Matsalar tsaro: 'Yan Neja na neman danginsu da harin ƴan bindiga ya tarwatsa

Asalin hoton, others
Mutanen garin Galadima Kogo a jihar Neja na ci gaba da neman 'yan uwa da danginsu, waɗanda ake fargabar ko dai sun ɓata ko kuma an kashe su a wani mummunan hari da aka kai wa garin cikin ƙarshen mako.
Bayanai sun ce 'yan bindigar sun shafe tsawon sa'o'i suna cin karensu babu babbaka a garin da ke ƙaramar hukumar Shiroro, inda suka kashe mutanen da zuwa yanzu ba a tabbatar da yawansu ba.
Kazamin harin na zuwa ne mako biyu bayan shugaban Najeriya ya ƙaddamar da abin da ya kira wani gagarumin aikin soja don kakkaɓe 'yan fashin daji da gyauron 'yan Boko Haram a jihar ta Neja.
Shaidun BBC ta zanta da su, sun bayyana cewa maharan sun je garin Galadima Kogo a ranar Asabar da tsakar rana kan Babura dauke da muggan makamai.
Wani mutum da ya tsere zuwa garin Zumba mai makwaftaka ya shaidawa BBC cewa, suna shiga garin suka riƙa harbin kan mai uwa da wabi.
Sannan ya ce sun fasa ofishin 'yan sakai suka kubutar da 'yan uwansu kana suka ƙona ofishin da motocin da ke wurin.
Shi ma wani mutumin da ya rasa 'yan uwansa sakamakon farmakin, ya ce 'yan bindigar sun kashe mutane da dama tare da tarwatsa mutanen garin.
"Tsoro da fargaba sun hana mu zuwa dauko gawawwakin 'yan uwanmu, saboda fargabar ka da 'yan bindigar su sake dawowa, sannan mata da kananan yara na cikin firgici, sakamakon abin da ya faru."
Me gwamnati ke cewa?
Sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmad Matane ya tabbatar da kai harin, sai dai ya ce basu tantance adadin wadanda aka kashe ba.
Bayanai dai na cewa duk da iƙirari da hukumomi ke yi na samun nasara ko yaƙar matsalolin tsaro a Neja, 'yan fashin dajin, na ci gaba da aukawa jama'a a sassan jihar a kai-a kai.
A gefe guda kuma ga barazanar 'yan Boko Haram da ke ci gaba da mamaye garuruwa da dama na jihar, al'amarin da yasa al'ummar jihar Nejan suka bukaci mahukunta su sauya salo a yakin da ake da 'yan bindigar.
Karin haske
Tun a shekarar da ta gabata ake ta samun rahotanni da ke cewa ƙungiyar Boko Haram ta mamaye garuruwa da dama na jihar, inda suke bai wa mazauna ƙauyuka kuɗi tare da sanya su cikin mayakansu.
Akwai kuma lokacin da shi kan sa gwamnan Nejan Abubakar Sani Bello ya fito ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar Boko Haram ta kafa tuta a wasu ƙananan hukumomin jihar guda biyu.
Matsalar tsaro na ci gaba da zama tarnaki da janyo koma baya ta fannoni da dama a yankin arewacin Najeriya.
Fannin kasuwanci da noma duk sun samu tawaya sakamakon matsalar rashin tsaron, sai uwa uba zaman fargaba da zullumin da yawancin mazauna kauyuka da aka fi kai wa hari ke fama da ita.











