Manyan kaburbura a Ukraine: Yadda ake binne mutane a biranen da dakarun Rasha suka yi kaca-kaca da su

    • Marubuci, Daga Laurence Peter
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Luguden wutar da dakarun Rasha suke yi a wasu wuraren da ke Ukraine ya yi tsananin da ya tilasta wa garuruwa da birane binne fararen hular da aka kashe a manyan kaburbura.

Babu inda yakin ya fi kazanta kamar Mariupol, birnin da ke gabar teku wanda yake ta shan luguden wuta, inda aka haka manyan kaburbura cikin makonni biyu domin binne mutanen da aka kashe.

"Ba za mu iya binne kowanne mutum da aka kashe a kabarinsa shi kadai ba, kamar yadda ake yi ga mutanen da ke wajen birni da kuma yankunan da dakarun Rasha suke rike da su," a cewar mataimakin magajin birnin Mariupol Serhiy Orlov a hirarsa da BBC ta wayar tarho.

Wuraren da za a rika binne mamatan sun hadada wata tsohuwar makabarta wadda aka sake budewa, in ji Mr Orlov.

Gargadi: Wannan labarin yana kunshe da wasu hotuna da ka iya tayar da hankali

Ranar Lahadi, majalisar birnin ta ce adadin fararen hular da aka kashe ya haura 2,100. Luguden wutar da dakarun Rasha suke yi ya hana mutane fita daga Mariupol, duk da yunkurin da ake yi na samar da tudun mun-tsira.

Mr Orlov baiiya bayar da adadin fararen hular da aka binne a manyan kaburbura ba, sai dai ya ce an binne gawarwakin mutum 67 a wani katon kabari. "Ba mu iya gane wasu da aka kashe ba sai dai akwai takardun wasu da ke nuna ko su wane ne shu."

Dubban mutane suna boye a gidajen karkashin kasa, kuma a wasu lokuta, ya ce, mutane suna binne 'yan uwansu a bayan gida ko lambuna.

A cewarsa masu kwashe shara da masu gyaran hanyoyi suna kwashe gawarwaki daga kan tituna, a yayin da tsarin kula da birane ya wargaje. "An kashe wasu daga cikin mutanen a yayin da ake kwashe shara. Ba mu da hasken wutar lantarki, ko na'urar dumama daki, da ruwa da abinci tsawon kwana 11," in ji shi.

Mil 400 daga arewa maso yamma, a gefen babban birnin kasar, wato Kyiv, an haka wani babban kabari kusa da coci a garin Bucha, a cewar wani dan majalisar dokoki Mykhailyna Skoryk-Shkarivska. An binne fiye da mutum 60.

Wani likita da ke aiki a kusa da Irpin, Andriy Levkivsky, ya wallafa hoton yadda aka binne gawarwakin a Facebook. Likitoci sun binne wadanda aka kashe, wadanda aka kai gawarwakinsu asibitin Irpin.

Ms Skoryk-Shkarivska ta shaida wa BBC cewa an yi "jana'izarsu" a wani asibiti kafin a binne su. Ba dukansu aka gane ba kuma "babu wanda ya san tabbacin inda 'yan uwansu suke," in ji ta.

Dakarun Rasha sun kwace asibiti ranar Asabar kuma sun umarci likitoci su fice. Bucha da rabin Irpin yana hannun dakarun Rasha, a cewarta.

Dawowar manyan kaburbura abu ne mai girgiza zukata ga 'yan kasar Ukraine. Da dama daga cikinsu suna iya tuna Yakin Duniya na Biyu, lokacin da 'yan Nazi suka karkashe yahudawa da 'yan Soviet da kuma wani fari da dakarun Soviet suka kirkiro a Ukraine ta hanyar kwace hatsi da dabbobinsu a shekarun 1930.

Dakarun Rasha sun yi kawanya a biranen Kharkiv, Chernihiv da kuma Sumy da ke arewacin Ukraine inda suke ta barin wuta ba ji ba gani kuma sun kashe fararen hula da dama.

Ranar 6 ga watan Maris Oleksandra Matviichuk, wani dan rajin kare hakkin dan adam, ya wallafa hotunan makara a shafinsa na Tuwita tare da wani sako da ke cewa: "Bam din da dakarun Rasha suka harba ya kashe fararen hula a Chernihiv inda aka binne wadanda suka mutu a wasu manyan kaburbura. An binne wadanda suka mutu a dajin Yalivshchyna saboda dakarun Rasha suna luguden wuta a babbar makabartar Yatsevo da ke birnin."

Oleksandr Lomako, sakataren karamar hukumar hukumar Chernihiv, ya shaida wa BBC cewa ana binne mutanen da luguden wutar dakarun Rasha ya kashe a wata makabartar wucin-gadi. Ya tabbatar da cewa ba a iya shiga babbar makabartar garin a halin yanzu, saboda dakarun Rasha sun kewaye birnin daga bangarori uku.

"Bayan yakin za mu sake binne mamatan," a cewarsa, inda ya kiyasta cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon luguden wutar dakarun Rasha ya kai kusan 200.

Wani hari ta sama da suka kai ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 45 a Chernihiv - kisa mafi muni, a cewar Mr Lomako - inda ya kara da cewa hare-haren da ake kai wa da daddare suna kashe akalla fararen hula bakwai a kowacce rana.

Mutanen da ke cikin yanayi na kawanya kuma dakarun Rasha suke yi musu luguden wuta, binne 'yan uwansu a kaburburan wucin-gadi wani babban wulakanci ne.