Kiswah: Abubuwan da ya kamata ku sani game da yadda ake dinka rigar Dakin Ka'aba

Rigar Ka'aba

Asalin hoton, Reasahalharamain

Bayanan hoto, Ma'aikata kenan yayin da suke lulluɓa ɗakin Ka'aba sabuwar riga
    • Marubuci, Yusuf Yakasai
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Da safiyar ranar Arfa ne ake gagarumin aikin sauya rigar dakin Ka'aba a birnin Makka na kasar Saudiyya, wanda ake yi sau daya a kowace shekara, kodayake na wannan shekarar an sauya shi tun ranar Lahadi 8 ga Zul Hijjah.

Ana wannan aikin ne a lokacin da alhazai suka bar birnin Makka suke tsayuwar Arfa, wadda ita ce babban rukunin aikin Hajji.

Sabon abin da alhazai za su tarar idan suka koma Makka ranar Babbar Sallah shi ne sabuwar rigar Ka'aba.

Ana ɗaukar sauya wa Ka'aba riga a matsayin wani babban lamari na girmama ɗakin na Allah da kuma tsarkake shi.

Sauya rigar na daga abubuwa mafiya daɗewa a tarihin duniya.

An shafe ɗaruruwan shekaru ana sauya wa Ka'aba riga gabanin zuwan Musulunci, abin da wasu sarakunan Larabawa suka riƙe kuma ya zama wani babban abin alfahari a wajen Larabawa.

Rigar Ka'aba

Asalin hoton, Reasahalharamain

A yanzu kimanin ma'aikata 160 ne suke aikin sauya rigar ta Ka'aba a duk shekara.

Saka sabuwar riga ga kofar Ka'aba shi ne abin da ya fi komai wahala a wajen sauya rigar, kasancewar yadda ake ɗinka rigar kofar ya bambanta da sauran tufafin da ake sakawa a jikin bangon ɗakin.

Presentational grey line
Presentational grey line

Da me ake ɗinka rigar Ka'aba?

Rigar Ka'aba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda masaƙa ke saƙa rigar Ka'aba

Bayanai daga majiyoyi a Saudiyya sun nuna cewa ana dinka rigar ta Ka'aba da zaren siliki mai inganci, sai a rina shi zuwa baƙi.

Launin tufafin daga waje baƙi ne, daga ciki kuma kore ne. Sannan ana amfani da zarurrukan siliki da na gwal da azurfa wajen ɗinkin rigar.

Ana amfani da zallan zaren siliki da ya kai nauyin kilogiram 670, wanda ake kawo shi daga ƙasar Italiya.

Sai kuma zaren da aka cuɗanya shi da gwal mai nauyin kilogiram 120 da kuma zaren da aka cuɗanya da azurfa mai nauyin kilogiram 100 waɗanda ake kawo su daga Jamus.

Ana bin wasu tsauraran matakai na tabbatar da inganci da kuma ganin cewa an yi komai kadaran-kadahan.

Rigar ta Ka'aba ta kunshi ƙyallaye 47 da ake saƙa su daban-daban, sannan daga baya a haɗe su a dinke waje ɗaya. Tsawon kowane kyalle ɗaya ya kai mita 14, faɗinsa kuma ya kai santimita 101.

Ana yi wa rigar kwalliya da rubutun ayoyin Kur'ani, waɗanda ake amfani da zarurrukan gwal da na azurfa wajen rubuta su.

Ana kammala ɗinka rigar wata biyu gabanin fara aikin Hajji, kuma ana ƙwarya-ƙwaryar bikin kammala ɗinka ta kafin a miƙa ta ga hukumomin da ke kula da Masallatan Makka da Madina.

Daga nan kuma sai a miƙa rigar ga iyalan ƙabilar Bani Shaiba, waɗanda su ne Annabi Muhammadu SAW ya tabbatar wa haƙƙin kula da Ka'aba.

Tarihin samarwa ko ɗinka rigar Ka'aba

Rigar Ka'aba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai saɓani kan wanda ya fara rufa wa Ka'aba riga

Ka'aba wato ɗakin Allah, al'ummar Musulmai sun yi imainin cewa shi ne ɗaki ko wani gini na farko a wannan duniyar, gini ne da babu abin da ya kai shi tarihi a duniya. Hakan ta sa Larabawa suke matuƙar alfahari da ɗakin.

Wanda ya fara samar wa Ka'aba riga a Musulunci shi ne Annabi Muhammad SAW, inda ya tufatar da ɗakin da rigar da aka saƙa a Yamen.

Haka nan kuma, wasu halifofinsa da suka biyo bayansa sun ci gaba da samar wa Ka'aba riga duk shekara da tufafin da ake saƙawa a Yamen.

Amma an ce mutum na farko da ya fara samar wa da Ka'aba riga shi ne wani sarkin Yamen da ake cewa Tubba'u.

Ya ziyarci ɗakin shekaru da dama kafin zuwan Musulunci kuma tun daga nan ne ake samar wa Ka'aba riga.

Sai dai wasu bayanan na cewa mutum na farko da ya fara samar wa Ka'aba riga shi ne Adnan, wanda shi ne kakan Larabawa zuriyar Annabi Isma'il ɗan Annabi Ibrahim.

Amma tarihi ya nuna cewa mutum na farko da ya haɗa kan kan ƙabilun Larabawa wajen tufatar da Ka'aba shi ne 'Kusayyu ɗan Kilabu, kakan Manzon Allah SAW na huɗu.

Shi ne ya tsara wa Larabawa yadda za su dinga karo-karo wajen samar wa da Ka'aba riga.

Lamarin ya ci gaba a haka, har lokacin da aka yi wani shahararren attajiri a Makka mai suna Abu Rabi'a Abdullahi Al-Mukhzumi, wanda ya ce wa Kuraishawa zai dinga ɗaukar nauyin samar da rigar Ka'aba a shekara, wata shekarar kuma Kuraishawan su yi karo-karo su samar da ita.

To amma a zamanin daulolin Musulunci bayan Annabi Muhammad an ringa samun bambamce-bambance a lokutan da ake sanya wa Ka'aba tufafi, inda a wasu lokutan ake sauya rigar sau biyu, a wasu lokutan kuma sau uku.

Ƙasashen da suka samar da rigar Ka'aba

Rigar Ka'aba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun farko ana yin karo-karo wajen samar da rigar Ka'aba

Tun daga 1962, Saudiyya ce ke ɗaukar nauyin samar da rigar ta Ka'aba da duk wasu hidindimu da ake yi mata.

A zamanin mulkin daular Bani Umayya, ana ɗinka rigar ce a ƙasar Sham (Syria) sai a aika da ita Makka duk shekara.

Daga baya Masar ta ɗauki nauyin samar da rigar, abin da ta riƙa da cikakken alfahari.

A shekarar 1926 Sarki Abdulaziz wanda ya kafa daular Al Saud, ya bayar da umarnin kafa masana'antar rigar Ka'aba a birnin Alkahira na Masar.

A 1927, sarkin ya bayar da umarnin ware wani gida a kusa da Haramin Makka don saƙar rigar, kuma wannan shi ne karon farko da aka saƙa rigar a Saudiyya.

Masar ta dakatar da saƙa sabuwar rigar Ka'aba saboda wani saɓani na siyasa tsakaninta da Saudiyya, abin da kenan ya sa Saudiyya ta rungumi aikin gaba-gaɗi.

An fara amfani da na'urori na zamani wajen saƙa rigar Ka'aba a 1965. A shekarar 1972, Sarki Faisal bin Abdulaziz ya ba da umarnin kafa masana'anta ta musamman don saƙa rigar.

Saƙa rigar Ka'aba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwararru fiye 200 ne daga ƙasashen duniya suke aiki a masaƙar

A 2017, Sarki Salman ya ba da umarnin sauya duka injinan da ake amfani da su wajen saƙa rigar ta Ka'aba, inda ya ba da umarnin a saka na zamani.

Wasu bayanai na cewa masaƙar, ita ce masakar tufafi mafi girma kuma mafi kyawun na'urori a duniya.

Fiye da ƙwararru 200 ne daga ƙasashen duniya suke aiki a masaƙar, inda suke shafe shekara guda suna ɗinka riga ɗaya da aka yi imanin ita ce mafi tsada a duniya.

An ƙiyasta cewa ana kashe kusan dala miliyan shida wajen samar da rigar ta Ka'aba.

Ya ake yi da rigar da aka cire?

Rigar Ka'aba

Asalin hoton, Other

A duk shekara ana kai rigar Ka'aba da aka cire zuwa wani wajen ajiye kayayyaki na gwamnatin Saudiyya, inda ake adana ta ta yadda ƙwayoyin cutar bakteriya ba za su taɓata ba, ko kuma tasirin sinadarai su yi mata illa.

A wannan wajen ne ake yayyanka rigar zuwa ƙyallaye da dama, a rarraba wa manyan mutane na duniya da suka kai ziyara Saudiyya.

Ana kuma aike wa ƙasashe da ofisoshin jakadanci da ke ƙasar ta Saudiyya.