Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An gano gawar Hanifa, yarinyar da aka sace a Kano bayan kwana 47
An gano gawar yarinyar da aka sace a birnin Kano da ke arewacin Najeriya ranar 4 ga watan Disamban 2021.
Mahaifin yarinyar ya tabbatar wa da BBC cewa an gano hakan ne ta hanyar gano wanda ya sace ta ɗin, bayan da ya zayyana wa jami'an tsaro yadda komai ya wakana.
Mahaifin Hanifa ya ce a yanzu haka an tono gawar ƴar tasa wacce mutumin da ya sace ta ya kashe ya kuma binne ta tun kwana biyar da sace ta.
Wanda ake zargi da kisan na gaban ƴan sanda yana fuskantar tuhuma, kuma tuni ya fara bayani kan yadda aka yi ya kashe ta.
Mahaifin Hanifa ya ce tuni aka tono gawar Hanifa da mutumin ya binne, don gudanar da bincike a kanta. Sannan kuma an sake binne ta kamar yadda shari'a ta tanada a maƙabartar Ƴan Kaba.
Ya kuma shi mai lafin ya shaida wa jami'an tsaro cewa ya sanya mata shinkafar ɓera ne tare da ƙunshe ta a leda ya kuma binne ta a rami.
Wasu labaran da za ku so
Ta yaya aka gano Hanifa?
Tun sanda abin ya faru ne aka ƙaddamar da binciken hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro na farin kaya na DSS da ƴan sanda da jami'an Civil Defence.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda jihar Kano ya shaida wa manema labarai a ranar da aka gano gawar tata cewa, jim kaɗan bayan sace Hanifa sai ɓarayin suka kira iyayenta suna neman kuɗin fansa har kimanin naira miliyan shida.
Bayan samun rahoton ne sai kwamishinan ƴan sanda na jihar CP Sama'ila ya haɗa taron gaggawa na manyan shugabannin tsaro don gano cewa an gano ƙarin dabarun tabbatar da tsaro a jihar Kano.
Daga nan kuma sai rundunar ƴan sanda ta tayar da tawagar Kan Ka ce Kwabo, wato Operation Puff Ader don tabbatar da kamo waɗanda suka sace yarinyar.
"Da aka ci gaba da bibiya aka yi ta aiki da har nasara ta kai aka kama mutum biyu da farko, wato Abdulmalik Muhammad Tanko mai shekara 30 da abokinsa Hashim Isiyaku mai shekara 37 da suke unguwar Tudun Murtala, kuma jami'an DSS suka yi nasarar kama su," in ji DSP Abdullahi Haruna Kiyawa.
"Daga binciken da aka fara ne Abdulmalik ya tabbatar da cewa Hanifa dalibarsa ce tana karatu a makarantar da yake koyarwa a Kwanar Dakata. Ya sace ta ne ya kai ta gidansa ya ɓoye ta har kimanin sati biyu, ya kuma nemi a ba shi kuɗi har naira miliyan shida.
"Ranar 18 ga watan 12 da ya fahimci ana so a gano cewa yarinyar tana tare da shi, don har gidansa ana ta bibiya an je, sai ya gaya mana (ƴan sanda) cewa ya ba ta guba ta sha ta mutu.
"Daga nan sai suka haɗa baki da wancan abokin nasa Hashim suka ɗauke ta suka sa a buhu suka kai ta wannan makarantar suka yi tono suka binne ta," kamar yadda kakakin ƴan sanda ya ce.
DSP Kiyawa ya ƙara da cewa "sai a yau 20 ga watan Janairun 2021 ne muka yi nasarar kamo su."
Kakakin ƴan sanda ya ce sun fara da yi wa Hashim tambayoyi ne inda ya tabbatar da cewa haƙiƙa Abdulmalik ya neme shi ya taya shi wani aiki cewa akwai abin da za su je su binne a buhu, kuma ya taimaka masa wajen yin tonon a cikin makarantar suka kuma binne.
Sannan ya gaya wa ƴan sanda cewa kafin ma wannan lokacin shi Abdulmalik din ya samu Hamshim shi da wata Fatima Jibrin Musa mai shekara 27 da ke zaune a Tudun Murtala, ya kuma ce musu su je su sato masa wannan yarinya, amma sun ce daga baya sun gaya masa ba za su yi ba.
A yanzu dai ƴan sandan sun ce dukkan mutum ukun da Abdulmalik da Hashim da Fartima duk suna hannun ƴan sanda za a ci gaba da bincike.
A wane hali aka ga gawar Hanifa?
A hotunan da ƴan sanda suka sake dai an ga gawar Hanifa da aka tono a cikin buhu duk ta dagargaje.
A cikin hotunan masu ɗaga hankalin gaske, an ga hatta da ƙoƙon kan Hanifa.
Sannan ga yadda ake ganin hotunan gawar da alama an yi gunduwa-gunduwa ne da ita.
Jami'an lafiya na ɓangaren ƴan sanda ne suka yi aikin tonon gawar tata.
Waiwaye
A ranar wata Asabar 4 ga watan Disamban shekarar da ta ƙare ta 2021 ne aka sace Hanifa mai shekara biyar a unguwar Kawaji da ke birnin Kano.
Mutanen sun ɗauke Hanifa Abubakar ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma bayan sun isa wurin a cikin babur mai ƙafa uku ko kuma A daidaita-Sahu.
Iyayen Hanifa sun ce mutanen sun sace ta ne jim kaɗan bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya tare da sauran yaran maƙota.
"Babu nisa tsakanin makarantar da gidansu (Hanifa), saboda haka yaran sun saba zuwa da ƙafarsu," a cewar Suraj Zubair, kawun Hanifa.
"Wasu daga cikin yaran da suka ga lokacin da abin ya faru sun ce ɓarayin sun zo ne a A daidaita-Sahu kuma suka ce za su kai su gida.
Bayan sun kai su, sai suka ce Hanifa ta sake hawa don su ɗana ta, amma sai suka gudu da ita."