Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Azare: WhatsApp ya taimaka an gano yarinyar da ta bace tsawon shekara hudu
Iyayen wata ƙaramar yarinya da aka yi zargin an sace a garin Azare na jihar Bauchi, suna ci gaba da murnar sake ganin 'yarsu Zainab bayan kimanin shekara huɗu.
Hukumomi ne suka shiga tsakani wajen karɓar yarinyar wadda a yanzu ta kai shekara bakwai daga hannun wadanda suka riƙa kula da ita a garin Giade, bayan mahaifanta na ainihi sun gano ta, ta hanyar WhatsApp.
Sun ce sun samu labari ne ta WhatsApp cewa akwai wata yarinya a garin Giade da aka taba tsinta tana ƴar shekara uku, sai suka buƙaci ganin hotunanta, sai aka rura musu ta WhatsApp ɗin.
Daga nan ne suka gane ƴarsu ce, sai suka niƙi gari suka tafi garin Giade mai nisan tafiyar minti 15 a mota dag Azaren don ganowa da idonsu.
Satar ƙananan yara na ƙara zama ruwan dare a wasu birane da garuruwan arewacin Najeriya.
Mahaifin Zainab, Mallam Sama'ila Haruna ya ce bai taɓa fitar da ran sake ganin 'yarsa ba, duk da yake sun yi imanin cewa sace ta aka yi a farkon 2018.
Ya ce sun yi ta neman Zainab 'yar shekara uku kafin ɓacewarta, inda nema ya kai shi har zuwa birnin Kano da Gombe, bayan samun rahoton gano wasu ƙananan yara a hannun mutanen da ake zargi sun sace su can a baya.
Rashin magana na Zainab lokacin da aka tsince ta, ya sa cigiyar iyayenta na asali ya zamo wani abu mai matuƙar wahala, mai yiwuwa saboda ƙarancin shekaru da kuma ɗimuwar da ta shiga.
Lokacin da suke ƙoƙarin karɓar 'yarsu, Mahaifin Zainab ya ce shaida wa BBC cewa sun same ta cikin kyakkyawan hali tare da yaba wa wanda yarinyar ke hannunsa bayan sun je garin Giaɗe.
"Ya riƙe ta kamar ƴarsa ta cikinsa, ya yi ɗawainiya da ita tare da ba ta tarbiyya mai kyau domin ba ta da wani alamar yunwa ko wahala, kuma ba ta canja kamanni ba sai girma da ta ƙara," in ji shi.
Mutumin da ya riƙe Zainab tsawon shekara huɗu, Ahmed Adamu Giaɗe, Mai Dalan Giaɗe, ya ce an tsinto yarinyar a halin gigita da askakken kai a tsakiyar dare.
Bayan mahukunta sun nemi ya riƙe ta ne, sai ya raɗa mata suna Aisha, kuma ya saka ta makarantar Boko da Islamiyya.
"Mun yi wa iyayenta na asali murnar samun ƴarsu amma ba ƙaramin tashin hankali muka shiga ba ni da iyalina saboda ɓacin ran rabuwa da ita," in ji Ahmed Adamu Giaɗe wanda ya riƙe Zainab.
Mahaifiyar yarinyar, Rabi'a Ahmed ta ce sai da ta yi kuka a lokacin da ta sake haɗa ido da 'yar tata, saboda farin ciki.
Iyayen yarinyar sun ce ta fita gida ne, kuma tun da ta fitan ba su sake ganinta ba.
Ofishin kyautata jin daɗin al'umma na ƙaramar hukumar Giaɗe ya ce sun tantance duk shaidun da mahaifan Zainab na asali suka gabatar kafin su ɗauke ta, tare da damƙa ta hannun ƙaramar hukumar Azare wadda ita kuma ta miƙa yarinyar ga iyayenta.
Auwal Ahmad Giaɗe mataimakin shugaba a ofishin kyautata jin daɗin al'umma na Giaɗe, ya ce yarinyar tana kama da mahaifiyarta kuma da farko ba ta gane mahaifiyarta ba sai daga baya da hankalinta ya dawo ta faɗa da bakinta cewa wannan mahaifiyarta ce.
Ba duk iyayen da suka rasa ƴaƴansu ba ne ke katarin sake ganinsu ba. Mahaifan Zainab dai sun yi matuƙar auna arziƙi, bayan Allah ya kuɓutar da ƴarsu kuma ya damƙa ta hannun na gari.
Uwar Zainab ta ce a shekarar da 'yarta ta ɓata, an yi fama da ɓata ko satar ƴaƴa a garin Azare. Kuma a baya-bayan nan ana ƙarin damuwa a birane kamar Kano game da ɓata ko satar ƙananan yara.