Sace-sacen ɗalibai a makarantu huɗu da suka girgiza Najeriya

A ranar Talata da tsakar dare ne wasu 'yan bindiga suka yi dirar mikiya a makarantar sakandaren Kagara da ke jihar Neja ta arewacin Najeriya inda suka yi awon gaba da wasu ɗalibai da malamansu.

Shugaban makarantar, Danasabe Ubaidu, ya shaida wa BBC Hausa cewa akwai dalibai kimanin 600 a makarantar lokacin da lamarin ya faru.

Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya ce an kwashe dalibai 27 da ma'aikata uku hadi da iyalansu 12.

Duk da kawo yanzu ba a iya tantance masu alhakin harin ba, satar mutane don neman kudin fansa ba sabon abu bane a Najeriya, kuma jihar Neja na cikin yankunan arewacin kasar da yan bindigar suke aika aikarsu.

Ba wannan ne karon farko da aka sace dalibai daga makarantunsu ba, lamarin da masana harkokin tsaro ke bayyanawa a matsayin wani yunƙuri daga ɓangaren 'yan bindiga na samun kudin-shiga da kuma ci gaba da kasancewa a kafafen watsa labarai.

Mun duba sace-sacen dalibai a makarantu hudu da suka girgiza Najeriya da ma duniya:

Sace ƴan matan makarantar Chibok

Harin da mayaƙan kungiyar Boko Haram suka kai makarantar sakandaren mata da ke Chibok a jihar Borno ranar 14 ga watan Afrilun 2014, shi ne ya fi jan hankalin kasashen duniya.

Mayakan dauke da manyan bindigoyi sun shiga garin da tsakar dare suka tashi mazauna da karar harbi kafin su kutsa cikin dakunan kwanan dalibai suka loda su a motoci sannan suka yi awon gaba da 'yan mata 276.

Karon farko kenan da aka fara ganin irin wannan tashin hankali a garin Chibok duk da cewa kungiyar Boko Haram ta saba kai hari a wasu kananan hukumomin jihar Borno.

Hakan ya sa kasashen duniya sun yi ta sukan gwamnatin Najeriya ta wancan lokacin karkashin jagorancin Goodluck Jonathan bisa rashin daukar mataki.

Hasalima an ƙirƙiro maudu'in #BringBackOurGirl a shafin Twitter wanda ke nufin 'A dawo da 'ya'yanmu mata' inda fitattun mutane ciki har da mai dakin tsohon shugaban Amurka Michaelle Obama suka riƙa yayatawa domin jan hankalin hukumomi su dauki mataki.

Ko da yake an ceto galibinsu lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulki, amma har yanzu wasu suna hannun mayakan kungiyar ta Boko Haram.

Daliban makarantar Dapchi

A watan Fabrairun 2018 ne wasu da ake zargi mayakan kungiyar ta Boko Haram ne suka kai hari makarantar mata da ke garin Dapci na jihar Yobe sannan suka sace dalibai 110.

Lamarin ya faru ne kusan shekara hudu bayan sace 'yan matan makarantar Chibok.

Bayan sace su ne gwamnatin tarayya ta tura sojojin sama da sauran jami'an tsaro domin ceto 'yan makarantar.

Gwamnan jihar Yobe na wannan lokaci Ibrahim Gaidam, ya dora alhakin sace matan a kan sojojin Najeriya wadanda ya zarga da janye shingen binciken ababen hawa daga garin na Dapchi, lamarin da ya ce shi ya bai wa Boko Haram damar sace daliban.

An saki 104 daga cikinsu a watan Maris na 2018 yayin da biyar suka mutu a ranar da aka sace su, amma yarinya daya mai suna Leah Sharibu tana ci gaba da zama a hannun mayakan na Boko Haram, wadanda suka ƙi yarda su sake ta saboda ta ce ba za ta bar addininta na Kirista ba.

Daliban makarantar Kankara

A watan Disamba na shekarar 2020 ne wasu 'yan bindiga suka kai hari makarantar sakandaren kimiyya ta maza da ke garin Kankara na jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

'Yan bindigar sun sace dalibai fiye da 300 inda suka yi doguwar tafiya da su zuwa wasu dazuka da ke jihar Zamfara mai fama da matsalolin 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

Wannan satar dalibai ta jawo ce-ce-ku-ce bayan da shugaban wani bangare na kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya ce mayakansa ne suka sace daliban.

Sai dai daga bisani hukumomi a jihar Katsina da Zamfara sun ce masu satar mutane ne suka sace daliban.

Bayan wasu kwanaki ne 'yan fashin dajin suka saki dalibai 340 daga jihar dajin jihar Zamfara bayan gwamnan jihar Bello Matawalle ya ce kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta shiga tsakani.

Sace daliban makarantar Kagara

Da tsakar daren Talata 16 ga watan Fabrairun 2021 ne wasu 'yan bindiga suka shiga makarantar sakandaren maza da ke garin Kagara na jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya inda suka yi awon gaba da wasu daga cikinsu da malamansu da kuma wasu iyalan malaman.

Shugaban makarantar ya shaida wa BBC cewa akwai dalibai kusan 600 a makarantar ta kwana lokacin da lamarin ya faru.

Sai dai daga bisani Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya ce an kwashe dalibai 27 da ma'aikata uku hadi da iyalansu su goma sha biyu.

Duk da kawo yanzu ba a iya tantance masu alhakin harin ba, satar mutane don neman kudin fansa ba sabon abu bane a Najeriya, kuma jahar Neja na cikin yankunan arewacin kasar da yan bindigar suke aika aikarsu.