscow abun ya faru daga bakin safiyar yau (Alhamis).

"Mun tashi a cikin yanayi na dar-dar amma mu yi ɗan hakuri kaɗan zuwa gobe ko jibi zamu fi fahimtar abun da ake ciki".

Tambaya - 'Yan Najeriya da ke nan Rasha, wani hali su ke ciki?

Ambasada: "Ala kulli halin, mu muna zaune lafiya, akwai dar-dar din amma babu wani tashi hankalin da za a ce a'a ai abu ta faru a gudu. Kuma ko yaki aka fara din ba mataki mai kyau ba ne kawai ka fara gudu, idan abu ya faru ba ka san in da yakin zai fito ba.

"Hali ne da ake ciki wanda muna gargadin mutane su kwantar da hankali mu fahimce abun da ake ciki.

"In ta kai wadda za mu bada shawara wa gwamnatin ga matakin da za ta dauka, dalilin da mu ke a nan din kenan don ba da shawara ga gwamnati da halin da ake ciki.

"Amma a halin da ake ciki a yau zan tabbatar maka duk da dar-dar da ake ciki din muna cikin hakuri kuma ba mu samu wani rahoto kan wani dan Najeriya ya shiga wani halin da ba mu iya taimaka masa ba, babu.

"Muna nan duk 'yan kwamitin muna jin in da suke muna waya, mu ji ya ya ku ke? kuna lafia? su ce muna nan lafiya.

Daliban mu da su ke garurukan da ke iyaka da Ukraine fa?

Ambasada: "Eh su ma su na cikin lafiya amma akwai fargaba da su ka ji harbe harben nan da safe. Toh amma suna zuwa cikin ajujuwansu su yi karatu, amma dar-dar din ne dai.

"Na ce to dar-dar din kawai a yi hakuri a lura kawai a kiyaye inda bai kamata a fita dole ba sai a dan kiyaye don mu ga abunda halin ke ciki nan da kwana biyu.

Kamar akwai yiwuwa idan abun ya ƙazanta a ce za a kwashe 'yan Najeriya, musamman dalibai daga kasar Rasha misali?

Ambasada: "Ya danganta ga irin abunda mu ka gani kuma mu ka bada shawara ga gwamnati, duk abunda muka ba da shawara ga gwamnati za ta yi amfani da shi.

Toh kamar a can tsallake cikin Ukraine, in da nanne ake batun wannan rikici yake faruwa, wane bayani kuke samu game da halin da 'yan Najeriya ke ciki?

Ambasada: "Eh toh ni hurumi na ya kare a nan Rasha, akwai mu da ambassador a Ukraine.

Amma kuna tattaunawa da su ai, kuna jin halin da ake ciki?

Ambasada:Muna tattaunawa, muna tattaunawa.

Wannan rikici ne da kasashen duniya daban daban suke tofa albarkacin bakinsu da bayyana matsayinsu.

Menene matsayin Najeriya kan wannan rikicin Rasha da na Ukraine?

Ambasada: "To ai matsayin Najeriya, kai ka fi kusa da inda fadar Najeriya take...

Amma kai kake wakiltar Najeriya a Rasha kuma tushen wannar al'amari?

Ambasada: "Amma ai matsayin Najeriya sai a Abuja ake dauka kafin aka tura mana ai, ko ba haka ba?

Ni dai zan gaya musu abin da ke nan a kasa ne, su kuma sai su dauki mataki su ce ga matsayin Najeriya.

Ka tuntubi ma'aikatan harkokin waje ko fadar shugaban kasa, mai yuyuwa akwai wata matakin da aka dauka amma ba a gaya min komai ba".