Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Juyin mulki a Sudan: Dubban mutane suna zanga-zanga
Al'ummar Sudan sun bazama kan tituna domin zanga-zangar kin amincewa da mulkin sojoji, a yayin da aka cika shekaru uku da yin juyin juya hali a kasar.
Dubban 'yan Sudan ne suka cika titunan birnin Khartoum, inda jami'an tsaro suka mayar da martani da harba hayaki mai sa hawaye.
Zanga-zanga a shekarar 20919 ta kai ga hambarar da mulkin dadadden shugaban kasar Omar al-Bashir
Shugabannin sojoji da farar hula sun kulla yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka, bayan juyin mulkin da aka yi a watan Oktoba.
A watan da ya gabata, aka mayar da hambararren Firaiministan kasar Abdalla Hamdok kan mukaminsa, bayan an yi masa daurin-talala bayan sojoji sun yi juyin mulki.
Sai dai matakin bai sanya an daina zanga-zanga ba, inda masu boren ke bukatar a samar da gwamnatin tsantsar farar hula.
A ranar Lahadi, masu zanga-zanga sun yi maci har zuwa fadar gwamnati da ke Khartoum, wanda nan ne gidan jagoran juyin mulki Janaral Abdel Fattah al-Burhan, suna rera wakar ''Mutane na da karfi, babu gudu ba ja da baya.''
Tare da fatan ganin "faduwar" al-Burhan.
"Duk wani salon juyin mulki haramtacce ne, hatta dawo da Hamdok mukaminsa. Lokacin juyin juya hali, wato na watan Disamba, an yi ne domin kasa baki daya, ba wai domin wani wasu tsirarun mutane ba," in ji wani mai zanga-zanga a hira da kamfanin dillancin labarai mna AFP.
An kuma gudanar da zanga-zanga a wasu birane da garuruwan kasar Sudan.
Hotuna sun nuna dandazon ma su zanga-zanga, su na daga tutar Sudan, ya yin da wasu ke rike da hotunan wadanda aka kashe tun daga zanga-zangar juyin-juya hali, zuwa zanga-zanga bayan juyin mulki.
A kalla mutum 45 ne suka mutu daga lokacin zanga-zangar juyin mulkin watan Oktoba, kamar yadda kungiyar likitoci mai zaman kanta ta bayyana.
Karkashin rabon madafun ikon da aka cimma matsaya a shekarra 2019, lokaci ya yi da Janaral Burhan ya sauka daga mukamin, tare da mikawa ga farra hula a watan jiya.
Ya kare matakin juyin mulki da cewa sojoji na kokarin kare kasar daga fadawa yakin basasa, wanda ke barazanar barkewa da 'yan siyasa ke tunzura farar hula da bijirewa jami'an tsaro.
Ya kara da cewa har yanzu Sudan na da aniyar mika mulki ga farar hula, tare da shirya lokacin zabe a watan Yulin shekarar 2023.
Karkashin yarjejeniyar da Mista Hamdok ya amince da ita a watan jiya, ministan da aka zaba zai ci gaba da jan ragamar kasar. Sai dai babu tabbacin yawan kujerun da za a bai wa farar hula a gwamnatin, amma ana ganin sojoji ne za su mamaye gwamnatin.
Masu zanga-zangar ba su amince da sojoji ba, sun kuma yi watsi da duk wata yarjejeniyar ta raba madafun iko.
"Na zo wajen nan saboda ban amince da duk wata yarjejeniyarsiyasa da aka cimma ba, tun da ba ta kunshi ko wakilcoi al'umma ba," in ji wani mai zanga-zanga a birnin Khartoum.