Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sudan: Masu kalubalantar janar-janar na sojin Sudan sun ce: 'Ba za ku iya kashe dukkanmu ba'
- Marubuci, Daga Andrew Harding
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Khartoum
Mako biyu ke nan bayan da sojoji suka karbe mulkin kasar sakamakon juyin mulkin da suka yi, amma har yanzu an toshe wasu titunan babban birnin kasar Khartoum inda aka sa shingaye.
A yawancin wurare, an cire duwatsu da kuma tayoyin da aka sanya a kan tituna saboda a ba da damar wucewa.
To amma akwai zaton da ake yi cewa komai zai iya dawowa kamar kona tayoyi da zanga-zanga dama abubuwan da sojoji ke yi.
Babu wata mafita face sasantawa ta hanyar tattaunawa, inji Suleima Elkhalifa, wadda ke jagorantar wani bangare na gwmnatin rikon kwaryar kasar da aka dorawa alhakin kare mata da yara daga dukkan cin zarafi.
"A yanzu al'ummar kasar sun farga. Sun waye da siyasa. Bayan shekara 30 ana mulkin kama-karya na sojoji ba za mu mika wuya ba. Muna da matasa da yawansu ya kai kashi 50 cikin 100 a kasarmu, don haka a bayyane take ba ma son wannan gwamnatin. Ba za mu bari su kashe mu gaba daya ba, ba za mu su lalata mana burikanmu ba" inji ta.
'Sojoji kamar dabbobi suke'
Alamu sun nuna yadda ake nuna goyon baya ga Abdalla Hamdok, firaministan gwamnatin rikon kwarya, wanda aka tsare bayan sojoji sun yi juyin mulki a kasar, har yanzu na karkashin daurin talala.
"Hamdok ya tabatar mana da cewa shi mutum ne mai faɗa da cikawa, shi yasa mutane suka aminta da shi duk da halin da tattalin arzikin kasarmu ke ciki," in ji Ms Elkhalifa.
Ta ce,"Muna fata Masar da Saudiyya da sauran kasashe za su sauya tunaninsu", ta bayyana tana nufin kasashen da ke goyon bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.
A wani asibiti na kudi mai suna Royal Care Hospital, akwai mutane danƙam wadanda suka ji rauni bayan juyin mulkin da aka yi a kasar, su ma sun bayyana fatansu.
Muhayed Faisal, tsohon dalibi dan shekara 18, an harbe shi sau biyu a kafa a yayin zanga-zangar da aka yi.
Ya ce: "An harbe tare da raunata mutum tara. Babu wani gargadi sai kawai suka fara harbi. Sojojin nan suna abu tamkar dabbobi, kila ma dabbobi sun fi su".
A yanzu an yi masa aiki sau uku a kafarsa ta dama. "Akidarmu ba ta sauya ba, ba ma son sojoji su mulke mu," in ji shi a yayin da likita ke mikar da kafarsa.
A kusa da shi akwai tela mai shekara 54 Yair Mohammed Ali Abdallah, 'yan uwansa sun kewaye shi. Ya bar shagonsa ya bi sahun zanga-zangar a lokacin da aka yi juyin mulkin. Ya ce da gangan motar sojoji ta bi ta kansa a kusa da filin jirgin sama na Khartoum.
Ya ce: "Bayan nan, mutum biyar ko shida sun yi mani dukan tsiya da sanda a bayana da kirjina. Na bi sahun zanga-zangar ce don neman 'yanci da zaman lafiya. Idan har sojoji ba za su iya samar da hakan ba to su bar wa wadanda za su iya".
Akwai jita-jitar da ake kan yiwuwar kulla yarjejeniya tsakanin sojoji da wasu jam'iyyu da ma kungiyoyin da ke cikin gwamnatin rikon kwaryar da aka kafa a 2019.
Amma wasu sun yi watsi da hakan suna masu cewa duk wata yarjejeniya da za a kulla dole a yi abin da ya dace.
An yi asarar biliyoyi
Wata cibiya da sojoji suka rufe bayan juyin mulkin da aka yi a kasar, cibiya ce da aka kafa don ƙwace kadarorin da ake zargi wasu manyan kusoshi sun sace a tsohuwar gwamnati.
Watanni kafin juyin mulkin kasar, daya daga cikin mambobin kwamitin, Wajdi Saleh, ya shaida wa BBC cewa yana da shaida a kan abubuwan da ke faruwa.
Ya ce: "Akwai wasu mutane da suka shirya sace wasu kudade, a yanzu muna neman wasu miliyoyi da suka ɓata."
An kama mutumin a lokacin juyin mulki, kuma har yanzu yana tsare tare da wasu kusoshi a gwamnatin rikon kwaryar kasar da aka rushe.