'Babu sisin wani maniyyaci a hannunmu'

Ka'aba

A Najeriya, Hukumar Alhazai ta kasar ta ce ba ta rike ko da sisin kwabon wani maniyyaci a hannunta a karkashin shirin nan na adashin gata da maniyyata ke yi.

A cewar hukumar dukkan kudaden da maniyyata ke biya yana shiga asusunsu da ke bankin Ja`iz, don haka babu dalilin fargabar kwabonsu zai yi ciwon kai.

Kwamishinan ma'aikata da kudi a hukumar, Alhaji Nura Hassan, ya shaida wa BBC cewa, akwai bambanci tsakanin shirin adashin gata da kuma shirin da ake tuntuni wanda maniyyata ke biyan kudin aikin Hajjin su a hukumomin aikin Hajji na jihohinsu.

Ya ce, su wadanda suka biya kudinsu ta hannun hukumomin alhazai na jihohi, to kudinsu na nan a hannun hukumomin da suka biya kudin, don haka duk wani karin bayani da suke nema sai su je can.

Alhaji Nura Hassan, na mai da martani ne ga wani zargi da majalisar wakilan Najeriyarta yi cewa hukumar na karbar kudaden maniyyata tun a shekara ta 2020 zuwa yanzu, ga shi ba ayi aikin hajji ba a tsakani.

Ya ce," Babu kwabon wani alhaji ta hannun hukumar alhazai ta jiha a hannun hukumar alhazai ta kasa."

Kwamishinan ma'aikata da kudi a hukumar alhazai ta kasar ya ce, ya kamata mutane su sani, shirin adashin gata da aka bullo da shi ga maniyyata aikin hajj, shima ba hukumar alhazai ta kasa ce ke ajiye kudinba.

Ya ce, " Shiri ne wanda muka yi shi tsakaninmu hukumar alhazai ta kasa da ta jihohi da kuma bankin Ja'iz, don haka kudin suna wajen bankin Ja'iz."

Alhaji Nura Hassan, kowanne maniyyaci da ya bude asusu a Ja'iz, to kudinsu yana nan a bankin, kuma zai iya ganin komai.

Jami'in hukumar alhazan ta Najeriya, ya ce wadanda suke cikin tsarin adashin gata idan lokacin aikin hajj ya zo, aka fadi cikon da za ayi suka cika, to sune za a bawa fifiko wajen tafiya aikin Hajj.

Karin bayani

Majalisar wakilan Najeriya ce ta ba da umarnin gudanar da bincike a kan shirin adashin gata na maniyyata aikin hajji da hukumar alhazai ta NAHCON ke gudanarwa.

Matakin ya zo ne bayan gabatar da bukatar gaggawa a gaban zauren majalisar kan zargin cewa ɗaruruwan 'yan ƙasar sun biya kuɗin aikin Hajji tun a shekarar 2020, amma har yanzu ba su san matsayinsu ba.