Alkalai mata da ke jagorantar shari'a a Kotun Kolin Najeriya

A makon jiya ne aka tabbatar da Mai Shari'a Ketanji Brown Jackson a matsayin bakar-fata mace ta farko da ta zama alkaliyar Kotun Kolin Amurka.
Wannan shi ne karon farko da bakar-fata za ta shiga sahun alkalan Kotun Kolin kasar a tarihinta na shekara 233.
Shugaba Joe Biden ne ya mika sunanta ga Majalisar Dattawa domin amincewa da ita a wannan mukami mai matukar muhimmanci bayan ya yi alkawarin yin hakan a lokacin yakin neman zabensa.
Ms Jackson, mai shekara 51, za ta maye gurbin Mai Shari'a Stephen Breyer a Kotun.
Ana kallon ta a matsayin kwararriya a fannin shari'a, kodayake wasu na zargin ta da kasancewa "mai sasauci" a kan masu aikata laifuka.
Najeriya ma na daga cikin kasashe masu tasowa da mata suka yi fice a bangaren shari'a, inda suka kai matakai da matsayi daban-daban a manyan kotunan kasar, ciki har da Kotun Koli.
Mun binciko muku wasu daga cikin irin wadannan mata da suka taka muhimmiyar rawa a kotuna daban-daban inda har suka kai Kotun Koli:
1. Amina Adamu Augie

Asalin hoton, Supreme Court of Nigeria
An haifi Mai Shari'a Amina Adamu Augie a ranar 3 ga watan Satumban 1953. 'Yar asalin jihar Kebbi ce da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ta kuma fara karatu a makamarantar firamare ta Abadina, a Jami'ar Kwalejin Ibadan daga shekarar 1958 zuwa 1960, da makarantar firamare ta Hope Waddell da ke birnin Calabar daga shekarar 1960 zuwa 1962, sai makarantar firamare ta Holy Rosary da ke Enugu daga shekarar 1966 zuwa 1967, da Kwalejin Queen Amina ta Kaduna daga 1968 zuwa 1971.
Daga nan ne ta tafi Jami'ar Ife, Ile-Ife daga shekarar 1972 zuwa 1977.
Ta kuma halarci makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya da ke Lagos daga shekarar 1977 -zuwa 1978. Ta kuma yi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria daga shekarar 1980 zuwa 1981, sai kuma Jami'ar Jihar Lagos daga shekarar 1986 zuwa 1987. A ranar 8 ga watan Yulin shekarar 1978 ne kuma ta zama cikakkiyar lauyar Najeriya.
Mai Shari'a Amina A. Augie ta fara aikinta na lauya a matsayin lauya Jihar Sokoto lokacin da take aikin yi wa kasa hidima daga shekarar 1978 zuwa 1979. Daga shekarar 1980 -zuwa 1982, ta yi aikin wucin-gadi a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria a matsayin mataimakiyar mai koyarwa.
Daga shekarar 1982 zuwa 1984, ta yi aiki a matsayin babbar lauya a ofishin shugaban kasa a wancan lokacin Alhaji Shehu Shagari, wanda bayan nan ne ta samu aiki a matsayin mai koyarwa a Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Najeriya da ke Lagos.
A shekarar 1988, Amina Adamu Augie ta samu mukamin Babbar Alkalin Majistare a Ma'aikatar Shari'a ta jihar Sokoto.
Ta kuma yi aikin koyarwa na wucin-gadi a sashen koyon aikin lauya a Jami'ar Usuman Danfodio Sokoto daga shekarar 1989 zuwa 1992.
Mai Shari'a Augie ta samu cigaba zuwa Kotun Daukaka Kara a shekarar 2002, inda ta yi aiki a matakai daban-daban na Kotun a rassan da ke wasu jihohin.
Amina Adamu Augie ta samu karin girma zuwa Mai Shari'a a Kotun Kolin Najeriya ranar 7 ga watan Nuwambar 2016.
Mai Shari'a Augie na da 'ya'ya hudu.
2. Mary Ukaego Peter-Odili

Asalin hoton, Kotun Kolin Najeriya
An haifi Mai Shari'a Mary Ukaego Odili da ake yi wa lakabi da Nzenwa a ranar 12 ga watan Mayun shekarar 1952 a garin Amudi Obizi, Ezinihitte - Karamar Hukumar Mbaise ta Jihar Imo.
Ta yi karatu a makarantun firamare da dama da suka hada da St Benedict's, da Obizi Ezinihitte, da St Michael's , da Umuahia, da St Agnes, da Maryland a Lagos da kuma Our Lady of Apostles Primary School, Yaba da ke jihar Lagos tsakanin shekarar 1959 da1965.
Ta kuma yi karatu a makarantun sakandare da dama da suka hada da Our Lady of Apostles da ke Yaba a jihar Lagos, da makarantar sakandaren 'yan mata ta Owerri, da makarantar 'yan mata ta Mbaise Jihar Imo da kuma Kwalejin Queen of the Rosary College da ke garin Onitsha tsakanin shekarar 1965 da 1972.
Daga nan ta ci gaba zuwa Jami'ar Najeriya ta Nsukka (jihar Enugu) inda ta kammala karatun Digirin Farko a fannin Shari'a a shekarar 1976. Ta kuma yi karatu a Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Najeriya a shekarar 1977.
Ta kuma rike mukamai da matsayi a Ma'aikatar Shari'a ta Abeokuta, jihar Ogun daga shekarar 1977 zuwa 1978, da Ma'aikatar Shari'a ta birnin Benin, jihar Bendel, a shekarar 1978, da Kotun Majistare mataki na 3 a garin Benin, Jihar Bendel daga shekarar 1978 zuwa 1979.
Haka kuma ta rike mukamin shugabar Kotun Matasa a garin na Benin daga shekarar 1978 zuwa 1979, sai kuma jihar Rivers daga shekarar 1979 zuwa 1981, har ya zuwa mukamin Alkali a Kotun Daukaka kara reshen Abuja daga shekarar 2004 zuwa 2010 da kuma Mai Shari'a a Kotun Daukaka Kara reshen jihar Kaduna daga shekarar 2010 zuwa 2011.
An nada Mai Shari'a Mary Ukaego Peter Odili a matsayin Alkaliyar Kotun Kolin Najeriya a ranar 23 ga watan Yunin shekarar 2011.
Tana da aure da kuma 'ya'ya.
3. Uwani Musa Abba Aji

Asalin hoton, Supreme Court of Nigeria
An haifi Mai Shari'a Uwani Musa Abba Aji a ranar 7 ga watan Nuwambar shekarar 1956 a garin Gashua, jihar Yobe, arewa maso gabashin Najeriya. Ta kuma fara karatu a makarantar firamare da ke garin Gashua da Makarantar Sakandaren 'Yan mata ta Maiduguri daga tsakanin shekarar 1961 da 1972. Ta kammala karatun Difloma a fannin Shari'a daga Jami'ar Ahmadun Bello ta Zaria a shekarar 1976 da kuma Digirin Farko a fannin Lauya a jami'ar a shekarar 1980.
A shekarar 1981 ne ta zama Cikakkiyar Lauyar Najeriya, kuma ta fara aikinta na Lauya a shekarar 1982.Ta kuma rike mukamai da dama da suka hada da Mataimakiyar Rajitara, mukuaddashin rajitara, da babbar rajistara a tsakanin shekarar 1973 da 1982.
Bayan nada ta mukamin lauya mai bai wa gwamnatin shawara a shekarar 1982, ta samu karin girma zuwa wasu matakan matsayi inda ta zama Mukaddashin Babban Lauya a shekarar 1984, sai Majistare mai mataki na biyu a shekarar 1986, da Babbar Majistire shekarar 1987, Babbanr Majistire mataki na daya da kuma Babbar Rajistara a shekarar 1991.
An kuma nada ta Babbar Alkalin Kotu a Ma'aikatar Shari'a ta jihar Yobe a watan Disambar shekarar 199, da ya sa ta zama mace alkali ta farko a ma'aikatar, matsayin da ta rike har ya zuwa shekarar 2004 lokacin da aka yi mata karin matsayi zuwa Kotun Daukaka Kara.
A cikin 'yan shekaru, Mai Shari'a Uwani ta kasance Sakatariyar Kungiyar Alkalan Kotun Majistare ta Najeriya reshen jihar Borno; Shugabar Kwamitin Bincike kan Tayar Da Zaune Tsaye a garin Potiskum; Shugabar Kwamitin Bincike a Damaturu da Potisku jihar Yobe; Shugabar Kungiyar Mata Musulmai ta Najeriya Amairah, (FOMWAN); Shugabar Kungiyar Mata Alkalai ta Najeriya (NAWJN), National Legal Adviser of FOMWAN and Chairperson, Kwamitin Kyautata Jin Dadin Alkalan Kotun Daukaka Kara.
Ta kuma yi aiki a kotunan shari'ar da ta shafi kararrakin zabe da dama baya ga kasancewa alkalin koton hukunta masu aikita laifukan cin hanci da rashawa ICPC a tsakanin shekarar 2001 da 2014.
Kafin ta kara zamun cigaba zuwa Kotun Kolu a ranar 8 ga watan Janairun shekarar 2019, Mai Shari'a Uwani ta kasance Alkali mai jagorantar Korun Daukaka reshen jihar Kaduna, matsayin da ta rike har na tsawon shekaru hudu.
Tana da aure da kuma 'yaya uku.
Kana mai sha'awar karance-karance, da rubuce-rubuce da aikin lambu ce. Ta kuma yi tafiye-tafiye zuwa kasashe da nahiyoyi da dama a duniya.
4. Kudirat Motonmori Olatokunbo Kekere-Ekun

Asalin hoton, Supreme Court of Nigeria
An haifi Mai Shari'a Kudirat Motonmori Olatokunbo da ake yi wa lakabi da Kekere-Ekun a ranar 7 ga watan Mayun shekarar 1958.
Ta kammala karatun Digirin Farko a Fannin Lauya a shekarar 1980 daga Jami'ar jihar Lagos da kuma Digiri na Biyu a fannin Lauyan a Jami'ar Harkokin Tattalin Arziki da Kimiyyar Siyasa ta birnin London a watan Nuwambar 1983.
Haka nan a ranar 10 ga watan Yulin 1981, ta zama cikakkiyar lauya a Najeriya.
An kuma nada ta a matsayin Babbar Majistare mai mataki na 2 a Ma'aikatar Shari'a ta jihar Lagos a watan Disamban 1989.
A watan Yulin 1996 ne aka nada ta Alkaliyar Babbar Kotun jihar Lagos.
Ta kuma rike matsayin shugabar kotun hukunta 'yan fashi da masu rike da makamai, Zone II, Ikeja, Legas daga Nuwamban 1996 zuwa Mayun 1999.
An yi mata karin girma a matsayin Alkalin Kotun Daukaka Kara a ranar 22 fa watan Satumbar shekarar 2004.
Ta kuma yi aiki a matsayin mamba a Kwanitin ICT na Kotun Daukaka Kara daga watan Yunin shekarar 2011 zuwa Yulin 2013.
Ta kuma halarci kwasa-kwasai da tarukan bita a ciki da wajen Najeriya da suka hada da Hadaddiyar Daular Larabawa da Birtaniya.
An kuma nada ta a matsayin Alkalin Kotun Kolin Najeriya a ranar 8 ga watan Yunin shekarar 2013.
Da gabatar da kasidu a taruka da dama na kara wa juna sani, da bita, da horar da akalan kotun majistire da sauran alkalai.
Kana mamba ce a kungiyoyin lauyoyi, kuma ta samu kyautukan lambobin yabo da dama.
Tana da sha'awar karance-karance, da jin wakoki da harkar fasahar zamani da kuma yin nasiha da kwantar da hankalin.
Tana da aure da kuma 'ya'ya.

Tsohuwar Mai Shari'a Zainab Adamu Bulkachuwa
Duk da cewa ta yi ritaya, Mai Shari'a Zainab Adamu Bulkachuwa, ita ce mace ta farko da ta shugabanci Kotun Daukaka Kara a kasar, kuma ta sahida wa BBC cewa ba ta taba yanke hukuncin kisa ba a tsawon wadannan shekaru.
Kafin rike wannan matsayi, ta yi aiki a bangarorin shari'a daban-daban tare da rike mukamai da dama a jihohi da ma gwamnatin tarayya.
Sai dai a lokacin da ta cika shekara 70 a duniya ranar 6 ga watan Maris din 2020, a wannan lokacin ne kuma ta ajiye aiki, amma kamar yadda aka sani, tafiya irin wannan na cike da dumbin nasarori da kalubale.
A wata hira ta musamman da Sashen Hausa na BBC kwanaki kadan kafin ritayar tata, Mai Shari'a Bulkachuwa ta bayyana mana irin matakan da ta hau masu dadi da masu tsauri, tare da fadin abin da za ta sa a gaba bayan ajiye aiki.












