An gano kashin mutum mai shekara dubu biyar a kogin London

Mai tukin kwale-kwale Simon Hunt shi ne ya gano kashin a karkashin kogin

Asalin hoton, Simon Hunt

Bayanan hoto, Mai tukin kwale-kwale Simon Hunt shi ne ya gano kashin a karkashin kogin
    • Marubuci, Daga Harriet Orrell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Wani mai tukin kwale-kwale ya gano wani kashin mutum wanda ake ganin zai iya kasancewa abu mafi dadewa da aka taba tsamowa daga kogin Thames na London.

Simon Hunt ya tsinto kashin ne wanda na cinya ne a kasan kogin inda igiyar ruwan ba ta da karfi sosai. Binciken da aka yi a kansa ya nuna cewa ya kai sama da shekara dubu biyar.

Nan da nan ya fahimci cewa kashin mutum ne, sai ya fara fargaba.

"Da ka ganshi za ka ga ya dade sosai, amma kuma sai wata zuciya ke ce min idan kuma ba tsohon ba ne fa?'' In ji Simon din.

Ya kara da cewa, :''Ban san yadda za a ga kashi ba idan shekara biyu kawai ya yi a cikin ruwa, to idan kuma ya kasance wani abu ne kuma na daban fa wanda zai tayar da hankali?"

Simon, wanda mai sana'ar zane ne, ya hangi kashin ne lokacin da yake shiga kwale-kwalensa. Daga nan ne ya tuka jirgin ya je ya tsamo kashin daga kasan ruwan.

The bone on a book shelf

Asalin hoton, Simon Hunt

Bayanan hoto, Kashin ke nan a gidan Simon watakila inda kyanwarsa Nutmeg ba za ta guiguye shi ba, kafin a kai shi gidan adana kayan tarihi

Farar jakar leda

Daga nan ne sai ya sanya kashin a wata jakar leda fara ya tafi da shi gida ya nuna wa matarsa. Yana tafe da kashin wanda kusan kowa yana iya ganinsa karara a cikin ledar, amma ba wanda ya damu da mene ne.

Ya kira 'yan sanda, wadanda suka neme shi da ya nuna musu inda ya samo shi domin su gudanar da bincike inda. sai dai lokacin da 'yan-sandan suka je wurin ruwan ya fara toroko, wajen ya yi zurfi sosai.

'Yan-sandan sun aika da kashin dakin binciken kimiyya, abin da ya dauki watanni.

'Ko ka san shekararsa nawa?'

Simon ya ce bayan da aka dawo da shi, 'yan-sandan sun shammace shi, "Sun ce min dadadde ne, sannan suka tambaye ni ko na san shekarunsa?''

Stonehenge, in Wiltshire, UK

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kashin ya girmi wadannan duwatsu da aka yi musu wannan fasali kusan shekara 2500 kafin zuwan Annabi Isa (as)

"Tunanina na tsoho ko dadadden abu bai kai can-can ba, to amma na sha mamaki ainun."

Zamanin mutanen da

Binciken ya nuna cewa kashin na mutum ne wanda ya rayu tun a zamanin da da na Birtaniya da ake amfani da duwatsu a matsayin kayan aiki. Kwararru sun ce ya kasance ne daga shekarar 3516 da 3365 kafin bayyanar Annabi Isa(as).

Ba a dai iya gano kashin ko na mace ne ko namiji ba.

Kashin ya fi hatta dalar Giza da ake da su a Masar dadewa.

The Great Pyramids of Giza with a camel lying in front of them

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dalar Masar wadda mutanen zamanin da suka gina daga kusan shekara ta 2550 zuwa 2490 kafin zuwan Annabi Isa (as) kusan shekara dubu bayan mutumin ya rayu a duniya

"Mutane na ce min suna ganin abin mamaki ne a ce an samu kashin a London, amma sai su san cewa fa a lokacin babu London,'' in ji Simon

ya kara da cewa : "Ina ganin kila tabo ne ya rufe shi ko wani abu har ya kawo wannan lokaci daga baya kuma kila ruwa ko wani abu ya tono shi, har ni kuma na same shi a ruwan."

The bone with a tape measure showing it is around 43cm (17 inches) long

Asalin hoton, Simon Hunt

Bayanan hoto, Wani kwararre ya kiyasta tsawon mutumin da ke da kashin ya kai kafa 5 da inci 7, ta hanyar auna tsawon kashin guiwar

Kokon kan mutanen da

Gidan adana kayan tarihi na London, wanda Simon yake fatan can za a kai kashin a karshe, yana da wani bangare na kokon kan irin mutanen da da suka rayu a tsakanin shekara 3645 da 3600 kafin zuwan Annabi Isa (as).

Dakin adana kayan tarihin ya ce kokon kan na daga cikin abubuwa dadaddu da aka samo daga kogin na London, kuma za a adana wannan kashin a kusa da wannan kashin kai.

A yanzu dai an mayar wa Simon wannan kashin yana tare da shi.

'Kyanwa ba za ta guiguya ba'

Mutumin ya ce "A gaskiya ban yi tunanin ma inda zan ajiye shi ba, amma dai koma ina ne wuri ne da kyanwa ba za ta guiguye shi ba."

"Ina son in mutunta shi saboda mutum ne.

"Wannan kashin wani bangare ne na kafar mutum, wanda yake tafiya a nan sama da shekara dubu biyar da ta wuce."

Wani mai laliben tabo a kogin Thames ke nan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tabon kogin Thames na London yana da laka sosai saboda haka iska ba ta iya ratsa shi sosai don haka abu zai iya dadewa shekara da shekaru a cikinsa bai lalace ba

Masu laliben tabo

Kogin Thames, da ke London ya zama wani wuri da ke ajiye da abubuwa na tarihi masu daraja. Masu laliben tabo sun samo abubuwa da dama da yanzu suke ajiye a dakin adana kayan tarihi na London.

Mutum yana bukatar lasisi daga hukumar kula da tashar ruwa ta London kafin ya yi wannan sana'a ko aikin. Abu ne da ya saba doka ka yi lalube ko ka dauki wani abu na kayan tarihi ko wane iri ne daga ruwa ba tare da lasisin ba.

To amma a wannan karon, Simon yana kokarin sauke wani nauyi ne da ya rataya a wuyansa, kuma zuwa yanzu babu wani da ya tayar da jijiyar wuya a kan dauko wannan kashi.

A bar maganar tsarabe-tsaraben doka, wannan abu ne da kawai za a ce Simon ya taki babbar sa'a a wannan safiya ta tuka kwale-kwalensa.