Shugaba Zelensky ya ce Ukraine za ta yi nasara kan Rasha

Volodymyr Zelensky

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce kasarsa za ta murkushe sojin Rasha

Shugaban Ukraine Volodomyr Zelensky, ya ce kasarsa za ta yi nasara a yakin da take yi da Rasha, a wani jawabi da ya yi ta bidiyo, inda yake Allah-wadarai da zargin da ake yi cewa Rasha na harar fararen hula.

Kalaman na Mista Zelensky sun biyo bayan sanarwar da babban mai gabatar da kara na Ukraine ya yi ne cewa an gano gawarwakin mutane fiye da dari hudu daga garuruwan da ke kusa da babban birnin kasar Kyiv, wadanda Rasha ta yi wa kisan gilla.

A jawabin da ya gabatar cikin jimami da kalamai masu sosa rai ranar Lahadi da daddare Shugaba Volodomyr Zelensky, ya zargi Rasha da aikata laifin kisan kiyashi a kan 'yan Ukraine da ke kananan garuruwan da ke kewaye da babban birnin kasar, Kyiv.

Garuruwan da suka hada da Bucha da Irpin da kuma Hostemel, yana mai tambayar dalilin yi wa wadannan mutane da ba su ji ba, ba su gani ba kisan gilla.

Ceto

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana ceton wata mata bayan ruwan makamai a garin Irpin, na Ukraine

Ya ce, ''Ina son kowace mahaifiyar sojan Rasha ta ga gawarwakin mutanen da suka mutu a Bucha, Irpin da Hostomel. Me suka yi? Me ya sa aka kashe su? Me mutumin da ke tuka keke a titi ya yi?

Me ya sa kuke kokarin kashe mutanen da ba kowan-kowa ba, masu zaman lafiya a birnin da ke zaune kalau?

Me ya sa ake daure mata a wuya bayan an cizge dan kunnensu daga kunnuwansu?

Ta yaya ake yi wa mata fyade sannan a kashe su a gaban 'ya'yansu, a mayar da gawawwakinsu abin dariya har bayan sun mutu?

Me ya sa suke latse gawarwakin mutane da motocin igwa? Me birnin Bucha ya yi wa Rasha? Ta yaya ake duk wannan?''

Mista Zelensky ya ce ya yi amanna kasashen Yamma za su dauki mataki bisa la'akari da abin da aka yi wa mutanen garuruwan nan na kewayen Kyiv.

Ya ce, ''Ba shakka akwai karin sabbin takunkumi da za a sanya wa Rasha, amma ya tabbata wannan ba zai isa ba Muna bukatar karin bayani. Ba a kan Rasha ba kadai, har ma da dabi'ar siyasar da ta bayar da damar zuwan wannan mummunan aika-aika kasarmu.''

Wani sojan Ukraine na boye wa harin jirgin sama mai saukar ungulu na Rasha

Asalin hoton, Reuters

Shugaban ya ce ko da an sanya wa Rashar wani jerin sabon takunkumi, to hakan ba zai isa hukuncin laifin da ta aikata ba.

Sojojin Rasha sun kara tashi tsaye kan yawan hare-haren da suke kaiwa a wuraren da suke hara a kudu da kuma gabashin kasar ta Ukraine, inda ake samun rahotannin karin fashewar bama-bamai a ranar Lahadi da daddare a garin Odesa.

Jami'an sojin Birtaniya masu samar da bayanan sirri sun ce an ci gaba da mummunan yaki a can gabashin kasar, a garin Mariupol, mai tashar jirgin ruwa wanda sojin Rasha suka yi wa kawanya, da kuma birni na biyu mafi girma na Ukraine din, Kharkiv.

An ruwaito wata sanarwa daga ofishin mai gabatar da kara na yankin da ke cewa mutum akalla bakwai ne suka mutu a sanadiyyar makaman da Rasha ke harbawa ta sama.