Yadda cutar korona ta sauya tsarin da ake bi wajen gudanar da ayyukan Umrah

Ka'aba

Asalin hoton, HARAMAIN SHARIFAIN

    • Marubuci, Fauziyya Kabir Tukur
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Annobar cutar korona ta kawo sauye-sauye da dama a fannoni daban-daban na rayuwa tun bayan ɓullar ta fiye da shekara guda da ta wuce.

A iya cewa ta sauya yadda ake gudanar da al'amura na yau da kullum - kama daga tafiye-tafiye da gudanar da ayyukan ofis da taruka da karatu da dai sauransu.

Ba a bar ayyukan ibada a baya ba, domin kuwa annobar ta sauya yadda ake gudanar da sallah a masallatai a faɗin duniya musamman a lokacin da take kan ganiyarta.

Sai da ta kai an daina yin sallar jam'i a masallatai, kuma da aka koma yin sallah a masallaci, sai aka daina haɗa sahu. Wannan kuwa har a manyan masallatai na Makka da Madina waɗanda a wata gaɓa sai da aka rufe su kuma aka daina yin sallah a cikinsu.

Baya ga sallah, sauran nau'ikan ibada kamar ɗawafi ma duk an dakatar da yin su a wancan lokaci.

A yanzu da aka sassauta dokokin cutar korona dangane da taruwa a wuri guda, hukumomin masallacin na Ka'aba sun ƙirƙiro sabbin hanyoyin gudanar da ayyukan ibada da suke ganin za su taƙaita yaɗuwar cutar a tsakankanin masu ibada.

Ga wasu daga sauye-sauyen da aka samar don gudanar da ayyukan Umrah a Saudiyya:

Manhajar da ke ba da damar shiga masallaci a yi sallah

A ƙarshen shekarar da ta gabata ne ma'aikatar Hajji da Umrah a Saudiyya ta sanar da samar da wata manhaja da za ta bai wa maniyyata damar yin sallah a masallacin Ka'aba da shiga Raudha, wato kabarin Annabi (SAW) a masallacin Madina.

Ana amfani da manhajoji guda biyu masu suna Eatmarna da Tawakkalna wurin tanadin gurbin yin sallah a masallatan da kuma shiga Raudha.

Ana sauke manhajojin ne a kan wayoyin hannu kuma hukumomi sun ce suna taimaka wa maniyyata tsara aikin Umrarsu a yayin da annobar korona ke ci gaba da yaɗuwa.

Ana tsara yadda za a yi ziyara da salloli a masallatan biyu na Makka da Madina, dangane da yawan mutanen da hukumomi suka amince da su, inda za a tabbatar kowa na cikin tsaro da kiyaye dokokin cutar ta korona.

Haka kuma manhajar Tawakkalna na bai wa mai amfani da ita damar sani idan ya yi mu'amala da wani mai ɗauke da cutar.

Sannan ana amfani da manhajar Tawakkalna a wurin shiga otal da shaguna.

Kafin mutum ya shiga dole sai manhajar ta tabbatar wa mahukunta cewa ba ya ɗauke da cutar korona kuma bai yi mu'amala da mai cutar ko wanda ya ke da haɗarin cutar ba.

Manhajojin na bai wa hukumomin masallaci ƙayyade iyakar mutanen da za a ba damar yin sallah a dai-dai wani lokaci.

Ka'aba

Asalin hoton, HARAMAIN SHARIFAIN

Yin sallah a masallaci da ɗawafi da safa da marwa

Ba kamar yadda aka saba ba, yanzu a masallatan Makka da Madina an kwashe duka Ƙur'anai da aka ajiye a cikinsu, sai dai mutum ya yi karatu daga wayarsa ko kuma ya shiga da Ƙur'aninsa, kamar yadda wani wanda ya yi aikin Umrah kwanan nan ya shaida wa BBC.

"Haka ma ruwan zamzam, babu manyan randunan nan da aka saba ajiyewa da maniyyata ke iya ɗiban ruwan su sha a duk lokacin da suka so. Yanzu ma'aikatan masallaci ne ke rabawa mutane ruwan a ƴar roba wadda da mutum ya sha sai ya jefa ta a shara," a cewarsa.

Ruwan ZAMZAM a kwalba

Asalin hoton, HARAMAIN SHARIFAIN

Bayanan hoto, Yanzu ma'aikatan masallaci ne ke rabawa mutane a a ƴar roba wadda da mutum ya sha sai ya sa ta shara

Haka kuma, a lokacin ɗawafi, akwai jami'an masallaci da ke sa ido domin tabbatar da cewa maniyyata sun bar tazara a tsakaninsu.

"Yanzu an hana yin sallah a Hijri Isma'il ko a bayan Muƙama Ibrahim kamar yadda aka sani, sai dai mutum ya bar harabar da ake yin ɗawafi ya yi sallarsa," a cewar mutumin.

Ya ce yanzu masu sanye da Ihrami wato masu yin Umrah ne kawai ake bari su shiga filin ɗawafi, amma su ma ba a bari su je kusa da Ka'aba.

Don haka babu taɓa Ka'aba da Hajrul Aswad da tsayuwa a ƙarƙashin indararon rahama.

Ya ce an kewaye Ka'aba da wasu robobi da za su hana mutane wucewa su je kusa da ita.

Haka ma a wurin Safa da Marwa, an samu sauyi sosai musamman yadda ake ɗaukar tsoffi da masu naƙasa a kujerar marasa lafiya.

Yanzu babu mutane masu tura su a kujerar ta marasa lafiya, sai dai an samar da wasu kujeru masu aiki da kansu waɗanda tsoho ko mai larurar nakasa zai iya hawa kujerar ta tuƙa kanta.

Barin tazara da sanya takunkumi

Baya ga killace kai da maniyyaci zai yi tsawon kwana biyu bayan ya isa Saudiyya kafin ya fara shiga masallaci, ana buƙatar ya zama kullum yana sanye da takunkumi.

Wani maniyyace ya bayyana mana cewa da ya je Umrah a watan Fabrairu, ya fahimci muhimmancin amfani da takunkumi a ko yaushe a cikin masallaci.

"Na sauke takunkumina a lokacin da nake sallah don in ɗan sha iska kawai sai askarawa suka zo suka tsaya a bayana. Ban san dalili ba sai da wani ɗan Najeriya da ke kusa da ni ya gaya min da Hausa cewa za su ci tara ta Riyal 1000 saboda sauke takunkumin da ka yi. Ya ce min kana idar da sallar nan za su kama ka," a cewarsa.

"Don haka sai na yi ta jawo surori masu tsawo na ƙi sallame sallar har sai da liman ya zo aka kabbara salla muka fara jam'i, a lokacin ne suka tafi suka ƙyale ni," ya faɗa yana dariya.

"Da na sallame sallar da karɓar fasfo ɗina za su yi, kuma su sa ni in biya tarara kuɗi," a cewarsa.

Masjidin Nabawi

Asalin hoton, HARAMAIN SHARIFAIN

Haka kuma, ko yaushe ana cikin tsaftace masallatai da sinadarai masu ƙarfi domin kashe ƙwayoyin cutar korona.

Kamar goge ƙasan masallacin da ƙofofinta sannan ana fesa magungunan kashe ƙwayoyin cuta.

Akwai ma'aikata da dama da aikinsu kenan kullum.

Masallata a Masallaci

Asalin hoton, HARAMAIN SHARIFAIN

Tun bayan ɓullar cutar hukumomi a Saudiyya suke ta lalubo hanyoyin ganin sun daƙile yaɗuwarta, musamman bayan da suka fara bayar da izinin shiga ga baƙi masu son yin Umrah.

Yanzu da aka fara bayar da allurar riga-kafin cutar a faɗin duniya, gwamnatin Saudiyya ta ce duk wanda zai shiga ƙasar sai yana da shaidar yin allurar sannan za a ba shi damar shiga.