Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kura-kuran amfani da makaman nukiliya da aka tafka da suka kusa jawo yakin duniya na uku
- Marubuci, Zaria Gorvett
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
Daga kutsen dabbobi zuwa lalacewar wani karfen na'urar komfutar da darajarsa ba ta wuce dala daya ba, wasu jerin sunayen abubuwan fargaba na tsallake rijiya da baya, sun nuna yadda yakin nukiliya ke da matukar saukin faruwa a bisa kuskure.
Da tsakar daren 25 ga watan Oktoba na shekarar 1962 ne, wata babbar motar daukar kaya na zura gudu a kan titin jirgin sama a Wisconsin. Lokaci kadan ya rage na dakatar da jirgi.
Mintoci kadan kafin nan, wani maigadi a Cibiyar Tsaro ta Sojin Saman Amurka da ake kira Duluth Sector Direction Center ya hangi wata inuwar wani abu na kokarin hawa ta kan shingen fili saukar jiragen sama.
Ya kai harbi kana ya danna kararrawar gargadi, cike da fargabar cewa wannan wani bangare ne na fadada kai hari daga Soviet. Nan da nan, kararrawar mai kutsen ta fara bugawa a ko wane sashe na sansanin filin jiragen soji saman.
Lamarin ya kara bazuwa cikin sauri.
A kusa da wani sansanin sojin saman na Volk Field, wani ya yi kuskuren danna wata kararrawa daban - don haka a maimakon gargadin tsaro, matuka jiragen sama sun ji wata jiniyar daukar matakin gaggawa da ke ankarar da su cewa su tattaru su tashi sama.
Ba tare da bata lokaci ba wuri ya cika makil da kai komo, a yayin da a guke suka yi ta kokarin tashi sama, bayan daura damarar yaki dauke da makaman nukiliya.
Lokacin ana tsakiyar tashin hankali na makamai masu linzamin kasar Cuba ne, kuma kowa na zaman zullumi.
Kwanaki goma sha daya kafin nan ne, wani jirgin leken asiri ya dauki wasu hotunan makamai masu linzami da na sirri, da kuma manyan motocin daukar makamai a kasar Cuba, wanda ke nuni da cewa dakarun Soviet na shirin kai hare-hare a fadin Amurka.
Yayin da hakan ke faruwa dai, game da wannan bati babu wani mai kuste - a takaice dai, ba wani mutum bane.
Inuwar da aka hanga na wucewa ta cikin shingen ba wani abu bane face dabbar bear. Duka dai kuskure ne.
Amma kuma a can sansanin Volk Field, sojojin basu san me yake faruwa ba. An ba su umarnin da suka hau jiragen saman su, an riga an ja hankulansu cewa ga abinda ke faruwa - an fara Yakin Duniya na Uku.
Tsallake rijiya da baya
Yana da matukar sauki a mance cewa akwai makaman nukiliya akalla 14,000 a fadin duniya, mai hadadden karfin hallaka rayuwar kusan mutane biliyan uku - ko ma batar da wasu halittu daga doron kasa.
Abinda ba mu yi tunani ba shi ne hakan ka iya faruwa a bisa kuskure.
An fada musu duka, tun bayan da aka kirkiro makaman nukiliya, an samu tsallake rijiya da baya akalla 22.
A shekarar 1958, wani jirgin saman yaki ya saki bam na nukiliya a lambun bayan gidan wasu iyalai a bisa kuskure; amma cikin ikon Allah, babu wanda ya mutu, duk da cewa kajin da suke kiwo sun kone.
Hadurra da dama sun faru, na baya-baya nan a shekarar 2010, lokacin dda Rundunar Sojin Saman Amurka ta gaza samun hanyoyin sadarwa da makamai masu linzami kimanin 50 na wani dan lokaci, da hakan ke nufin ba za a iya samun wata hanyar ganowa da dakatar da makaman daga sarrafawa da kai hari da kansu.
Yeltsin shugaba na farko da ya bude hanya
A ranar 25 ga watan Janairun shekarar 1995, da shugaban kasar Rasha na wancan lokacin Boris Yeltsinya zama shugaban kasa na farko a tarihi da ya bude ''dan akwatin nukliya'' - wata jakar da ke kunshe da fasahar zamani da umarnin yadda za a tayar da bama-baman nukiliya.
Masu sarrafa na'urar hangen jiragen na shugaba Yeltsin sun lura da cewa an kaddamar da harin roka a gabar tekun Norway, kana sun rika kallo cikin damuwa da fargaba a yayin da ya tashi can cikin sararin samaniya. Ina ya dosa - kana shin na abokan gaba ne?
Dauke da dan akwati a hannunsa, Yeltsin cikin zafin rai ya sanar wa da manyan mashawartansa game da ko ya kaddanar da harin ramuwar gayya.
Cikin mintocin da ya rage musu na su yanke hukunci, sai suka lura da cewa ya doshi bakin teku ne, kana ba wata barazana ba ce.
Daga bisani ne aka fahimci cewa ba harin makaman nukiliya ba ne.
Mahukuntan kasar Norway sun cika da mamakin cewa hakan ya haifar da rudani, saboda an riga an sanar da kaddamarwa wa jama'a akalla wata guda kafin lokacin.
Babu gudu babu ja da baya
Muhimmin abu, koda an kaddamar da makamin nukiliya saboda gwaji ne ne ko da gaske ne komai na iya faruwa - da zarar an harba, ba za a iya sauyawa ba.
"Muddin shugaban kasa ya amince da gargadin karya, to shi ma zai fara yakin nukiliya a bisa kuskure,'' in ji IWilliam Perry, wanda ya taba aiki da Sakataren Harkokin Tsaron Amurka karkashin tsohon shugaban kasa Bill Clinton.
"Babu abinda zai iya yi game da hakan. Ba za a iya yi wa makamai masu linzami kiranye ba, kuma ba za a iya lalata su ba.''
Me yasa ake ta samun tsallake rijiya da baya? Kuma ta yaya za mu iya hana kara faruwar hakan nan gaba?
Yadda aka fara kai hare-haren makaman nukiliya
A lokacin da ake tunanin yiwuwar tafka kurakurai, su ne alamun gargadi na farko lokacin Yakin Cacar Baka.
A maimakon jiran abkawar makamai masu linzami kan wajen da aka harba su - wanda za su, samar da ingantattun shaidu na wani hari - wannan wani yunkuri ne na gano su tun da wur, don mayar da martani cikin sauri tun kafin a lalata su.
Kafin yin hakan kuma kana bukatar cikakkun bayanai.
Abubuwan da Amurkawa da dama ba su sani ba, yanzu haka Amurka na da taurarin dan adam da dama da a asirce da ke lura da ita a koda yaushe, da suka hada hudu da ke aiki daga nisan kilomita 35,400 a saman doron kasa.
Kuma ba sa matsawa daga gurbin da suke.
Hakan na nufin suna iya kallon wuri guda a koda yaushe, don su rika gano yiwuwar duk wata barazanar makamin nukiliya, kwanaki bakwai na makom sa'oi 21 a kullum.
Abinda taurarin dan adama za su iya yi shi ne bin diddigin yadda makamai masu linzami ke tafiiya.
Kan haka, Amurka tana kuma da daruruwan tashohin hangen jirage, da za su iya nuna matsayinsu, da karfin gudunsu, da kuma lissafa hanyoyinsu.
Fasaha
Akwai kura-kurai kashi biyu da ka iya haifar da gargadin gargadin barazana a bisa kuskure - na fasahar zamani da kuma na dan adam( ko kuma, idan lallai mun take sa'a, duka a lokaci guda).
Babban misalin abinda ya faru da farko shi ne a yayin da Perry na aiki wa Shugaban Amurka Jimmy Carter a shekarar 1980.
"Abin mai matukar mamaki ne,'' in ji Perry. Y afara ne ta kiran wayar tarho da misalin karfe uku, lokacin da ofishin sa ido na rundunar sojin saman Amurka ya sanar da shi cewa na'urorin komfutar sa ido sun gano makamai masu linazmi 200 na tunkarowa kai tsaye daga Trayyar Soviet zuwa Amurka.
Lokacin, sun riga sun farga cewa ba haring aske ba ne - na'urorin komfutar ne suka yi kuskure.
''Sun kira fadar White House kafin su kira ne - sun kira shugaban kasa. Kiran wayar ya shiga zuwa mai bas hi shawara kan harkokin tsaro,'' in ji Perry.
An taki sa'a ya jinkirta na tsawon mintoci kafin ya tashi shugaban kasa, lokacin da suka samu bayanin cewa ba gakiya bane.
Amma in da a ce ba su dan jinkirta ba - da sun tashi Carter daga barci cikin sauri, da yanzu duniya zama wani abu da ban a yanzu.
Yadda za a kauce wa mummunan hadari
A bisa yin la'akari da duka wannan, Perry ya yi hadin guiwar rubuta wani littafi - The Button: The New Nuclear Arms Race and Presidential Power from Truman to Trump - tare da Tom Collina, daraktan Ploughshares Fund, kungiyar da ke fafutika game da manufofi kan samun kariya daga makaman nukiliya, tare da samar da shawarwarin da suka dace.
Da farkon fari, suna bukatar ganin an karshen jagorancin mutum daya tak - don saboda a rika yanke shawara kan ko a kaddamar da wadannan makaman kare dangi a siyasance, da kuma yin la'akari sassauci kan mummuna tasirinsu kan lafiya da kwakwalwa.
A Amurka hakan na nufin kada kuri'a a Majalisar Dokoki.
"Hakan zai jinkirta daukar mataki game da ko za a kaddamar da su,'' Perry ya ce.
"Irin ramuwar gayyar kadai da ya kamata a yi ita ce inda ka san cewa za su kawo hari.
Ba za mu taba amincewa da gargadin barazana na a bisa kuskure ba,'' in ji Collina.
Kuma hanya mafi sahihanci na tabbatar da cewa barazanar da gaske ne, shi ne a jira ta sauka.
Ba batun amfani a karon farko
Na biyu shi ne, Perry da Collina sun yi azanci kan karfin makamashin nukiliya tare da yin alkawarin yin amfani da wajen mayar da martani kawai - amma ko kadan batin kasancewa a karon farko ba.
"China wani muhimmin misali ne da za a iya yi da ita, saboda ba ta da manufofi a kan batun yin amfani a karon farko,'' in ji Collina.
"Sun sanar da cewa ba za su taba amfani da malaman nukiliya a farkon tashin hankali ba, kana akwai sahihanci a wannan manufa saboda kasar China ta rarrabe manyan makamanta( da suka kunshi kayan nukiliya) daga makamai masu linzaminta (tsarin ayyuka).''
Hakan na nufin dole sai China ta hada biyun wuri guda kafin ta kaddamar da hari, kana da taurarin dan adam da dama da ke kallon irin wannan akai-akai, akwai tunanin wani zai lura.