Boyayyun al'amura kan shirin juyin mulki mai alaka da fataucin kwayoyi

Sojojin Guinea-Bissau - 7 February 2022

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Daga Nicolas Négoce
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Bissau

A farkon watan Fabrairun 2022, alamu suka nuna cewa kasar Guinea Bissau ita ma za ta bi sahun wasu kasashen yammacin Afrika da sojoji su ka yi juyin mulki sai dai yanzu wasu sun fara nuna shakku a kan bayanan da hukumomi suka fitar a kan al'amarin.

Sojoji sun yi juyin mulki da dama ko kuma sun rika kokarin kifar da gwamnati tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1974, kuma saboda ana amfani da ita a matsayin cibiyar masu fataucin miyagun kwayoyi, labarin da aka samu daga kasar a kan cewa mutane na kokarin kifar da gwamnatin shugaba Umaro Sissoco Embalo, ya yi kama da abin da za a kira da yanayi na rashin zaman lafiya.

Sojoji sun yi juyin mulki a Mali da Guinea da Burkina Faso, kuma a ranar 1 ga watan Fabrairun 2022, 'yan bindiga da ke barin wuta suka kutsa cikin fadar shugaban kasa a Bissau babban birnin kasar.

Shugaban kasar mai shekara 49 da ministocinsa na cikin ginin suna taro a wancan lokaci .

Sai dai bayan sa'oi biyar da gwabza fadan da ya yi sanadin mutuwar mutum 11 , Mr Emballo, ya ce an shawo kan al'amarin kuma ya danganta shi a kan yunkurin masu fataucin miyagun kwayoyi da suka yi kokarin kifar da gwamnatinsa.

A baya bayannan ya kuma bayyana sunayen mutum uku da a baya aka cafke a Amurka lokacin da suka yi kokarin shigar da hodar ibilis cikin kasar wadanda ake zargin suna da hannu a yunkurin juyin mulki.

Shugaban kasar Guinea Bissau

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaba Umaro Sissoco Embaló ya ce ya ga wadanda ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi lokacin da ake musayar wuta

Daya daga cikinsu shi ne tsohon shugaban rundunar sojin ruwan kasar , José Américo Bubo Na Tchuto, kuma shugaban ya ce ya ga sauran biyun da kansa a lokacin da yake kokarin boyewa daga maharan.

Tuni aka cafke mutanen uku kuma kawo yanzu ba su ce komai ba a kan zarge zargen.

A hirar da ya yi da 'yan jarida ya fada mu su cewa ya tsallake rijiya da baya saboda karfin imaninsa.

Sai dai hasashen da ake yi cewa watakila miyagun kwayoyi na da nasaba da harin ya biyo bayan kaurin sunan da kasar ta yi na komawa matattarar kwayoyin da ake shigowa da su daga kasashen da ke yankin Latin Amurka da za a wuce da su zuwa turai.

A baya Majalisar Dinkin Duniya da Amurka sun bayyana kasar da yawan al'umarta ya kai miliyan biyu a matsayin cibiyar masu" safarar miyagun kwayoyi" inda 'yan siyasa ke samun kudi daga masu aikata muggan laifuka kuma akwai wasu da aka ba wa mukamai a cikin gwamnati domin kare haramtacciyar cinikayyar.

A cikin 2019, Mista Embaló, ya yi nasara a zabukan da aka yi ta ce-ce-kuce da su kuma ya yi alkawarin yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi.

Magoya bayansa sun ce ya samar da yanayin da 'yan sanda za su iya yakar wannan sana'ar amma babu tabbas ko ya kawo wani sauyi.

"Wasu daga cikin wadanda ke da hannu a baya da alama sun dawo," in ji Lucia Bird ta kungiyar Global Initiative Against Transnational Organized Crime.

'Muna cikin zaman lafiya '

Sai dai mutane sun nuna shakku a kan yunkurin juyin mulkin.

A wani shagon aski da ke tsakiyyar Bissau, wani kwastoma ya ce shi bai yadda cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar ba.

Wata mata na tafiya a tsakiyar birnin Bissau

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Al'ummar kasar Bissau sun shiga cikin wani yanayi na fargaba

"Al'amura sun dai-daita. muna cikin zaman lafiya a Bissau," in ji shi . "Ba bu abin da ya faru ka duba ka gani."

Duk da haka, duk da rashin yawan dakarun soji, al'amura sun tabarbare kuma wata budurwa ta ce kamar kasar "ta na komawa baya".Duk da cewa ba bu sojoji a kan tituna, amma ana cikin wani yanayi.

Babban abokin hamayyar shugaban kasar a siyasa, tsohon Firayim Minista Domingos Simoes Pereira, wanda ke jagorantar babbar jam'iyyar siyasar kasar, ya fito fili ya nuna shakku a kan irin abubuwan da ya faru.

"Ya ya za ku gaya mani an yi harbe-harbe har tsawon sa'o'i biyar kuma babu wani jami'in soja da ya zo ya taimaka wa majalisar ministoci? Wannan abin mamaki ne," kamar yadda ya shaida wa BBC.

"'Yan kasar Guinea-Bissau suna son sanin hakikanin abin da ya haddasa wannan yunkurin juyin mulkin. Su wane ne wadanda suka yi wannan juyin mulkin? Su Nawa ne ? Wane ne jagoransu? Menene ainihin manufarsu?"

Sai dai shugaban kasar ya gaza bada cikakken bayani ga wadannan tambayoyi ko da yake ya kafa kwamitin bincike.

Shugaban kasar ya jadada cewa " Wadanda suke rike da bindigogi mutane ne masu alaka da kungiyoyin masu fataucin miyagun kwayoyi ".

' Harin da aka kitsa '

Da aka tambaye shi ko har yanzu yana da yakinin cewa yana da goyon bayan sojoji a lokacin da ake ganin ba su kai masa dauki ba, sai ya ce eh amma ya kara da cewa abu mafi muhimmanci shi ne ya yi imani da Allah.

Akwai kuma bayanin da masana siyasa irinsu Rui Landim, suka yi wadanda suka ce shi ne dalilin da yasa shugaban kasar ya tsira da kuma yadda sojoji suka rika dari-darin kai masa dauki.

Ya shaida wa BBC cewa, yana tunanin mai yi wuwa Mr Embalo, ya shirya juyin mulkii ne domin shawo kan kungiyar ECOWAS ta tura masa da sojoji domin "ya ci gaba da kasancewa kan mulki".

Sojojin Ecowas a Guinea-Bissau a 2011

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A baya an tura sojojin kasashen yammacin Afrika zuwa kasar

Bambance-bambancen da ke tsakanin shugaban kasa da firaminista da majalisar dokokin kasar ya sa shi cikin mawuyacin hali.

Sai dai shugaban ya ce alkawarin da Ecowas ta yi na tura sojoji wani aiki ne na hadin kan yankin.

Haka kuma akwai rashin tabbas game da ainihin abin da ya faru kusan makwanni biyu da suka gabata kuma kawo yanzu akwai wasu da ke jin tsoro

Bayan harin da aka kai, wasu sun tsere zuwa cikin karkara kuma har yanzu ba su dawo ba.