Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ƴan bindiga sun sace fasinjoji daga motoci goma a Zamfara'
Rahotanni daga Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya na cewa 'yan bindiga sun sace matafiya da dama da ke kan hanyarsu ta zuwa jihar daga jihar Katsina.
Ganau sun shaida wa BBC Hausa cewa daga ranar Juma'a zuwa safiyar Asabar 'yan bindigar sun kai hari kan motocin fasinja kusan goma, kuma sun kwashi mutane da dama sannan suka kashe wasu.
Wata mata da ke daya daga cikin motocin ta shaida mana cewa lamarin ya faru ne lokacin da suka taso daga jihar Katsina mai makotaka zuwa jihar Zamfara kuma ya rutsa da abokiyar tafiyarta.
"Mun taso daga garin Jibiya da karfe huɗu na yamma kuma mun isa Funtua da misalin ƙarfe bakwai da wani abu. Daga nan mun wuto 'Yankara zuwa garin Kuceri. Ba mu san da su ba saboda suna cikin duhu ne. Kawai sai muka ji ƙarar harbi a ko'ina," in ji ta.
Ta ce da direban motar ya ji ana harbinsu, sai ya juya motar zuwa cikin gona, inda ya koma kan titi, amma sai ɓarayin suka bi su suka harbe tayar motar guda ta baya.
"A lokacin ne wani harsashi da suka harbo ya zoje ni ga kunchi kuma ya wuce ya bi ta cikin kujera, inda ya same ta a kanta."
Ta ce saboda harbin, "gilashin motar ya watse kuma ya shiga cikin ijiyata ya yanke ni."
Daga nan ne direban motar ya wuce da su zuwa garin Wanzamai.
Matar ta ce bayan sun isa Wanzamai sai direban motar ya bukaci jama'a su ba su agaji, "Daga nan sai aka zo da wata mota kuma aka saka ni da waccan wadda aka harba a kai domin a kai mu asibiti a 'Yankara".
Ta kara da cewa, "Lokacin da muka isa 'Yankara mun ɗauka harbin da aka yi mata a bayanta ne, sai da muka kai asibiti ne suka duba kuma suka ce a kanta aka harbe ta."
Ta bayyana cewa ana cikin kulawa da ita abokiyar tafiyarta ta cika: "Ana min dressing, kai kafin a gama min dressing ma rai ya yi halinsa."
Matar ta kuma ce ba motar su barayin su ka fara tarewa ba.
"Sun fara tare wata mota kuma suka harbi wani mutum guda a kafa cikin motar, inda shi ma ya juyo kuma ya rinka yi ma direbanmu alama da hannu cewa akwai matsala amma da yake dare ne takwas da rabi shi ya sa bai gani ba."
Ta bayyana cewa bayan da direban motar da suke ciki ya juya, shi ma ya rika kokarin sanar da wasu direbobin matsalar da ke wurin amma ba su gane ba.
"To sun dai kama wadannan motocin kuma har sun tafi da mutanen da ke cikin motocin. Sun kama kusan mota goma ciki har da tireloli."
'Da naji cewa an harbe ta a baya, na san ta riga ta mutu'
Murtala Aminu shi ne maigidan matar da ta mutu a cikin wannan hari ga kuma abin da ya ke cewa: "Zuwa dai karfe shida mun yi waya da ita, kimanin shida da rabi, sai ta ce sun taso har sun wuce Funtua. To bayan na zo gida kuma bayan karfe bakwai, sai aka aiko cewa ana kirana. Har na ki zuwa sai aka ce in tafi mana saboda yana iya yiwuwa abu muhimmi ne."
Bayan ya isa gidansu sai abokiyar zaman matarsa ta ce an kira waya cewa an harbi Aisha da Jamila. Sai aka ce min a baya aka harbe ta. Ina jin haka sai na ce na san ta rasu."
Mallam Murtala ya ce daga baya mahaifinsa da wani dan uwansa sun same shi a gida kuma sun tabbatar masa cewa matarsa ta mutu a sanadin harbin da aka yi ma ta a ka.
Ya kuma ce bayan gari ya waye ne aka taho da gawarta kuma aka yi ma ta sutura.
Ya zuwa wannan lokaci hukumomi ba su ce komai a kan batun ba.