Rikicin Sudan: Rashin rayuka domin neman 'yanci

    • Marubuci, Daga Mohanad Hashim
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

"Ko na tsira daga kisan kiyashi?" in ji wani matashi ɗan Sudan yayin da yake amsa kiran da na yi masa ta wayar tarho jim kaɗan bayan da jami'an tsaro suka bude wa masu zanga-zanga wuta a Khartoum.

Matashin wanda aka fi sani da sunan Bashy a shafinsa na Twitter, ya shaida min yadda daya daga cikin mutum bakwai da aka jikkata ya mutu ranar Litinin a babban birnin.

"Ina cikin daukan bidiyon masu zanga-zangar kuma ina tafiya a kafa lokacin da wani harsashi ya fasa kirjinsa; a gaba na ya mutu. kadan ya rage harsashin ya same ni!"

Wata uku kenan da Bashy, wanda shekarunsa na haihuwa ba su kai talatin ba, ke fita zanga-zanga.

Kamar sauran sa'o'insa ya fusata da sojoji suka kwace mulki a watan Oktoba, kimanin shekara biyu bayan kulla yarjejeniyar da sojoji suka kula da kungiyoyin fararen hula ta yin karba-karba a bangaren mulki.

Rayuwa ta fara inganta kuma tattalin arzikin kasar ya fara farfadowa yayin da Firminista Abdalla Hamdok ya fara kokarin dawo da Sudan cikin hayyacinta bayan takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakaba wa kasar yayin tsawon mulkin Omar al-Bashir, wanda ake tuhuma da amfani da kasar wajen taimaka wa ta'addanci.

Makarraban tsohon shugaban kasar ne suka hambarar da gwamnatinsa a watan Afrilun 2019 yayin zanga-zangar gama garin da aka yi, sai dai sun nuna gazawarsu wajen mika wa fararen hula mulki yayin da suka fara harbinsu bayan da suka bayyana a titunan kasar watanni biyu bayan juyin mulkin.

Fushin da duniya ta nuna ya tilasta wa sojojin amincewa da shirin mika mulki - sai dai kamar yadda kowa ya sani ne, sojojin ba su ji dadin tsarin ba kuma juyin mulkin na baya-bayan nan ya tabbatar da haka.

'Kwan-gaba kwan-baya'

Bashy ya ce matasan ne ke jagorantar kwamitocin da ke shirya dukkan zanga-zangar da ake yi a fadin kasar.

A zahiri ana kiyasta cewa kashi 61 cikin 100 na 'yan Sudan wadanda shekarunsu na haihuwa na kasa da 25 ne, kuma sun gaji da abin da Bashy ya kira "mulkin kama karya".

"Daban muke da sauran wadanda suka gabace mu", inji Bashy.

"Muna son kawo karshen wannan tsarin na kwan-gaba, kwan-baya a mulkin kasarmu. Wannan ne dalilin da muke zanga-zanga - saboda muna son ganin karshen wannan matsalar."

An mayar da makarrabai bisa madafan iko

Masu zanga-zangar na jin gaskiya na tare da su - kuma an yi wa gwamnatin sojin kasar mummunar illa bayan da Firaiminista Hamdok ya ajiye mukaminsa a farkon wannan shekarar.

An dai yi ma sa daurin talala bayan juyin mulkin - amma sai da ya kulla wata sabuwar yarjejeniya da hafsoshin sojin - matakin da kungiyoyin da ke mara masa baya wato Forces for Freedom and Change suka yi watsi da shi.

Makonni shida kawai Hamdok ya yi kafin ya gane cewa ba zai iya mulkin kasar ba sai da goyon bayan kungiyoyin da ke karkashin inuwar Forces for Freedom and Change.

A cikin wannan makon, Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kafa wata sabuwar gwamnatin rikon kwarya wadda ta hada da wasu cikin mukarraban tsohon shugaban Omar al-Bashir.

Babu sauran aminci

A tsakiyar watan Janairu ne gwamnatin mulkin sojin ta kafa wata rundunar yaki da ta'addanci.

Kallon masu zanga-zangar a matsayin 'yan ta'adda ya yi kama da dabarar da tsohon shugaba al-Bashir ya rika amfani da ita ta raba kawunan al'umma.

Kan halin da ake ciki ne wata kungiya mai sunan Friends of Sudan suka yi wani taro cikin wannan makon domin samar da wata mafita.

Kungiyar ta hada da Amurka da Birtaniya da wasu kasashen Tarayyar Turai da kawaye kamar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sai dai Bashy da matasan Sudan masu fafutuka ba sa ganin yunkurin zai haifar da wani abin a zo a gani.