Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda dunkulen zinare mai girma yayi layar zana a Nijar
Batan wani danƙareren zinare da nauyinsa ya kai kilogram 122 a Jamhuriyar Nijar ya janyo taƙaddama tsakanin wasu masu haƙar ma'adanai da jami'an tsaron da suka yi wa zinaren rakiya.
Bayanai sun ce an haƙo zinaren ne a Djado, wani wurin haƙar ma'adanai, inda masu haƙar suka nemi rakiyar jami'an tsaro, amma sai masu rakiyar suka ce an ƙwace dutsen mai matuƙar daraja a lokacin wani hari da aka kai musu.
Sai dai masu zinaren sun yi tsalle sun dire kan cewa atafau wasa da hankali ake son yi musu da dukiya, lamarin da ya sanya Gwamnan jihar Agadez shiga tsakani.
An ƙiyasta cewa darajar zinaren ya kai biliyan 3.6 na sefa, kwatankwacin dala miliyan 34.
Taƙaddamar ɓacewar zinaren ta taso ne tsakanin masu zinaren na Djado da kuma jami'an tsaro masu rakiyarsa zuwa birnin Agadez.
Nauyin zinaren kwatankwacin kilogram 122 wanda ake zargin ya yi ɓatan dabo tsakanin garin Chirfa da na Dinne, bayan wani harin da aka ce an kai kan ayarin motocin da ke dakon zinaren ranar 29 ga watan nan na Janairu.
Mallam Nouriddine Garba Djibo na cikin wadanda suka mallaki zinaren, ya shaida wa BBC cewa ba za ta saɓu ba:
"Ba a cewa an kai hari ba tare da an yi ɓarin jini ko an yi mace-mace ba. A ce an yi atak an tafi, mu kayanmu suna hannunsu. Su ba mu kayanmu, domin mu abin da muka fi gamsuwa da shi kenan."
Ya ce akwai daya daga cikin masu harkar zinaren da ya biyo ayarin motocin "kuma sai da ya kai wani waje mai suna Amzagar, inda bayan ya farka daga barci sai ya tafi sayen nama.
"Sai aka ce masa 'ba ka san an yi atak ba ne?'. Sai ya ce a ina aka yi atak? Sai aka ce ma sa kenan kana kwana."
Ya kuma ce mutumin ya yi mamakin cewa an kai hari kan ayarin motocin, kuma an kai shi har gaban gwamnan jihar Agadez inda ya maimaita abin da ya faru a gabansa.
An kuma yi wani zama da gwamnan na Agadez Magaji Mamane Dada tsakanin jami'an tsaro da masu zinaren, kuma gwamnan ya shaida wa BBC cewa ya saurari dukan bangarorin kuma ya bayar da umarni da a binciki yadda lamain ya auku.
"Jami'an tsaro na gudanar da bincike, kuma alkalai za su karɓi takardu daga hannunsu. Bayan an kammala bincike za mu ga abin da Allah zai bayyana mana."
Wani wakilin masu zinaren ya ce gwamnan na Agadez ya ce su ba shi kwana uku domin a gano inda aka yi da dukiyarsu.
Abin da ya tunzura masu zinaren har suka kai kara ofishin gwamnan Agadez shi ne rahoton farko da suka samu daga jami'an tsaro cewa an gano zinaren a wani wuri, amma daga baya sai labarin ya sauya, inda aka ce musu ba a san inda zinaren yake ba.